Sashe 5
Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk wannan lokacin zaman saurare Kubrah take yi, bata da burin da ya wuce ta ga Uncle Isah ya zo, yaci ace yayi zuwa uku amma a wannan karon ko É—aya bai yi ba, ko da tsara shirin nasu yau kwanaki uku kenan. Har ta gaji ta fara cewa zata je ta nemo da kanta.
Suna zaune a tafkeken Falo wanda ke a tsakiyar Gidan suna hira sai ga Affah ya shigo , kallon inda suke yayi gami da cewa "Uncle Isah ya zo" bai jira cewarsu ba ya wuce gaba, da sauri Kubrah ta miƙe tana cewa "To bari in kai masa abun sha" dakatawa yayi da tafiyar hakan bai wadatar ba har saida ya juyo ya ƙare mata kallo bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya.
ÆŠan numfasawa tayi kafin tace Abee zo ka raka ni.
Saim ma miƙewa yayi yana cewa , "Ni ma bari in tashi tun kafin a tashe ni"
A Falon da suka saba zaman karatu suka same shi, tuni har an kawo masa kayan ciye-ciye, Kubrah tafi kowa matsawa kusa dashi, ko gaisawa bata bari sun yi ba ta ce "Uncle Don Allah irin wannan abun nake so!" Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Wanne kenan Ƴata?!" Abee ta kalla cike da son ƙarin bayani, ɗan sosa ƙeya yayi sannan yace "Uncle,! She's talking about phone" shi kansa maganar ta girgiza shi, bai san lokacin da ya zazzaro ido gami da maimaita sunan "Phone?" ɗin ba, gyaɗa kai tayi domin ba shi tabbaci.
a gefe guda Saim da Zara suka haɗa baki wajen jefo mata tambaya Saim ya ce "What will you do with it?!!!!!" Zahrah ta ce "Me za kiyi da waya kuma??" "Nothing ! kar ku damu kanku, kawai ina so ne" shiru ne ya ratsa tsakani mamaki ya hana su ƙara yin magana, Abee da Kubra kuwa jiran amsa suke daga Uncle Isah.
sai da ya sauke gwauron numfashi sannan ya ce "Gaskiya ba zan iya baki wannan goyon bayan ba, ba naƙi bane amma kiyi haƙuri kawai!" sai da ya rufe baki sannan ta ɗauke kallonta daga kansa gami da cewa "Shi kenan, zan nema da kaina bana buƙatar goyon bayan kowa tunda Abee yana tare dani"
Bai ƙara yin magana akai ba sai ma cewa da yayi "Yau kawai na zo ganinku ne, ba zan iya baku kowane darasi ba don banida isasshiyar lafiya"
Saim ya ce "Ai na ga alama, me yake damunka ne Uncle?" rausayar da kai Uncle Isah yayi tare da yin dukkan ƙoƙarinsa wajen danne sirrin dake ɓoye a Zuciyarsa, '"Saim koda na yi maka bayani ba zaka gane ba, idan ba damuwa zaku iya tafiya ku turo min Yallaɓai?"
Kubrah ce ta fara tashi fuuuuu!! tayi gaba Abee ya bi bayanta yana kiran sunanta.
Saim da Zahra ma tashi sukayi suka nufi cikin gidan dan isar da saƙonsa.
Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke yana rarraba idanu. Duk da Sanyin AC dake dukansa hakan bai hana zuffa tsatstsafo masa ba, duk lokacin da ya tuna ƙudurinsa akan mai gidan nasa yakanji Zuciyarsa ta buga da iya ƙarfinta!.
Yana nan zaune yana tufka da warwara Affah yayi sallama, a É—an firgice ya amsa gami da gyara zamansa yana kakalo fara,a.
Zama Affah yayi yana tsura masa ido kafin yace "Me ya faru da kai ne?" da ƙyar ya nemo jarumta ya aza sannan yace "Babu komai kwana biyun nan ne nake wani Ɗan zazzabi, amma ba wata damuwa"
gyaɗa kai yayi alamar ya gamsu da hakan, ya ƙara da cewa "Ina saurarenka da fatan dai ba Yara ne sukayi wani shirmen ba!" daidaita nutsuwarsa yayi sosai sannan yace "Alfarma nake nema in ba damuwa!, Ƴata Fatima ita kaɗai ce nake zama in bata labarinka,,,, a wannan lokacin ta ce min tana so tazo nan ta ɗan kwana biyu , shine nace zan nemi wannan Alfarmar!". Murmusawa Affah ya ɗan yi kafin ya ce "Shine abun neman Alfarma?, a gaya mata nan ma gidansu ne!"
shiru Uncle Isa yayi saboda wani mashi da ya soki Zuciyarsa...... "Me yasa rayuwa ta canjani haka? wanda yake zaune dani da zuciya ɗaya shi nake shirin cutarwa!" abunda ya faɗa kenan a zuciyarsa, Affah ne ya katse shi da cewa "Akwai wani abun ne bayan wannan?" cikin sauri ya girgza kai gami da cewa "A'a babu, so nake in tambaya Yaushe zan kawo ta?" "Duk lokacin da ta shirya ƙofa a buɗe take" ya faɗa yana ƙoƙarin tashi,
ƙarawa yayi da cewa "Na gode da ƙoƙarinka gare ni" Uncle Isah yayi murmushin ƙarfin hali kafin ya ce "Nauyi ne wanda ya rataya a wuyana, ka dena yi min godiya Yallaɓai!" Affah ya ɗan murmusa ba tare da ya ce komai ba.
Yau Tun da Safe ta shirya ta saci hanya ta fice daga gidan, babu wanda ya san ta fita sai Abee shi ma don ya zame mata dole ta faÉ—a masa.
Kai tsaye Ƙofar gidan su Umar Ahmadi ya ci burki da ita, cike da girmamawa ya kalleta gami da cewa "Wannan shine gidan da Suke rayuwa shi da iyayensa!" "Yanzu ta yaya zan ganshi?, gashi Gidan Babba ne sosai, ban san a wane sashi zan iya samunsa ba!" Ahmadi ya ce "Gimbiya kuma Uwar Masu gida!! wannan gida duk girmansa bai kai ya Gidanku ba! don haka memansa ba zai mana wahala ba Ranki-ya-daɗe , naga idan Baƙo ya zo aika yake yi cikin gidan ayi sallama, ina ga hakan zamuyi ko ?"
É—an tsaki tayi tace "Ashe ka san da hakan ka zo ka ajiye ni a nan?".
"A gafarce ni" ya faÉ—a yana rusunawa.
Waige-waige ya fara yi ko zai samu É—an aike amma fayau kasancewar Unguwar manyan gidaje ne zalla shiru babu masu fitowa zaman kan layi"
ganin wankin hula yana neman kaisu dare ya sa Kubrah ta sa kai ƙofar gidan ta fara nocking.
ta ɗan jima tana yi kafin Mai Gadi ya buɗe ya leƙo yana cewa "Kai Bana son hayya-hayya!! waye ne!!??" ganin wata sabuwar halitta a gabansa ya sa yayi saurin saita nutsuwarsa ya gyara tsayuwa yana zuba mata ido.
"Na ce ko zaka kira min Umar?" caraf! ya amsa da cewa "Ke a suwa? Umar gadan-gatsai babu taunawa?! Yallaɓai ko kuma Me gida haka za ki ce, ki bar gani Allah ya hore miki kyau ɗinnan wallahi in ba a ban izini ba ba zaki shiga ba ehe!".
murmushin takaici tayi kafin ta ce "A gurinka ne yake da wannan sunan, amma ni a wajena da kai dashi duk bayi ne!" yadda ta faɗi maganar cike da ƙwarin gwiwa yasa Mai gadi ya sarara don kuwa irin kuɗi da ƙarfin ikon da Mahaifin Umar yake dashi ko masu kuɗin ba zasu iya ɗaga baki su kira shi bawa ba, jin hakan daga gareta kuwa ya tabbatar masa bata fito ba sai da ta shirya.
ƙare mata kallo yayi sama da ƙasa kafin ya jinjina kai yana cewa "To yanzu na gane!, Girl friend dinki ne shi ko?, bari in kira shi yi haƙuri Hajjaju" kafin ya juya tace "Malam! ni Mace ni ce girl friend ɗin ba shi ba, ƙato sukutum dashi" ,, Yanzu zaka iya kira min shi?"
"An gama!" ya faÉ—a gami da nufar inda zai samu Æ´an aikin da aka sahalewa shiga gidan.
(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)
SHARE FISABILILLAH
https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw
*🪻SAWUN KEKE🪻*
Season 2
EP .......6
By INDO
Fitowarsa kenan Parlour da shirin tafiya Wajen nemansa Shamsiyya ta ƙaraso tana raɓe-raɓe a can gefe ta sanar masa saƙon. Bata faɗi suna ba sai suffanta kamanni kamar yadda Mai gadi yayi mata.
yana jin haka zuciyarsa tayi wata ƙwaƙƙwarar bugawa.
Da sauri ya nufi hanyar fita yana gyara zaman bag É—insa akan kafaÉ—arsa.
"Wata Matsiyaciyar ka gayyato mana kuma?" Mommy da ke kan stairs tana saukowa ta jefo masa tambayar .
jim! ya ɗan yi kafin ya ce "Duk da ban san asalinta ba amma na tabbata ta fi ƙarfin Tsiya Mommy!, ko ni da nake ɗan masu arziƙin ni ba Komai ne a wajenta ba! matsayina bai wuce na Boyi-boyinta ba!"
suman tsaye Mommy tayi hakan yasa ta gaza furta wani kalamin, shi kuwa hakan dama ce ta fitarsa.
tuni ya fice harda gudu-gudu.
Tana tsaye a inda take É—azu fuskarta babu alamun annuri.
"Kubrah!!" bakinsa ya furta a lokacin da idanunsa suka sauka akan fuskarta.
Ɗago idonta wanda ya fara rikiɗa yana sauya kala tayi ta zuba masa kafin ta ce "Shine sai an wulaƙanta ni saboda na zo neman alfarma wajenka?" kallon kallo suka yi shi da mai gadi wanda yake maƙale a bayansu yana kallon ikon Allah.
Da sauri ya ce "Wallahi umarnin Hajiya Babba na cika Yallaɓai!"
maida hankali Umar yayi zuwa kanta, cikin tattausar murya ya ce "Amma ni ban san da hakan ba bare in wulaƙanta ki, kuma bana fatan ki nemi Alfarma a wajena Kubrah!, saboda nasan alfarmarki ta wuce ki tsaya nemanta!, ina yi miki barka da zuwa ƙofar gidanmu!" ya ƙarasa maganar yana murmushi.
bata san lokacin da ta saki murmushin ba, ta É—an numfasa sannan tace "Ai Kowa a Fadarsa Sarki ne Umar!, ina gaisuwa!" .
Lumshe idanunsa yayi gami da jan dogon numfashi , jin kansa yake kamar me shirin faÉ—awa dogon suma, Zuciyarsa sai dukan sittin saba'in take amma duk da haka yau a nutsuwarsa yake ba kamar wancan lokacin ba.
"Amma akwai Wanda in Sarauta ta kai Sarauta duk inda ya shiga ma Sarki ne, hatta Sarakunan ma gani za kiyi suna zube gwiwoyinsu a ƙasa suna ɗibar Gaisuwa"
murmusawa tayi gami da cewa "Amma dai anan kai ne Sarkin!, don haka zan je maganata kai tsaye, ina son siyen Waya ne da fatan kai ma ba za ka ƙi bani goyon baya ba"
Kasancewar bai san dawan garin ba buɗar bakinsa yace "Abu me sauƙi ma irin wannan shine sai kin tsaya wahalar da kanki??,,,,, amma wani hanzari ba gudu ba waye bai baki goyon baya kan siyenta ba?"
farr! tayi da ido kafin ta ce "Wannan abunda ya shafi rayuwata ne, yanzu dai ka raka ni in siya don sai na zaɓa" ta ƙarasa maganar tana miƙawa Ahmadi hannu, da sauri ya ƙaroso gami da miƙo mata wata ƙaramar jaka dake hannunsa.