← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 16

Sashe 4

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasuwar Kwari..... misalin ƙarfe 3:21pm Ammar yana zaune a shagonsu wanda ya kasance na haɗin gwiwa tsakaninsu , Umar ya faɗo kamar wanda aka jefo daga sama, cikin mamakin ganinsa Ammar ya ce "Laa!" Kafin ya rufe baki Umar ya ce "Meye wani laaa! sai kace wani Mace ??" "To ai ban yi tsammanin ganinka ba ne" ya faɗa yana dariya nemar waje Umar yayi ya zauna sannan ya ce "Momy fa ta kaini inda take son kaini, wai Aure take so in yi ni kuma gaskiya bana ra,ayi" Ammar ya Ajiye wayar hannunsa ya dawo da hankalinsa kan Umar sannan ya ce "Ina ganin kawai ka yi biyayya, kai ma kanka zaka fi samun kwanciyar hankali, maybe zaka dena ma tunanin wannan Aljanar" Murmushin takaici Umar yayi kafin ya ce "Da a ce wata Matar ce daban da zan Aure ta, amma wannan dai ba ta yi min ba, ina son kusanci da wanda zai dinga mutunta ni ya mutunta Abokaina da duk wanda nake mu'amala dashi,,, na rasa hakan daga ƙannena da iyayena zan so in samu daga Matata, amma in na sake na Auri wannan yarinyar zan rasa wannan mafarkin har Abada" ɗan ƙaramin tsaki Ammar yayi kafin ce ""Ba na so ka tsallake wannan damar Bro, kana buƙatar ƙarin kusanci da iyayenka, ina ganin yin hakan zai kawo maslaha amma kai ba ka ganewa" "Indai akan haka ne ba zan gane ba, abu ɗaya ne kawai,,,, nasan na fi su gaskiya, Ammar ko ni bata mutunta ni ba bare kai bare kuma sauran mutanen da suke tare damu, domin Allah in ka ga na Aureta sai tsananin rubutun ƙaddara wanda bana fatansa, don haka ka janye wannan maganar taka, ka ga wata shigar banza da tayi kuwa? wai a hakan zatayi haɗuwar farko da Bahaushen Saurayi irina, haba ! Impossible wallahi" Ammar ya ce "Kana da kafiya Umar, don Allah ka dinga tausasawa akan wani abun mana, Aure fa ba zai taɓa zama kuskure ba" "Amma Aurar Matar da zata haifi Ƴaƴan da basu da rana kasan dai shine mafi girman kuskure ko?, ka manta da ita kawai Ammar,,,,,,, ni fa wallahi da na san Gidan su Aljanar nan da ba shakka ita zan ɗauko in nunawa iyayena a matsayin wadda zan Aura!"
ido Ammar ya zaro tare da faɗin "What!? kai fa ka gama zaucewa Aboki, na gaya maka Aljana ce ba zaka ganta ba!" ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya, Umar ya ce "Ni fa ban yarda ba, kuma in baka sani ba yanzu kullum ji nake tamkar na ƙara kusanci da ita , a duk lokacin da nake tunaninta nakanji tamkar tana kusa dani, haka bugun Zuciyata yake nuna min" "To Allah ya bada sa,a tunda na faɗa ka ƙi yarda, inda zaka yarda ko iya hakan ma ya isa tabbatar maka Aljana ce" "Sai kayi kuma" Umar ya faɗa gami da miƙewa ya nufi wajen Yaron Shagon wanda yake ta fama da costumers.
___________________________________________

Yau.........
akan hanyarsa ta komawa Gida, yana driving yana tunane-tunane bai ankare ba sai da ya kusa yin awon gaba da wani ƙoshashshen Doki a gabansa, da sauri ya taka burki tare da zazzaro ido, a take Zuciyarsa ta fara wani bugu da ƙarfi kamar wanda aka sanyawa wuƙa a maƙoshi ana shirin yankawa.
Cikin sauri ya fito daga motar ya nufo wajen Dokin cike da fatan yayi tozali da wadda Zuciyarsa take marari.

"Umarh!" sai da numfashinsa ya ɗan samu tangarɗa lokacin da zazzaƙar muryarta ta bashi ƙararrawar sanarwa a cikin kunnensa, da sauri ya juyo baya inda yaji muryar ta fito, tuni jikinsa ya fara wata irin karkarwa wadda bai san sanadinta ba, abu ɗaya kawai zai iya bada shaida shine muryarta da kuma yadda ta furta sunansa cikin salo mai matuƙar taɓa zuciya da ƙwaƙwalwar Ɗan Adam sun fi komai dagula masa lissafi, sai da yaji tsigar jikinsa ta tashi yarrr!!!.
Babu shakka da yana da nutsuwa a wannan lokacin da ya yi nazari akan kalaman Ammar na cewar Aljana ce , sai dai ba shi da wannan ƙwarin gwiwar a yanzu.

Ido ya zuba mata yayinda ita ma take kallonsa idanunta cike taf da hawaye, Cikin rawar baki ya furta sunanta cikin salo makamancin nata sai dai shi ya haɗa da alamar tambaya "Kubrah!!!?" gyaɗa masa kai tayi alamar eh, kafin ta sakar masa murmushi wanda ya ƙara susuta shi, "Ka yi haƙuri Umar!!" ta faɗa tare da yin gefe da kanta.
É—an numfasawa yayi kafin ya ce "For what?! me kikai min?, wai Kubrah don Allah wacece ke??"

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)

*Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌🏻👌🏻👌🏻 Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.👏🏻 Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................*

SHARE FISABILILLAH https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw

🪻SAWUN KEKE🪻
Season2
EP .......5
By INDO

Shiru bata bashi amsa ba sai ma kallon Ahmadi dake gefenta takeyi.

Umar bai fahimci me yake faruwa ba sai da ya ga Ahmadi ya fara zayyano masa cewar Gimbiyarsa tana da muradin bashi haƙuri ne koda babu silar hakan. "Amma ai ita na tambaya ba kai ba, ba zan ƙara samun kyautar Jin zazzaƙar muryarki bane Kubrah!" sai da yayi ƙoƙarin gaske sannan ya iya zuwa ƙarshen maganar duba da yadda take futowa da ƙyar tamkar wanda bai taɓa kurɓar ruwa ba.

Ahmadi zai ƙara magana ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu, ta sauke ajiyar Zuciya sannan ta fara magana tana kallon Ahmadi "Ahmadi ka gaya masa na Fasa masa abunsa ranar nan, ni ban san meye daɗinsa ko akasinsa ba, abu na biyu kuma nasan dole sai yayi jinya Bisa wurga masa Kibiya da nayi duk da bata same shi sosai ba amma dole zata taɓa shi!, sai abu na uku shine shigowa rayuwarsa da nayi, dole in bashi haƙuri akan hakan domin ban sani ba Farar Sa'a ce ko akasinta"
Tuni Umar ya zagayo kusa da Ahmadi don ya fi kallonta da kyau ko zai fahimci halin da yake ciki, lissafin bai warware masa ba sai ma ƙara shiga wani lulluɓin da yayi, ya fahimci cewa tana magana ne akan wayarsa da ta fasa da kuma ganinsa ma da tayi gabaki ɗaya, cike da ƙarfin hali ya ce "Amma wacece ke? a ina kike, meyesa na ga kin bambanta da Matan da na sani a wannan Nahiya tamu?, kuma meyesa ba zaki yi magana dani kai tsaye ba dole sai ta hanyarsa?" murmusawa tayi kafin ta ce "Ahmadi ka gaya masa cewa na yiwa ɗan uwana Alƙawarin kalmar haƙuri kawai zan faɗa masa, sauran tambayarsa kuma basu da amsa domin gabaki ɗaya Rayuwata Tambaya ce babba, wadda ni kaina ban san amsarta ba; Bayan ka isar da saƙon sai mu tafi don gudun saɓa lokaci" da sauri Umar ya ce "Na ji ki, ba sai ya faɗa ba, hakan ma na gode, iya ganinki ma babbar Ni'ima ce Allah yayi min Allah ya kai ki gida lafiya yake wannan kyakkyawar halitta!!"
Ya ƙarasa maganar gami da sakin murmushi wanda yayi daidai da zubowar hawayensa ba tare da ya shirya ba.
Lumshe idanunta tayi gami da jan dogon numfashi ta sauke shi tare da nannauyar ajiyar Zuciya, hawaye sun so ɓalle mata amma tayi ƙoƙarin dakatar dasu, ba tare da ta ce komai ba ta haye Dokinta ta zabure shi.

Ya É—an jima a wajen yana tunane-tunane har sai da wani me mota ya fara masifa akan cewar ya tsaya kan hanya sannan ya koma Motar ya janyeta, don ma cikin unguwa ne da Allah ne kaÉ—ai yasan go slow da zai tara.

fasa shiga Gidan nasu yayi ya sauya akalar tafiyar zuwa gidan su Ammar domin ya bashi tabbacin yau ya ƙara ganin Kubrah.
koda ya zayyana masa abunda ya faru ƙin yarda yayi sai cewa yayi Aljanun ne dai suka ƙara buɗe masa ido. Dolensa ya haƙura tare da fatan Allah yasa wataran tazo a lokacin da suke tare.

____________________________________

Abee ne ya kalli Kubrah wadda tayi zurfi a cikin tunani, ya murmusawa gami da cewa "Yanzu kin yi farin ciki ko?, kuma mun yi sa,a Affah bai gane ba"
"Ba ƙaramar sa,a muka yi ba , kuma nayi farin ciki amma bai kai yadda nayi tunani ba; nayi zaton bayan haka zan manta dashi kwata-kwata amma sai naga ashe ba haka bane, sai ma sauya salo da tunanin nawa yayi" "To fa!, kin iya tarairayar masifa ke kam; to ni dai bana son ƙara jin wani abu akansa, ki manta dashi kawai" ɗan kallonsa tayi ta ɗauke kai sannan tace "Dole ne hakan ai, duk da cewar akwai wuya, yau fa 1 week kenan da haɗuwarmu amma har yanzu komai sabo yake a wajena" "Kin ga , canja wata maganar na gaji da wannan" murmushi ta saki kafiin ta ce "Wadda zan kawo ɗin ma ba mai kwantar da hankalj ba ce, ina son Waya ne kuma da gaske nake, in ban sameta ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba!"

zaro ido yayi yana cewa "Waya dai irin wadda kika fasa wa Umar??!!" gyaɗa kai tayi tana cewa "Ba shakka ita nake nufi , inaso in san amfaninta da kuma haɗarin nata" ya wangame baki zaiyi magana tayi saurin tsayar dashi ta hanyar riƙo hannunsa tana cewa "Don Allah kar ka ce min a'a, ka temaka min in samu!"
Idanu ya tsira mata jiki a sanyaye yace "Amma ke meyasa ba kya ƙauracewa abunda ya zamo tashin hankali ?" marairaicewa tayi tace "Abee don Allah!, nasan akwai rigima amma fa sai in Affah ya sani, kuma ba za mu bari ya sani ba" nazari ya ɗan yi kafin ya ce "Kin tabbata ba zaki bari ya sani ba?" gyaɗa kai tayi tana murmushi, ya ɗan numfasa sannan ya ce "Na san Uncle Isah ya kusa zuwa, in ya zo sai mu yi masa maganar, kin ga ba mu san inda ake siyarwa ba" da sauri ta ce "Yawwa hakan yayi, Allah yasa yazo yau" "Ba zai zo ba ma karki sa rai" Ya bata amsa gami da jan hannunta suka bar wajen.
Chapter 4 · 0% Book details