Sashe 12
Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Yana Tsaye gaban wani Ƙaton Table yana shirin Ɗaukar glass cup wanda ke ɗauke da ruwan Giya a ciki, da sauri ta zuro hannu zata ɗauke cup ɗin sai dai batayi sa'a ba don kuwa duk yadda ta kai ga zafin namanta ya fi ta, wata kyakkyawar damƙa ya yiwa hannun nata sai da ta saki ƙara sabida azabar da ta ratsa ta har cikin kanta.
Da ɗayan hannun ya ɗauki cup ɗin ya kurɓi abunda ke ciki sannan ya watsa mata guntun a fuskarta. Runtse idanunta tayi da ƙarfi tana ƙoƙarin gogewa da ɗayan hannunta don kuwa ya shiga idonta sosai. Bai bata damar hakan ba ya fizgota da ƙarfi ta faɗo jikinsa ya matse ta da ƙarfi,,, hakan ya tilasta mata buɗe idanun nata ta jefa su cikin nasa, sai da ya cire mayafin da ta rufe fuskar dashi sannan ya ce "Raina ya fi na Mamata Ƙwari, ba za ku iya Kashe ni ba!" "Koda kowa zai iya yin hakan ni ba zan iya ba!" da ƙyar ta fizgo maganar don tuni numfashinta ya fara sarƙe saboda muguwar matsar da ya yiwa ƙirjinta a cikin nasa.....
Murmushin gefen baki yayi wanda in mutum ba ya da lura sosai ba zai gane yayi ba ma.
"Ƙiyayyar da nakewa Mahaifinki ta sa bana son in dinga ganinki" "Ni kuma ba zan ƙauracewa idanunka ba komai yawan azabar da zaka yi min, kuma ba zan taɓa dena sonka ba" ɗan sunkuyawa ya ƙara yi fuskarsa ta kai daf da tata sannan ya ce "Ranar da na na kashe ku ke da shi za ki dena ko?" kawar da kanta tayi gefe ta ɗan girgiza kai ba tare da ta yi magana ba, wasu zafafan hawaye na azaba gami da ƙunar Zuciya suka fara tsiyayowa daga idanunta. Hannunsa ɗaya yasa ya matse kumatukanta da ƙarfi irin yadda ake wa yaro ɗurar magani,, sai dai salon ya bambanta don shi nashi yadda yasan zataji zafi yayi, juyo da fuskarta yayi saitin tasa sannan ya ce "Har kin kai matakin da zanyi magana kiyi shiru ko?" "Za ka kasheni fa!" ta faɗa cikin muryar da take nuna ta kusan shiɗewa. Murmushin nasa na masifa yayi ya ɗan sumbaci laɓɓanta sannan ya ce "Na fi so ki Mutu, amma ba yanzu ba sai lokacin da na gama cikawa Babana Muradensa sannan zan Kashe ki in kashe Mamanki don ina so Zhengyu ya san zafin Mutuwa" bai bata damar yin magana ba ya rufe bakinta da nasa ya fara kissing ɗinta..... Zuwa yanzu hawayen nata sun tsaya cak idanunta sun firfito waje guru-guru ta fara kokawa da numfashinta wanda yake barazanar ficewa ya barta......
Sai da ya tabbatar ta kusa sumewa sannan ya janye bakinsa daga kan nata ya hankaɗa ta da ƙarfi ta faɗa kan Table sannan ta dawo ƙasa ta baje tana wani mugun tari kamar me shirin barin Duniya.
Juyawa yayi ya fice cike da rashin imani , bai damu da halin da ya barta a ciki ba hasalima burinsa kenan a kullum ya dinga yi mata izayar da wataran za a wayi gari da kanta ta ce bata Ƙaunar ganinsa.
Aikinsa kenan kullum in suka haÉ—u sai ya tabbatar yayi mata abinda zata daÉ—e yana mata ciwo.
tana cikin wannan halin na uku Bala'i Ƙartin Sojojinsa suka shigo suka ɗaure ta tamau da Sarƙoƙi suka kinkimo ta suka fitar da ita can bainan-nasi sannan suka yasarta a wajen.
Ta daɗe tana majaujawa a wajen Sannan ta iya miƙewa tana tafiya tana haɗa hanya ta nufi sashinsu.
Kafin ta isa labari ya iske Prince ZhengYu, a tsaye ta same shi yana safa da marwa, tsoro ne ya fara ɗarsuwa a Zuciyarta tuni jikinta ya ƙara ɗaukar tsuma, kasa ƙarasawa wajensa tayi don ta san shi akwai baƙar Zuciya ga saurin hannu. Duk da haka bata tsira ba bata san ta ya akai yazo kusa da ita ba sai jin saukar Yatsunsa biyar tayi a kumatunta, sai da yayi mata uku kyawawa sannan ya fara zazzaga bala'i ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba...........
*🪻SAWUN KEKE🪻*
season *2*
By INDO
(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)
WANNAN LITTAFIN NA KUÆŠI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci É—aya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun)
SHARE FISABILILLAH
Ep...........13
https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw
Nigeria.....
Kubrah da Abee yau ma a karo na barkatai sun yi sa'a babu wanda ya san sun fita har suka je suka dawo, sai da suka daÉ—e da dawowa ne Mamma ta fara nemansu sai suka nuna mata bacci ma suke yi.
"Ni fa ina ganin gwara mu faɗawa Affah Alaƙarki da Umar!" Abee ya faɗa yana kallon Kubrah, numfasa tayi sannan ta ce "A'a gaskiya ina jin tsoro, ina ganin hakan ba zai sauya komai ba, kuma jikina yana bani ba lallai ya amince da shi ba, ka ga in ka faɗa yanzu kawai zai raba ni dashi ne, ni kuma ban shiryawa hakan ba!" Shiru ne ya ratsa tsakani kafin Abee ya ce "Amma kin iya wauta Kubrah!, kin san kina jin hakan kuma kika fara? kuma me yasa zaki sako Umar a cikin rayuwarki indai kin san za ki rabu dashi?, ai da kin sani baki faɗa masa kina son shi ba" "Ba ni da zaɓi ne!, ina matuƙar son shi Abee, koda zan rabu dashi ina son alaƙarmu ta yi tsayi fiye da haka, shi yasa na zaɓi ɓoyewa Affah!" "Shi kenan, na fahimce ki amma Allah yasa hakan ya haifi Ɗa me ido, kin san halin shi ba sai na gaya miki ba, ni ina mamaki ma da kike fita ba tare da ya sani ba a wannan lokacin"
''Ni ma ina wannan mamakin, amma nafi tunanin hakan yana da nasaba da Tasirin da Umar yake dashi gareni, Allah ne kaɗai yasan me ke ɓoye a cikin hakan!"