← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 16

Sashe 13

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru suka ɗan yi na wucin gadi sannan Abee ya ce "Ban san da wane yare ya kamata in miki bayani ba, amma jikina yana bani akwai abunda zai faru a nan gaba kuma ba lallai ya zamo me daɗi ba, sannan ina ganin kamar rayuwa zata ɗan canja mana koda na ɗan lokaci ne" a take jikinta ya ƙara yin sanyi ƙalau, ita ma takan fuskanci irin yanayin da Abee yake fuskanta sai dai bata ɗauki hakan matsayin komai ba face ruɗanin Soyayyar Umar.
Ta buÉ—e baki zatayi magana Mariam ta riga ta da cewa "Tsuntsun da ya ja ruwa dai shi ruwa ke jibga!"
Dukkansu suka zuba mata kallo cike da son fashin baƙi akan kalamin nata, ƙarasowa tayi tana girgiza da kwarkwasa ta zauna kan Kujerar dake fuskantar 2seater ɗin da suke kai, "Rana Dubu ta ɓarawo, rana ɗaya tak! ta me kaya..." ta ɗan murmusa sannan ta cigaba da cewa "Ba ni na faɗi hakan ba fa Hausawa ne suke faɗe, na ga kun fara fusata!"
cikin mamaki Kubrah ta ce "Amma me yake damunki ne ? na ga kin canja fa"
taɓe baki tayi ta ce "Murna nake na san wani ɓoyayyen Sirri naku, kuma gaf nake da tona muku asiri kowa ya san abunda kuke shukawa"
kallon kallo Abee da Kubrah suka yi cike da mamaki da rashin fahimtar abunda take son faÉ—e.
"Na san kuna fita kuma ku bar shiyyar nan, abu ɗaya na kasa ganewa shine inda kuke zuwa, to ina son sani idan kuma kun ƙi faɗa min babu shakka zan tona muku asiri har in ƙara da sharri!" ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki.
Murmushin kan laɓɓa Abee yayi gami da gyara zamansa ya kashingiɗa a jikin tattausan Filon kusa dashi, Kubrah ta buɗe baki zatayi magana ya ɗaga mata hannu tayi shiru.
Ganin haka ya sa Mariam ta fara shan jinin jikinta, duk da tana da makamin da zata iya Yaƙarsu amma tana matuƙar tsoron Shu'umancin Abee....
Katse mata tunanin yayi da cewa "Yarinya ! idan ba ki san waye Abee ba baki san Kubrah ba ki je ki bibiyi Tarihi!, ba ke ba ko Babanki Uncle Isah bana jin yana da zarrar da zai sa mu faɗa masa inda muke zuwa, idan kin shirya faɗe Bismillah ki je ki taka bakin Faranti abun ciki ya tarwatse ayita ta ƙare, ni zanyi murna da hakan yayin da ke kuma zai zamo miki silar zubar hawaye daga nan har ƙarshen rayuwarki, ko shakka babu sai na zamo miki alaƙaƙai a rayuwa kuma sai na yi silar rabuwarki da jin daɗin Duniya!!"
Dim! dimm!!! Zuciyarta ta fara tsalle tana faɗuwa tana tashi, lokaci guda jikinta ya fara tsuma ga wata zuffa da ta fara keto mata..... da dafe-dafe ta tashi ta nufi hanyar fita idanunta har wani duhu-duhu suke nuna mata, haka kawai bata san dalili ba tayi matuƙar firgita da jin kalamansa, wata Zuciyar tana gaya mata ya riga ya gane zaman Leƙen asiri take a Gidansu wata Zuciyar kuma tana gaya mata bai gane ba kawai wani mugun ƙullin zai yi mata.
Ɗakinta ta koma ta rufe ƙofa ruf! sannan ta lalubo wayarta ta kwanta kan gado tayi lif! tana sauraran yadda ƙashushuwanta da jijiyoyinta suke ƙoƙarin daidaita kansu.
ta daɗe a haka ko motsi bata yi kafin ta samu ƙwarin gwiwar turawa Abbinta kira.
Ba ɓata lokaci ya amsa muryarsa a ƙasa-ƙasa ya ce "Ina Asibiti Mariam!, sun ƙara yiwa Rahma Allura ciwonta ya ƙara tashi yanzu an kwantar da ita ma, don Allah kiyi ƙoƙari mu samu wata makamar ko dan lafiyar Ƴar Uwarki!" "Abbi kar ka damu zata warke in sha Allah" jinkirtawa tayi saboda kukan da yake shirin kufce mata, sai da tayi da gaske sannan ta hana shi fitowa sai dai ta kasa dakatar da ƙwallarta wadda ƙunci da tashin hankali suka sa tayi zafi gami da raɗaɗi a cikin idanunta.
"Zan cigaba da ƙoƙari akan wanda nake yi, amma fa nima zan iya fuskantar haɗari a rayuwa, matsalar da take faruwa komai nasu sirri ne a tsakaninsu bana iya gane wani abun da suke yi, kuma na tambayi inda suke zuwa ɗin kamar yadda ka ce amma ban samu amsa ba sai ma barazana da na fuskanta" Abbi ya goge ƴar ƙwallarsa sannan ya ce "Kar ki damu Mariam, abinda nake so dake kar ki ƙara tambayarsu don in suka ce za su yi miki abu to yana iya faruwa, haka nan zamu haƙura mu fawwalawa Allah koda hakan na nufin Rahma za ta rasa ranta, kar kiyi dai abunda za ki jefa kanki cikin matsala nima ki jefa ni, in akayi haka anyi mutuwar kasko kenan, gwara waninmu ya mutu wani ya tsira, gwara waɗannan azzaluman su kashe ni su kashe Rahma, na san zaki kula da Mamanki da Ƙaninki, idan hakan ta faru kuma kar ki yarda ki bar inuwarsu, anan ne zaki fi samun tsar..........." ɗif! network ya ɗauke gashi dai kiran na aiki amma bata jinsa shi ma baya jinta, dolenta ta katse ta ƙara kira sai dai network ya ƙi bata damar kaiwa gacci,, tura wayar tayi ƙarƙashinta ta fashe da kuka me tsuma Zuciya, lallai abun ya ci tura tunda har Abbi ya fara bar min wasiyya, wai kuwa shi Wannan Mutumi wane irin Mutum ne da manyan Hatsabibai na Duniya suke nemansa???? ........ wannan tunanin ne ke famar kaikomo a cikin ƙwaƙwalwarta.

Affah.......

Cikin Ƙasaitaccen Takunsa yake ratsa sassa daban daban na cikin Masarautar, wadda ta sha ado ta ko'ina kamar ba za a Mutu ba, duk inda ya ratsa gaisuwa ake miƙo masa ta ko'ina har ya isa Babban sashi Na wadda ake yiwa laƙabi ga Uwar Masarauta!.

kai tsaye ya nufi tafkeken Gadonta wanda da an kalla za a hango tsantsar Mulki da gadara a tare dashi, duba da yadda ya sha kyakkyawar shimfiÉ—a ta Alfarma ga adon Gold ta ko'ina a jikin Gadon...

Durƙusawa yayi a Gabanta tare da ɗora hannunsa kan Kyakkyawar Fuskarta wadda ta nuna alamun Manyanta, "Mother!!!" ya furta cikin muryar raɗa.........
cikin nutsuwa ta dafa hannun nasa sannan ta buɗe gwara-gwara idanunta ta zuba a kansa, kamar ba zata yi wani motsi ba sai kuma Ta yunƙura ta tashi zaune, lallausan murmushi ta sakar masa gami da shafar kansa sannan ta ce "Kubrah da Abee sun ƙwace min Ɗa,,,,, He forgot his Mother!" "Ban isa in manta da ke ba Ammyna!, fatana lafiya ce tasa kika kwanta a wannan lokacin" ɗan numfasawa tayi sannan ta ce "Haka ne,! lafiya ce ta sa na kwanta duk da cewar tunaninka ne ya sa nake jin rashin walwala amma yanzu i'm Okay tunda na ganka" "I'm so sorry my Mother!" ya faɗa cike da ladabi......
Murmushi ta yi kafin ta miƙe ta gyara zaman Zankaɗeɗiyar doguwar rigarta sannan ta fara takawa one by one Tamkar wadda take gaba da ƙasa, miƙewa Affah yayi ya bi bayanta yana cewa "What Happen!" ya tabbata akwai wata a Ƙasa.
Tana tafe yana binta har suka ƙarasa wajen Window sannan ta tsaya tana leƙen tsirarun Mutanen da ke kai komo a can ƙasa, nannauyan Numfashi ta sauke sannan ta fara magana "A wajena kai ne wanda kula dai kai ya zame min dole, a wajenka kuma Su Kubrah su ne Dole!, Kai kana da ni su kuma suna da kai, ka cigaba da kula da su ka ji Ɗana!!" gyaɗa kai yayi alamar To sannan ya ce "Kubrah tana bani ciwon kai Mommah!, gashi na tarar da canji akan Fuskarki"
Murmushi me ɗan sauti tayi kafin ta fara magana "Nasan ka san Rayuwa takan iya canjawa, sai dai sanin lokacin canjawar tata sai Rabbissamawati, wani abun duk Dabararmu sai ya faru har mu dinga ganin kamar sakacin mu ne ya jawo haka, kar ka ɗauki wani abun a matsayin Gazawarka ka dinga dangana shi da Mu'ujizar Ubangiji , kasan Alƙawarin Allah ba ya gushewa ba tare da ya cika ba!,,, wani abun sai ka kawar da kai sannan ka zamo me haƙuri akansa amma Tabbas akwai Abunda yake shirin Faruwa sai dai sanin abun da kuma lokacin faruwarsa Sai Allah; abu ɗaya nake so ka ƙara riƙewa shine ninka Kusancinka da Ubangijinmu Allah; sannan kulli-yaumin ka dinga tuna cewa Ƙaddarata daban Taka daban haka ta Ƴaƴanka daban, ina fatan ka fahimta !" jinjina kai yayi kafin ya ce "Na gane Mommah! amma me yasa wani abun daban yake bibiyar rayuwata da IYALINA ??" "Ƙaddara kenan kowa da kalar zanen ta shi, ka sa a ranka komai zai wuce watarana sai dai aji Tarihi!" ya numfasa sannan ya ce "Shi kenan!, ina Ɗan Uwana?" "Yana Sashin Sarki, zaka je ne mu tafi tare ?" da kai ya bata amsa, ta ɗan numfasa kafin ta fara tafiya, bayanta ya bi Zuciyarsa cike taf da tunane tunane kala-kala.

*🪻SAWUN KEKE🪻*
season *2*

By INDO

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)

WANNAN LITTAFIN NA KUÆŠI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci É—aya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun)

SHARE FISABILILLAH
Ep............14

Sin........

Prince Jiehong yana Zaune kan kujera da take fuskantar wadda King Yizheng yake kai sun saka Table a tsakiya suna famar kallon Takardar Taswira dake kan Table ɗin, sun ɗan jima suna nazari sannan King Yizheng ya katse shirun da cewa "Dajin yana da Sarƙaƙiya sosai sai ka nutsu zaka iya shiga cikinsa don kuwa akwai Sojoji masu tsaronsa!"
cikin nutsuwa ya É—ago kai ya kalli Mahaifin nasa kafin yayi magana cikin salon miskilancinsa "Zanyi yadda ka ce !" King ya saki murmushin jin daÉ—i, duk duniya gani yake nasararsa tana tare da mutuwar Matarsa tunda gashi yanzu Prince Jiehong baya tsallake duk wani umarni na shi, ta haka ne kuwa zai yi nasarar cimma muradensa.
Bayani ya cigaba da yi masa sosai akan Taswirar, wani abun yana fahimta wani abun kuwa tunani ya hana shi gane me ake nufi........

....................

https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw
Chapter 13 · 0% Book details