← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abee Yana Zaune kan sofa ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana ƴan ciye-ciye ,Maryam tana tsaye a gefensa ta zuba masa wata uwar harara kamar idon zai faɗo ƙasa, a ranta tana tunanin Dalilin da yasa gabaki ɗaya baya ƙaunarta, a zahiri Kubrah ta fishi Barazanar Jinkai da Izza tare da ƙin shiga sabgar Mutane , tunda shi har Boyi-boyin Gidan ma yana sakar musu fuska ya saurare su amma ita ko Ƙuda ma ya fi ta Mutunci a idonsa. Ba ta ankare ba sai ji tayi ta zabga tsaki.

Cike da mamaki ya juyo yana binta da wani irin kallo me cike da salon bambanta tsara, "Wato tsayin Bakinki har ya kai ki jawo min tsaki ko?, sabida baki da Kunya har ki kalli tsabar idon ƙannena kina gaya musu kin tsane ni ko?, to nima na tsaneki!!" ya ƙarasa maganar tare da wurga mata Apple ɗin da ya fara gwaguya, cikin sa,a ta sauka akan bakinta jikake ɓam!!!...... Danne bakin tayi da duk hannayenta a take idanunta suka kawo ruwa saboda azabar da ta fara sagaraftu a cikin ƙwaƙwalwarta.
Mammi ce ta ƙaraso wajen da sauri tana cewa "Abee ubanka kenan! , kar ka ƙara harinta da duka ka san dai zafin hannu gareku, sai ka je ka illata mata baki a banza!"
ƙarasawa tayi wajen Mariam ta riƙo hannunta tana bata haƙuri. Tuni Yawu da jini sun haɗe sun fara tsiyaya zalalala!! , Mammi ta runtuma salati ta cigaba da cewa "Abee! baka da hankali ne? me tayi maka!!?"
"Mammi ta raina ni ne, har da cewa ta tsane ni!"
tsaki kawai tayi bata ƙara bi takansa ba sai ta shiga rarrashin Mariam......

Miƙewa yayi yana cewa "Gobe ki ƙara zuwa kiyi min tsaki, kuma naji daɗi da kika tsane ni don nima na tsane ki!"
raka shi sukayi da idanu har saida yayi nisa daga wajen sannan Mariam ta cigaba da kukanta ....... A zahiri kukan takeyi a cikin ranta kuwa jinjina izzar Ubangiji takeyi da ya halicce su tamkar Kaifin Takobi, Dukkansu babu na banza sai dai Abee da Kubrah sun fi Saim da Zahra tsauri, duk da ba sanin Affah tayi sosai ba amma takanji labarinsa a wajen Abbinta, idan ta kalli hakan kuwa sai taga babu abinda suka bari daga Mahaifinsu daga kan kamannin fuska har zuwa Miskilancinsa da tsarinsa da kuma Kaifin da yake dashi akan abu............

Kaitsaye inda yake tunanin zai samu Kubrah can ya nufa sai dai kash!!! bata nan, sai da Zuciyarsa ta yi wani wawan tsalle kafin ta fara harbawa da gudu-gudu. Cikin sauri ya fito yana tambayar duk wanda yaci karo dasu amma kowa cewa yake bai ganta ba.......
HaÉ—awa yayi da gudu ya fita daga cikin gidan ya nufi cikin Daji yana surfa mata kira.........
sai da ya sha bulayi sannan ya samota a gefen ruwan Kogin dake cikin Dajin tana zaune ta sa shi a gaba tana kalla...... da gudu ya ƙarasa wajen gami da dire gwiwoyinsa a ƙasa ya zube a gabanta yana maida numfashi, ,,,,, sai da ya ɗan sarara sannan ya ɗago idanunsa da suka canja Launi zuwa kalar zaiba sai sheƙi sukeyi tamkar ba na ɗan Adam ba.

Hawayen da ya gani layi-layi akan fuskarta ne ya tsayar masa da tunanin abunda zai yi wani mugun kallo ya zuba mata me cike da fusata, buɗe baki tayi zatayi masa magana ya dakatar da ita ta hanyar wanka mata wani Rantsatstsen Mari,,,,,, ba shiri ta miƙe tsaye hannunta na kan kumatun nata.
shi ma miƙewar yayi ya juya mata baya ,,,,,, da sauri ta nufo inda yake tana shirin faɗawa jikinsa yayi saurin dakatar da ita da cewa "Karki taɓani tunda bani da amfani a wajenki!!! " "Abeeeee!!!!" ta kira sunansa cikin mamakon firgici! cigaba tayi da cewa "Abee please listen to me Abee please!!" kukan da ya ci ƙarfinta ne ya hana ta ƙarasa maganar, a fusace yace "Me zaki gaya min??!!! me yasa zaki zauna kina kuka anan?? kenan ba za ki iya faɗa min damuwarki ba koda kuwa banida ƙarfin da zan temaka miki?!!! ko kuwa a tunaninki don kin ɓoye min farin ciki zanyi da hakan!! ! ! ! !!" ya ƙarasa maganar cikin tsawa,,,, girgiza kai ta shiga yi tana cewa "A'a Abee! ba zan so nauyin laifina ya cigaba da ɗoruwa akan kafaɗunka ba Abee" sassauta murya yayi kamar zai fashe da kuka ya ce "Ke fa dole na ce Kubrah!, duk da ban baki tazara ba amma fa ni ne babba a cikinku, nauyi ne akaina na hana zubar hawaye a idanunku, bare ke da tun Ina Cikin Mahaifiyata bani da Abokiyar wasa sai ke, babu wanda nake iya faɗawa Abunda ke kwance a cikin Zuciyata sai ke!, me yasa yau ɗaya zaki ɓoye min" cikin muryar kuka tace
"Abee!! faɗanka baya min daɗi Abee!!! kayi haƙuri don Allah!, babu abunda na yiwa ƙaddara amma ta haɗani da son wanda gwara in so Bawan dake Bauta a gidanmu zai fi Mutunci a idon Affah!,, Abee wallahi ina son shi, ina son kasancewa dashi har ƙarshen rayuwata,,,,, Abee!! ina so kullum idan na buɗe ido in dinga ganinsa, idan ban samu hakan ba kuma babu shakka farin cikina zai samu tangarɗa!!"
Lumshe idanunsa yayi gami da kwasar gefen leɓensa na ƙasa ya taune shi da ƙarfin gaske... Buɗe mata hannayensa yayi aikuwa ta yi saurin faɗawa jikinsa tana sakin wani sabon kukan,,, sai da ƴan sakanni suka shuɗe sannan ya buɗe idanunsa hakan yayi daidai da zubowar hawayensa, ,,,, "In Allah ya kaimu gobe ki je ki gayawa Umar Abunda kika gaya min yanzu,,, amma da sharaɗi ɗaya akansa muddin ya mutunta soyayyarki bai wulaƙanta ki ba zan so shi, amma idan wulaƙanci ya biyo baya zan tsane shi, hakan kuma Barazana ce ga duk wani farin cikin rayuwarsa , in kuma ya Amince da kaina zan sanarwa Affah domin babu amfanin zaman jira"
"Na gode Abee!" "Kar kiyi min godiya , kawai ki dena kukan shine abunda bana so!".....

"Ƙwarai kuka bai dace da ku ba Domin kun fito ne daga tsatson Gwarzon da Muke Kira Namijin Duniya,,,,, babu abunda yake firgita shi bare har ya sa shi Zubar da hawaye, don haka nake jin matuƙar raɗaɗi idan naga damuwa ta bayyana akan fuskarku, bayan hakan ba Ta'adar gidanku bace, ba a taɓa gane raunin Affanku akan fuskarsa, ku zamo masu dakakkiyar Zuciya tamkar shi,,,,, jinjina ga Sarakan Gobe!!"
Ahmadi ne yake zayyano jawabin cike da girmamawa gwiwoyinsa zube a ƙasa.
Murmusawa Abee yayi kafin ya ce "Ahmadi idan Mutum bai san halinka ba babu shakka zaka sa kansa yayi girman da shiga Ƙofar Masarautar Garin nan sai ya gagare shi, In Allah ya kaimu gobe ka kaita wajen Umar cike da kulawa, ka kasance tare da ita a kowane saƙo da lungu ka zamo shaida akan duk motsinsu!"
ƙara russunawa yayi yana cewa "Indai Allah ya aramin lafiya babu shakka zan aikata abunda ka Umarce ni Shugaba!".

*🪻SAWUN KEKE🪻*
season *2*

By INDO

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU.....)
Ep........10

*Ɗaya daga cikin Ƙauyuka mabambanta dake Ƙasar China.............................*

Kamar Yadda aka sani a cikin kowace Masarauta akan Fuskanci ƙalu-bale, haka saɓanin fahimta, kokuma bambancin ra'ayi, sannan akwai guru-gubji a cikinta ta yadda har akan iya rasa rai domin cimma wata manufa...........

Itama Masarautar da SARKI YIZHENG yake Jagoranta a wannan ƙarnin,,, cike take taf da irin waɗannan Ƙalu-balen , sannan cike take da Manyan MATSAFA da Masu SIHIRI, hallau sukanyi amfani da wannan damar wajen Mallakar duk wani abinda suke son cimmawa kokuma kawar da dukkan Ruhin da zai kawo Tsaiko ga Muradinsu....................
_______________________________
Daidai wannan lokacin zamu iya kiransa da Yamma yayin da rana take shirin gushewa daga sararin Samaniya ta koma Makwancinta wanda Allah ne kaÉ—ai Yasan ina ne..........

https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw

King Yizheng yana Zaune cikin sirrintaccen ÆŠakinsa wanda yake aiwatar da Tsafe-tsafensa, idanunsa na kan wata tafkekiyar Taswira.... Yadda yake kallon Taswirar kaÉ—ai ya isa tabbatar da muhimmancinta gareshi.

"Yi Zheng!! Kana wasa da damarka, muddin Bakayi sauri ba zaka rasa Ƙarfin ikon da kake son samu,,,, Kamar yadda muka gaya maka indai bakayi amfami da wannan Yarinya ba to ba zaka taɓa dawwama akan wannan Mulki ba, ɗan uwanka zaiyi nasarar Kawar da kai, sannan Ba zaka taɓa zama Babban Sarki a Ƙasan China ba...."
wata murya mara daɗin amo ke yi masa tuni akan aikinsa na gaba,, Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke bayan Hasken da ya bayyana akan Taswirar ya ɓace.

""Yizheng! ! !!"
Kyakkyawar Matarsa kuma kamalalliya, wadda ta sha ado irin na Sarauta itace ta katse masa tunanin da ya tafi.
Yadda ta kira sunansa cikin razani yasa shi saurin miƙewa yana Zuba mata idanunsa da suka ƙara girma.
Cigaba tayi da cewa "Meyasa kake son tarwatsa rayuwar wasu don cikar muradinka?, Ba na so ka dinga aikata waɗannan zunuban, ka zauna iya matsayinka, kar ka cutar da Ƴar Mutane!"

ÆŠan Murmusawa yayi kafin ya tako Zuwa inda take yasa hannu ya É—auki É—an cup É—in dake kan tray a hannun Hadimar Queen Xiang.
Sai da ya kurɓi Haɗin lemon Fruit ɗin ciki sannan ya kalleta cikin muryar raɗa yace "Hakan Mafarkina ne, cikar shi kuma ya zama nauyina, Kawar da duk wanda baya goyon bayana hakan haƙƙina ne; Kin sani ina sonki Queen Xiang abun alfahari ne gareki in Zamo Sarkin da Duniya take labarinsa kuma take matuƙar tsoronsa, kuma hakan zata faru ne bayan Yarinyar ta zama mallakina , Itace Mahaɗin Ƙarfin ikon da Duk Manyan Hatsabiban Duniya suke nema; Karki damu akan hakan cikin sauƙi zan kammala komai ba wata Yarinya ce me galihu ba ta kasance Ƴar Nigeria kin ga ba zan sha wahalar samunta ba!"
Hawayen baƙin ciki ne suka fara silalowa kan kumatun Queen Xiang, cike da ɓacin rai ta ce "Indai ina raye ba zan bari hakan ta kasance ba, ka kasance Azzalumin Sarki wanda baya tausayin Talakawansa, indai na bari ka shahara tabbas Al'umar Duniya zata yi Kuka da kai , kuma ka sani ka ci Amanata ka ci Amanar Mahaifina da ya baka Amanata, Tabbas zan dakatar da kai koda hakan na nufin rasa raina ko kuma naka!"
Chapter 9 · 0% Book details