← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 16

Sashe 7

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ɗan gyaran murya Abee yayi sannan ya ce "Da fatan kana lafiya!" sai da Umar ya furzar da zazzafar iska sannan ya amsa "Ina lafiya!" ''Okay nice, na gode da karrama Ƴar Uwata da kayi kuma har ta samu kyauta daga gareka, amma don Allah na roƙe ka ka dena mafarkinta! sannan ka dena tunaninta"
zumbur! Umar ya miƙe tsaye kamar an tsikare shi, wani duhu ne ya fara zagaya masa tun daga cikin ƙwaƙwalwarsa har zuwa idanunsa hakan ya tilasta masa durƙushewa kan gwiwoyinsa, cikin wata sarƙaƙƙiyar murya wadda take nuni da tsananin hargitsin da ya shiga ya ce "Amma me yasa??, baka yi tunanin cewa ba ni na zaɓawa kaina hakan ba Yaya!"
kallon-kallo Abee da Kubrah sukayi suna haɗa ido tayi ƙas da kai hawayen da take ta ƙoƙarin dannewa suka fara silalowa kan kumatunta, janyota ya ƙarayi ya rungumeta acikin ƙirjinsa yana ɗan bubbugar bayanta a hankali...... sai da sakanni suka shuɗe sannan Abee ya mayar da raddi ta hanyar cewa "Na san ba zaɓinka bane, don inda hakan ne babu yadda za a yi Kubrah ta dinga tunaninka, Amma zaka iya ƙoƙartawa ka dena ta hanyar mantawa da ita, itama a nata ɓangaren hakan zata faru; Na gode da karamcinka garemu!"
Daga haka ya katse kiran gami da jefar da wayar can gefe.
Zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Kin gani yanzu wayar tana nema ta zama wani sabon makami da zai Yaƙi rayuwarmu, Kubrah don Allah ki manta dashi!" "Zan yi ƙoƙari sosai don ganin nayi hakan, amma idan na kasa ba zaka kasance a tsagina ba Abee?!" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka,,,,, girgiza mata kai yayi yana ƙara rungumeta tuni hawaye suka fara aikin kwarara daga idanunsa.

Umar ...... Kuka kawai ya saki daga zaunen da yake, don kuwa ba ya jin zai iya wani abu bayan haka.
Ranar haka ya kwana yana tunane-tunane kala-kala har da mafarkai.
Washegari kamar lokacin da ya saba tashi yau ma ya tashi, bayan yayi shirin fita ya nufo Falo.. Yasan bai fiye samun Breakfast ba hakan yasa bai wani damu ba da shirin fitarsa yake fitowa.
Sai dai yau abun ya sha bamban, duk da ba baƙon abu bane ya fito ya ga babu motsin Kowa a Parlour amma da kamar wuya ace ko alamar mutane babu a gidan Musamman Mommy .
Sauya akalar tafiyarsa yayi zuwa ɓangaren Mommy koda ya isa bai ganta ba,. Sai da ya karaɗe gidan da nema amma bai ga Mommy ba, Haka Yasmin da Yaseer, duk da shi Yaseer daman ba fiye kwanan gida yayi ba.
Jiki a sanyaye ya dawo Falo zuciyarsa cike da tunane-tunane kala-kala.
Inda Mommy ta saba zama yaje ya zauna kamar zai fashe da kuka, karaf! idonsa ya sauka kan wata falleliyar takarda dake kan center table ɗinta, cikin sauri ya sa hannu ya ɗauka ya buɗe ta, karo ya ci da rubutun Mommy ya tsaya karantawa "Mun tafi Spain da ni da Ƴaƴanmu wanda suke jin maganar mu kuma suke bin tsarinmu!" iya abunda ya gani kenan, wurgi yayi da takardar ya miƙe bai san sanda ya fara rero kuka ba.
Da ace da me rarrashinsa a gidan da ba abunda zai hana shi ya zauna ya ci kukansa ya tsire sai dai kashh!.... gidan ma jinsa yake kamar kango gabaki ɗaya yayi masa ƙunci kamar an jefa shi a kurku.
Ficewa kawai yayi ya kama hanyar kasuwa, tun yana kukan har ya gaji ya share hawayensa don ya san babu mai rarrashinsa.

Koda ya dawo da yamma yayi niyar zama amma sai ya kasa, gidan ya zame masa tamkar Ƙaya, haɗa Ƴan Kayansa yayi a travel bag ya ɗauki Key ya nufi wajen Mota, sai da ya shiga ya bata wuta sannan ya kira Ammar, cikin sa,a kuwa ya ɗaga yana cewa "Yanzu nake bawa Ummi labarin Aljanarka! sai gashi ka kira!" cike da damuwa yace "Aljanar wasu zaka ce, ni na riga na manta da ita, ba itace damuwa ta ba yanzu"
gyara zama yayi yana cewa "To meye damuwar?" "Tambayarka zanyi Wane Hotel ne ya É—an fi abun mutunci a garin nan? bana son wanda Æ´an iska sukayi yawa a cikinsa"
Tsaki Ammar ya ja yana cewa "An gaya maka ni Karuwa ce da zaka tambayeni Hotel?, ni banga abunda zai haɗaka da Hotel ba ma in ba neman jaraba irin na Ƴaƴan Masu kuɗi ba!"
tuni hawayen da yake ta yiwa shamaki suka samu damar fara aiki akan fuskarsa, cikin rawar murya ya ce "Ammar kai ma ci min mutuncin zakayi kenan?, ni in zaka faÉ—a min ka faÉ—a min in tafi, iskancin nake so na fara nima"
jin alamun kuka acikim maganarsa yasa Ammar ya saita nutsuwarsa yace "Ƙarya kake wallahi!, ka gaya min gaskiyar abunda ya faru!" cikin muryar kuka ya ce "Su Mommy duk sun tafi Spain sun barni ni kaɗai a wannan Gidan!, ni kuma ba zan iya zama ba gaskiya gwara nayi garari a titi har zuwa lokacin da zasu dawo!, Wallahi Ammar ni ban taɓa Alfahari da kuɗin Babana ba hasalima gani nake kamar Dukiyarsa ce silar rasa farin cikina!, na kasa samun gatan da kowane Ɗa yake samu a wajen iyayensa, kar ka ƙara kira ɗan masu kuɗi bana so!, ni ga Allah nake gareshi na dogara, ƙoƙari nake kullum don ganin na inganta kaina har in samu damar inganta Ƴaƴan da zan haifa!, ni ba zan yi rayuwa irin ta iyayena ba Ammar!! , b..... !" ganin bashi da niyar yin shiru yasa Ammar dakatar dashi ta hanyar cewa "Ya isa haka mana Umar, ɗakinmu nida Al'amin yana da ɗan girma zai ishe mu ka tawo nan kawai"
"A'a Ammar ai abun kunya ne ma hakan!, ranar nan fa ina ji ina gani Mommy ta kore ka daga Gidanmu, kuma ta ce kar ka ƙara zuwa, sai kawai in tawo gidanku to da wane idon zan kalli su Ummi kenan?!" ɗan ƙaramin tsaki Ammar yayi kafin ya ce "Ranar nan da ka faɗawa Kubrah cewa ni Ɗan Uwanka ne na ɗauka fa da gaske kake, ashe ƙaryar banza ce!" da sauri ya ce "Kar kayi min gurguwar fahimta, ba haka bane ba fa" "Okay to in ba haka bane ka tawo Gidanmu da zuciya ɗaya, kuma Ummi ma ta ce tana nemanka yanzun nan " daga haka ya katse kiran yana cewa Ummi "Na gaya masa, nasan zai tawo tunda yaji kinyi magana"...
Umar ..... In banda yaji Ummi ta magantu da ba abunda zai sa shi zuwan, haka nan ya tattara ya tafi can.

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)

SHARE FISABILILLAH *🪻SAWUN KEKE...🪻*
season *2*

EP .......8
By INDO
https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw

*SAWUN KEKE...(Ba a Gane Gabanka!......)*

Kubrah.......
Duk suna zaune kaf a Babban Parlour suna hira har da Mammi,,, sai ga Affah kamar an jefo shi, a tsakiyarsu ya tsaya fuskar nan a murtuke kamar anyi yaƙi akanta cikin dakakkiyar murya ya ce "BA NI WAYAR HANNUNKIi!"
a tare sukayi kallon kallo su duka huÉ—un yayin da Zuciyoyinsu suka fara luguden Bugawa a tare......
Kasa magana Kubrah tayi sai girgiza kai da tayi alamar a'a.
Cikin sigar mamaki Mammi ta ce "Meye haɗin Kubrah da waya kuma Akhee!? gaskiya ina ga ka saɓa fahimta n...." ɗaga mata hannun da yayi ne yasa tayi yin shiru da bakinta, maimaitawa Kubrah tambayar yayi hallau dai ta ƙara girgiza masa kai.
Mariam ta buɗe baki zatayi magana tayi saurin rufe shi sabida mahangurɓar da Affah ya bawa Abee, ƙara Kubrah ta ƙwalla gami da zamewa daga kan Kujera ta durƙushe a ƙasa tana faɗin "Affana don Allah ka tausaya mana don Allah!" ....
Zahra da Abee da Saim ma durƙusawa sukayi kan gwiwoyinsu suna famar zazzare ido, ganin haka ya sa Mariam ta zube a ƙasa itama jikinta na wani mugun ɓari da karkarwa...

Duka Abee ya shiga rarraba musu a tsakanin su biyun amma hakan bai sa sun magantu ba sai aikin bayar da haƙuri wanda yake ƙara tunzura Zuciyar Affah.
Tun Mammi bata magana har ta gaji ta fara magiya da roƙon yayi haƙuri amma ko gezau beyi ba don kuwa ba ta ita yake ba.

Sun ɗauki lokaci suna shan duka amma taurin kai ya hana su fito da wayar, ganin abun nasu yayi yawa yasa Affah ya finciki hannun Abee ya fara jansa ƙiririri!!!,,,, rufa masa baya sukayi suna magiya da roƙon sassauci, zuwa yanzu Zahra da Kubrah tuni kuka ya ci ƙarfinsu, Mammi ma bin bayansu tayi tana cewa "Ya kamata ku faɗi gaskiyar abunda kuka aikata Kubrah!, na tabbata da bakuyi komai ba ba abunda zai faru"
Cikin kuka Kubrah tace "Don Allah Mammi ki ce ya ƙyale Abee, be yi laifin komai ba!"
ai kafin Mammi tayi wani yunƙuri tuni Affah ya shige inda yake son zuwa wato Kitchen,,, kai tsaye Cooker gas ya kunna gami da jan hannun Abee ya ɗora akai..... Zuwa yanzu har Mammi ma sai da ta fashe da kuka tana cewa "Haba Akhee in ba kai ba waye yake yin izaya da wuta saikace wani kafiri?!! don Allah ka bari kar ka nakasta min shi don Allah!, in ka tambayesu a hankali zasu gaya maka ba sai ka azabtar dasu ba!! " Banza yayi mata kamar be san tana yi ba, Abee dai yana karɓar azaba iya azaba sai ɓarza kuka yakeyi.
A burkice Kubrah ta miƙe tana cewa "Af.. Affah!! zan ɗauko! wallahi zan ɗauko don Allah ka ƙyale shi, Affah ! don Allah!!"
janye hannun Abee yayi daga kan wutar yana cewa "Okay Go ahead!" mayar da kallonsa yayi kan Mammi kafin ya ce "You See?! waÉ—annan da kike ganinsu Zuma ne sai da wuta!" mamaki da al'ajabi ya hana Mammi cewa komai sai ido da take rarrabawa cike da mamakin tana zaune haka turus! a gidan ashe har waya suka kawo suka ajiye bata sani ba.
Chapter 7 · 0% Book details