← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 16

Sashe 11

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kubrah!!" ya kira sunanta cikin wata kalar murya wadda tayi matuƙar tasiri akanta, cak!! ta tsaya ba tare da ta juyo ba haka kuma bata yi yunƙurin ƙara tafiya ba. "Kiyi Haƙuri ba zan iya Karɓar Soyayya daga gareki ba, banida wannan ƙwarin Zuciyar,,,, amma don Allah ina neman Alfarmarki!" runtse idanunta tayi da Matuƙar ƙarfi gami da cije gefen leɓenta........
Zagayawa yayi gabanta ya durƙusa kan gwiwoyinsa sannan ya haɗe hannayensa waje ɗaya, cikin raunin murya ya ce "Ki temaka ki zamo wani tsagi na rayuwata Kubrah!!!,, Ki Aure ni, ki kasance Tare dani Har Abada Don Allah!!!; Darajarki ta wuce ki nemi soyayyata sai dai ni in nemi Alfarma ki So ni, na baki haƙuri ne saboda kasa gaya miki da nayi har sai dai kika sha wahalar zuwa nemana, Tabbas da na san Inda zan nemi ki in baki amsoshinki da tuni na je har Wajen komai nisan sa Sannan da tuni na roƙe ki ki zamo Gatana, amma ko yanzu duk da na Makara ina Fatan zaki Zamo Haske gareni ki zamo silar Yayewar duhun da yayiwa rayuwata Ƙawanya Kubrah!!! don Allah!......" daidai lokacin Hawayen da suka cika idanunsa suka samu damar zirarowa suna sauka ƙasa......
Tunda ya fara magana idanunta suna kansa har sai da ya kai ƙarshe sannan ta numfasa, a hankali ta durƙusa saitinsa sannan ta ce "Baka makara ba!, yanzu ne daidai lokacin da ya dace,,, amma me yasa kake kuka a memakon kayi farin ciki Bayan ka gina Fadarka a Masarautar da kake Mafarkin Zama Sarki a cikinta?" ''Na kamu da matuƙar tsoron kar wani furci nawa ya zamo abun fushi gareki, ina matuƙar Sonki Kubrah!!" Yalwataccen murmushi ta saki kafin ta ce "Nayi farin ciki sosai da jin dukkan kalamanka, na ƙara samun ƙwarin gwiwa, musamman da ka yarda dani kuma ka so ni duk da baka san ko ni Wacece ba hakan kaɗai ya isa ya tunzura ni,,, in tunkari Duniya in sanar kai ne zaɓina!!" "Sonki daga Allah ne Kubrah, ba ni nayi Dashensa ba da kansa ya tsiro, ke kaɗai nake so shiyasa ban damu da bibiyar Tarihinki ba Duk da cewar ina son ji, ba zan tilasta miki wajen Faɗa min ba, sai lokacin da kika yi niyya!" Ɗan Murmusawa tayi kafin ta miƙe ta koma kan Kujera ta zauna, ganin haka ya sa shi miƙewa shi ma ya zauna.........

https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw

Sai da ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Khadijatul-Kubrah Ɗiya ga Muhammad Rislan !, Ina rayuwa a wata Ƴar Ƙaramar Duniya kuma keɓantacciya, Ba zan iya cewa ga Shiyyar da Muke ko kuma wani Local Government da ya jiɓance mu ba, abu ɗaya kawai na sani shi ne a Jihar Kano Muke, takamaimai ban san Yaya zan yi kwatance a gane Gidanmu ba, sannan Mutanen da muke mu'amala dasu a ƙayyade suke haka wanda suke rayuwa a ƙarƙashin Ikon Affana, Gidanmu Baya ɗaya daga cikin jerin Masarautun Duniya amma ya kasance Tamkar Masarauta sabida girmansa da kuma ɗumbin Dukiyar da ke cikinsa, sannan akwai Bayi da Hadimai a cikinsa,,, Affana ba Sarki bane amma Mutane da yawa da hakan suke kiransa ko su ce Mai Martaba ko kuma Shugaba, mu kuma sukan bamu Matsayin Ƴaƴan Sarki,,,, A Masarautar mu akwai kowa amma babu Waziri ko Galadima Affana shi kaɗai yake Mulkinsa kuma yake zartar da hukunci; Affa yana da tsauri musamman akan ra'ayinsa ko kuma Dokokinsa, ba ga Mutanen Gari ba kaɗai har mu Ƴaƴansa manta alaƙarmu yake yi a yayin da ya tashi Hukunta mu bisa Laifinmu, hakan ne yasa damu da Al'uma muke matuƙar tsoron Fushinsa,,,, Daga cikin gida sai Daji nan ne kaɗai inda Affa ya sahale mana mu je mu yi Wasa;, koda acikin Dangin Mamma ko kuma dangin Affa wasu suke son ganinmu sai dai su zo gidanmu su same mu, sai jefi-jefi ake kai mu gidajensu shi ma ta sigar da ba zamu iya mayar da kanmu Gidan ba" Shiru ta ɗan yi tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya sannan ta cigaba "Na taɓa gaya maka cewa gabaki ɗaya rayuwata Tambaya ce, gashi yau ina ƙara maimaita maka, Ni kaina ina da Tambayoyi akan rayuwata sai dai banida me bani amsar su, a taƙaice dai ni kaina ban gama sanin Wacece ni ba!!" Ɗan tsagaitawa tayi sannan ta ƙara da cewa "Ina fatan babu wani dalili ko wani tsanani da zai sa ka guje ni Umar!!!, ina fatan zaka iya Fuskantar Mahaifina da kuma Sauran Mutanen dake gareshi ka faɗa musu cewa Ka zaɓe ni a matsayin Abokiyar rayuwarka komai wuya komai runtsi, sannan fatana na ƙarshe shine,,,, koda zan kasance Musaka ko kuma in kasance cikin wani Jinsi daban hakan ba zai sa ka juya min baya ka ƙaurace min ba !" Gwauron numfashi ya sauke gami da lumshe idanunsa ya murmusa sannan ya ce "Indai haka ne zanyi, ko yanzu in zaki kaini zan faɗa masa, kuma ko ina za a shigar dani ba zan canja maganata ba, dukkan Fatanki zan cika shi Bi'izinillah, ba zakiyi da na sanin Sona da kikeyi ba zan zamo miki Bango a rayuwa da ikon Allah "
Miƙewa tayi gami da cewa "Lokacin tafiyata yayi ba don na gaji ba!" shima tashi yayi yana cewa "Yaushe zan ƙara ganinki?" "Ba ni ke yanke wannan hukuncin ba, in dan ni ce gobe ma zan dawo, amma ba zan iya hakan ba har sai na samu izinin Abee!"
ya buÉ—e baki zaiyi magana ya dakata don ganin idanun Abee a kansu...........

Ware mata hannayensa yayi aikuwa ta falla da gudu ta ɗafe shi ya rungumeta tsam gami da lumshe idanunsa, sai da ya ji sautin kukanta sannan ya ɗan janye jikinsa yana cewa "Kin san na hana ki kuka ko?" share ƙwallar tayi tana cewa "Yaushe ka zo?" Murmushinsa na gefen baki yayi kafin ya ce "Na daɗe da zuwa, hankalina ya kasa kwanciya ne, alhaki ne a wuya in mayarwa Affah Ɗiyarsa Gida lafiya!" "Na ji daɗi da ka zo, daman ina tsoron komawa ni kaɗai!" Bai ce komai ba ya sungume ta ya ɗorata kan Dokinta sannan ya haye nasa yana cewa "Ahmadi ka ƙara ninka kulawarka akanta" Ahmadi ya rusuna yana cewa "Zanyi hakan da izinin Allah"
Bai ce komai ba yayi gaba hannunsa ɗaya riƙe da Linzamin Dokin Kubrah, Ahmadi kuma ya bi bayansu .....
Har suka ɓace Kubrah tana waiwayen Umar shi ma yana ta famar kallonta.

Da baya da baya Umar ya ƙarasa jikin bango ya jingina tare da furzar da wata zazzafar iska kamar wanda ya kawo Ƙarshen Yaƙi.
Ammar ya kalle shi sama da ƙasa kafin ya ce "Danƙari maƙari, gaskiya sai na nemo Marubuta sun rubuta labarin Soyayyarka Abokina, na san hakan zai zamo Darasi ga Mutane daga nan har Ƙarni Casa'in Masu zuwa!" Murmusawa Umar yayi gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya sannan ya ce "Ba na son Zolaya Ammar, ni anan ban ga abun da zai zamo Darasi ba bare har a rubuta, ba fa a kaina aka fara So ba kuma ba a kaina aka gama ba"
"E, na san da hakan, amma ni kai na gani kuma kai na sani, nima na É—auki nawa Darasin saura Æ´an baya!, ni bari ka ga ma in koma in gayawa Ummi da Abba su yi shirin zuwa neman Aure, yau na fasa fita kasuwar ma!" yana kaiwa nan ya juya da gudu zuwa cikin Gida ba tare da tsayawa saurarar kiran da Umar yake masa ba.

Sin......

Cikin Sanɗa take takawa tana yi tana waige-waige gami da laɓewa da zarar ta ji wani motsi yana shirin tinkarota.....
Jikinta a rufe yake ruf!! cikin kaya na Alfarma irin na Ƴaƴan Sarauta a Ƙasar China, bayan duk adon da ta sha ta lulluɓe Fuskarta da Farin Mayafi sai iya idanunta wanda suka sha Gazal kaɗai ake iya gani, Daga yanayin Zubin Jikinta da kuma ƙwayar idanunta za a gane Yarinya ce wadda ba ta wuce shekara Ashirin ba.....

Shigowarta Sashin Yarima Jiehong ne ya sa ta ƙara sauya taku gami da ƙara taka-tsantsan don gudun Dakarun da suke aikinsu a wajen.
Ta shagala wajen tunani kawai taji Ƙafarta ta riƙe ƙam!! ko motsata ta kasa yi, a hankali tayi ƙasa da kanta ta duba ƙafafun nata, ko shakka babu Wani hatsabibin Matsafin ne ya riƙe mata ƙafa.
Ɗagowa tayi tana rarraba ido cike da son ganin ta inda za a ɓullo mata, Ganin Farar Takobi na walƙiya a saitin wuyanta ne ya sa Ƙara buɗe idanunta cike da razani, "Bayan kun Kashe mana Sarauniya yanzu shi ma so kuke ku kashe shi??" Muryar Ɗaya daga cikin Sojoji mafi kusa da Prince Jiehong ta ratsa kunnuwanta,, cike da ƙarfin hali ta ce "Ba don kai na zo nan ba, don haka ka bar ni in je gurinsa, kuma baku da Hujjar cewa Daga Ɓangarenmu aka kashe Sarauniya!" murmushin gefen baki yayi sannan ya ce "Babu wani Ɗa daga Gidanku da zai iya shiga nan koda Mahaifinki ne!" "Sai na shiga!" ta faɗa tare da sunkuyawa ƙasa ta zame daga tarkon nasa ta falla da gudu......

Ruwan Kibbau suka fara bata daga ko'ina ana kawo mata hari sai dai sun kasa samunta don ƙwararriya ce ta fannin tsalle-tsalle......
ganin hakan ba zai yi musu ba ya sa suka baza Tarko na Sarƙa suka zarge ƙafafunta...... Haukan ƙarya ta fara yi musu ta hanyar kai musu duka da fizge-fizge, ba shiri suka aika Mutum Ɗaya don sanarwa Yarima halin da ake ciki, ba daɗewa ya dawo yana numfarfashi yana cewa "Ku barta ta shiga!" Kwance ta suka yi ba don ransu ya so ba, ita kuwa ta miƙe ta kakkaɓe gefen zumbulelen skirt ɗinta ta hararesu sannan tayi ciki....
Chapter 11 · 0% Book details