← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 16

Sashe 3

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A zahiri dai tana zaune a gurin ne amma a gaskiyance kwata-kwata hankalinta baya cikin yankin ma gabaki daya bare cikin gidan, tayi matuk'ar zurfi cikin tunanin da yake shagaltar da ita a cikin kwanakin nan, ba zato ba tsammani taji an dafa kafad'arta , dogon numfashi me cike da firgici ta ja gami da zazzaro idanu waje ta tsaya ƙiƙam ko motsin kirki bata yi ba. Sai da ya zauna kusa da ita yayi irin zaman da tayi sannan ya ce "Firgicewar taki har ta kai haka?"
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Ban san kai ne ba"
Murmushin kan la'b'ba yayi kafin ya ƙara sassauta murya ya ce "Meye damuwarki?"
kasancewar basa ɓoyewa juna abunda ya shafe su yasa ta yanke hukuncin gaya masa.
"Ni fa ina matuƙar son in ƙara fita, ba tare da kowa ya sani ba"
kyawawan idanunsa ya zaro akanta a razane yana faÉ—in "What!??...... are serious?" "Yeah" ta bashi amsa kaitsaye, hannunta ya cafka da sauri gami da cewa "Why Kubrah!!? Ke bakya gudun 'bacin rai wai?"
'Dan numfasawa tayi kafin ta ce "I want to see him again, because I always think about him "
"Yasalam!!" Ya furta cikin kad'uwa, cigaba yayi da cewa "What Are You think?, what will you say to him !?"

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)

*Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌🏻👌🏻👌🏻 Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.👏🏻 Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................*

SHARE FISABILILLAH https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw

🪻SAWUN KEKE Season 2🪻
EP .......4
By INDO

Shiru tayi tare da zubawa hannunsa da yake k'ank'ame da nata ido, tana son yin maganar amma abun ya ci tura sai da ya k'ara maimaita tambayar sannan ta iya cewa "Hak'uri!!! Kalmar da zan fad'a masa kenan!!,,, bayan ita ba Ni da wani abun faÉ—ar gareshi a yanzu, amma fa da zan samu dama,,,,, Allah ne kad'ai yasan adadin kalaman da zasu fito daga bakina".
Dogon tsaki ya doka tare da janye hannunsa daga nata ya juya mata ƙeya zuciyarsa na wani irin tsalle..........

"Abee ! can't you help me?, babu wani abu daban da nake tunani bayan wanda na gaya maka!, ko kuskure ne bada hak'urin?"
"Bada hak'uri ba zai taba zama kuskure ba, karya dokar Affah shine kuskure mafi had'ari, kiyi hak'uri Ni kam shirme na bai kai matsayin nan ba, ba nak'i bane k'arfina ne bai kai na gasgata hakan ba"
Hawayen da sukayi kwanton 'bauna a cikin idanunta ne suka samu nasarar saukowa kan kumatunta , cikin sauri ta rik'o hannun Abee da yake shirin tashi ya barta, cikin rawar murya tace "Ban ce dole sai ka temaka min ba, nima ba na so laifina ya shafeka, sai dai yana da kyau in gaya maka kafin na aikata,,,,, amma da zaka temaka min zan yi farin ciki sosai! " ta k'arasa maganar tana murmushin k'arfin hali ga kuma hawayen da suka cigaba da ambaliya a fuskarta......

Tuni idanunsa sun kawo ruwan hawaye , Zuciyarsa tayi wata k'wak'k'warar tsinkewa. Cikin murya mai kama da raÉ—a ya ce " Kubrah ke ce Raunina, ganin hawayenki yakansa na manta cewa Ni namiji ne, faruwar wani abu gareki daidai yake da a sanya Takobi a tsaga Zuciyata, Ni zan cutu Indai har kika fad'a wani hali walau a cikin gida ko kuma a waje,,, Kubrah!!,,,,, Ganin ki cikin wannan yanayin yasa naji ina son shiga lamarin yanzu ba na tsoron abunda zai je ya zo burina shine kiyi farin ciki, amma wajibinki ne ki kula min da kanki sannan ki gujewa Had'uwar mu da Affah, kuma karki manta Affah ya gaya mana cewar Mutum ya fi Aljani illa don haka ki kula"
"Na gode Abee zan yi duk yadda ka ce" ta fad'a tana murmushi.
"In Allah ya kaimu gobe zan shiga Kasuwa daga nan zan sa a yi mana Bincike akansa da inda yake rayuwa, to daga nan ne zan baki dama ki fita, amma zuwa da dawowarki kar ya wuce 1 hour " gyad'a kai tayi gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya.
******************************

Umar da Ammar suna zaune suna fafata Muhawara kamar yadda suka saba a duk tsawon kwanakin nan tun bayan haÉ—uwarsu da Kubrah,,,,,
"A karo na barkatai ina k'ara gaya maka cewa watarana zan k'ara ganinta,,, hakan Zuciyata take gaya min" Umar ya faÉ—a cike da son tabbatar da gaskiyarsa...
"Ita dama Zuciya ai itace me tsara labarai da wanda zai yiwu da wanda ba zai taba yuwuwa ba,,, nima a karo na barkatai ina ka'ra gaya maka cewa Aljanu ne suka fara bud'e maka ido , Kubra É—innan sam ba Mutum ba ce, gabaki d'aya ka zare ka zauce sai surutai da tunane-tunane ! Duk ka dameni"
"Ka zuba ido, da yardar Allah watarana za ka ganta kai ma"

Yana shirin yin magana Yasmin ta shigo tsugul!.. babu ko sallama, tsayawa tayi ta rike ƙugu tana kallonsu kamar yadda suke kallonta sai dai yanayin kallon ya sha bamban , ita kallon raini take musu yayin da suke Binta da Kallon tuhuma.
Taɓe baki tayi gami da doka musu harara ta ce "Mom tana kira"
Daga haka ta juya ta fice tsigal-tsigal tana wata kwarkwasa.
Tsaki Umar ya ja tare da tashi ya bi bayanta yana cewa "Ina zuwa Ammar"

A d'an nesa da Mom ya zauna yana k'ara sauke rumfar ido, ganin yadda take wannan hucin ya tabbata yau Allah ne kaɗai zai ƙwaceshi. "Ban hana ka shigo min da ƙazamin Yaron can cikin Gida ba?, Don ubanka me yasa ba ka jin magana?"
"He's my best friend Mom, Me yasa wai ni bani da Y'anci a Gidan iyayena komai nayi ba daidai bane?"
Sakin baki tayi galala kafin ta ce "Okay har na fara fad'e kana mayar min? Kuma akan wancan kayan dattin?, wai anya kuwa kai ne d'an da na haifa ba canja min kai akayi ba?" Cikin kad'uwa ya d'ago idanunsa wanda suka cika taf da tarin damuwa ya zuba mata gami da cewa "Subhanallah! Mom....." Katse shi tayi ta hanyar É—aga masa hannu gami da cewa "Don't tell me anything!, Kuma yau ya zamo na k'arshe da zan k'ara ganin ka shigo min da wani Matsiyaci gidana; ina so ka je ka yi masa korar kare ka nuna masa kai da shi akwai bambanci!"
Cike da son barin wajen ya mike da sauri ya fara tafiya, tsayar dashi tayi da cewa " "Kuma gobe ka shirya akwai inda za mu je Ni da kai"
Kasa magana yayi kawai ya ci gaba da tafiya, yana jinta ta cigaba da zazzaga Bala,i Yasmin tana tayata.

Katari yayi da Ammar yana shirin fita, cikin sauri ya ce "Ya dai?" Ammar yayi murmushi fuskarsa ɗauke da damuwa yace "Na biyo bayanka ne da nufin in gaisar da Momy sai in yi maka sallama in wuce Gidanmu, yanzu baka buƙatar sake faɗa min saƙon Momy!, Ni a kowane lokaci ƙofar gidanmu a buɗe take gareka, zaka iya shiga lokacin da kake so kuma ka fita lokacin da kaso , saboda kai ma ɗa ne a gidanmu, amma gidanku in sha Allahu ba zan ƙara zuwa ba, ba zan temaka maka mu bujirewa umarninta ba, sai dai hakan sam bai taɓa alaƙarmu ba"
shiru yayi gami da É—aukar idanunsa da suka ciko taf da ruwan hawaye ya zubawa Ammar. Dafa kafaÉ—arsa Ammar yayi gami da cewa "Kar ka ji komai, ni ina tare da kai , kuma nasan kai ma haka"
gyaɗa kai yayi cike da son gazgata abunda Ammar ya faɗa, ɗorawa yayi da cewa "Ka faɗi gaskiya, amma hakan ba zai hana ni baka haƙuri ba Ammar!, a madadin dukkan Ƴan Gidanmu ina me baka haƙuri, kuma ina fatan wataran zaka sake ziyartata a cikin gidan........" katse shi yayi da cewa "Umar indai lafiya ƙalau to babu abunda zai sa na zo gidanku, Ba zan yi fatali da Umarnin Momy ba!, ni yanzu nake son tafiya in zaka kaini to mu je"
Hawayen da yake ta ƙoƙarin dannewa ne suka yi nasarar kwararowa kan kumatunsa, "Ina zuwa, zan kai ka da kaina"
ya faÉ—a gami da nufar hanyar komawa sashinsa domin É—auko key.

washegari.....
Chapter 3 · 0% Book details