Sashe 8
Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Afujajan Kubrah ta dawo Kitchen É—in jikinta sai rawa yake kamar mazari, duk numfashinta ya susuce.
miƙawa Affah Wayar tayi tana shirin yin baya taji ya haɗa da hannunta nata ya ɗora akan wuta,,, da sauri ta yarda wayar akan wutar aikuwa ta shiga ƙonewa, ihu ta fara kurmawa tana bashi haƙuri,,, "Waye ya siya miki ita??, na ce waye ya baki?????" ya yi tambayar cikin tsawa da barazana!" haɗa baki suka yi wajen bashi amsa Abee ya ce "Ni ne!!" ita kuma tace "Abee ne!" sakin hannun nata yayi kafin ya kifa mata wani zazzafan mari wanda yasa ta fara majaujawa a filin wajen, Saim ne ya ƙoƙarta ya riƙe ta suka faɗi rajaf!! a ƙasa.
A kausashe Affah yace "In na ce A'a ina nufin A'a!!, muddin aka samu wanda yake jin ya isa ya karya doka ta a cikin gidan nan babu shakka zan taka shi in yanka masa wuya!, ni ba a nuna min taurin kai!"
yana kaiwa nan ya nufi hanyar fita a fusace! kamar zai tashi sama.
Mammi ma dasa nata faÉ—an tayi, ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
Sai da ta gama sannan ta nemo magani ta basu suka sha, ta shafa musu na shafawa.
misalin ƙarfe 2:00am.........
Cikin sanɗa Mariam ta buɗe ƙofar bedroom ɗin da ya kasance masaukinta, leƙawa tayi waje ta kalli ko'ina sai da ta ga babu motsin kowa sannan ta koma ciki ta danno ƙofar gami da saka mukulli ta rufe. Wajen kayanta ta koma ta fara laluben Ƴar wayarta da Abbi Ya bata a sirrince,, tana cirowa ta lalubo Lambarsa wadda ita kaɗai take karakaina a cikin wayar.
Duka ɗaya Uncle Isah ya ɗauka yana ambaton sunanta, sai da yaji ta amsa sannan hankalinsa ya kwanta, ya sauke ɓoyayyar ajiyar Zuciya kafin ya ce "Tunaninki nake yi, nan zaman da nayi jiran kiranki nake yi, haka kawai jikina yake bani kamar wani abun na faruwa" haɗiye yawun da ya tokare mata maƙoshi tayi kana ta ce "Abbi Ya jikin Rahma?, da fatan dai duk kuna lafiya!" "Muna lafiya , Rahma kuma tana cigaba da shan Magani da Alluran da suka ce a dinga yi mata"
"To Alhamdu lillah!" ta faɗa kafin ta cigaba da cewa "Abbi ina matuƙar jin tsoron zaman Gidan nan Don Allah ku sauya wata shawarar nidai in dawo Gida!, wallahi Abbi duk ranar da ya gane muna yi masa zagon ƙasa ko shakka Babu sai ya ƙona ni da raina!, ashe haka yake Abbi?! Ƴaƴan cikinsa ma ba zaka so ka ga izayar da yayi misu ba Ɗazu saboda sun siyo Waya!" ta ƙarasa maganar cikin rauni tamkar zata fashe da kuka, Uncle Isa ya ce "Haka yake tamkar Garwashi! kallonsa daga nesa abun marmari amma da zarar ka taɓa zai saɓule maka fata!!, idan kuma kika iya binsa a hankali akansa zaki dafa Abincin da zaki ci ki rayu,,, wannan ita ce Suffarsa, baya duba da wanda ya taɓa shi kawai hukuncinsa yake ga kowa" Kuka ta saki tana cewa "Abbi nidai ina so in dawo Gida don Allah!" "Kiyi haƙuri Maryam, Banida zaɓin da ya wuce hakan, ki duba halin da ƙanwarki take ciki mana!''
"Amma....." katseta yayi da cewa "Calm down Mariam, nasan kafin safiya zeyi kamar ya manta abunda ya faru, to haka nake so ki manta ke ma, ba na so wani abu ya dinga firgita ki, ki saki jiki a cikinsu kin ji ko?, in sha Allahu ba abunda zai faru!"
gyaɗa kai tayi tana cewa "Shi kenan !" Uncle Isa yace "Wayar tana hannunsu ne?" "A'a ya ƙona ta haka ya dinga ƙona musu hannu fa Su Abee" "Kar ki damu, komai zai wuce, zamu yi nasara in sha Allah, good night!" yana kaiwa nan ya katse kiran.
Jiki a sanyaye Ta mayar da wayar zuciyarta cike fal!!! da tunane-tunane, babu shakka in banda tana son lafiyar Æ´ar uwarta da ba abunda zai sata wannan aika-aika.
Ta daɗe tana tunanin ta yaya ma zata samu kyakkyawar alaƙa tsakaninta da su, Don kuwa ba wani janta a jiki suke yi ba musamman Abee, sai me binsa Kubrah!.
Washegari
Sai lokacin da ta tabbatar zata samu Mutane a Falo sannan ta fito bayan ta gaisar da Mammi ta ƙara da cewa "Ina son in dubo Abee da Kubrah!" ido Mammi ta zuba mata kafin tace "Kar ki damu sun ji sauƙi kuma suna samun kulawa sosai, in kuma ganin nasu ya zama dole zan shiga in fito miki dasu sai ku gaisa" girgiza kai tayi alamar a'a duk sai taji ta tsargu lokaci ɗaya, duk da ba wannan ne karon farko na nuna mata iyakarta ba.
Cigaba tayi da ƴan sabgoginta sai dai hankalinta ya karkata sosai kan su Abee, musamman dai shi don ta tabbatar yafi shan izaya, tun tana sa ran ganinsu cikin sauƙi har ta fitar don kuwa dare yayi amma ko motsinsu babu.
Kasa jurewa tayi sai da ta tambayi Mammi, Mammi ta kalli inda Abbi yake cike da son samun amsa, ɗan jim tayi kafin tace "Za ki dubo su ko?" da sauri ta gyaɗa kai, Mammi ta miƙe tana murmushi gami da cewa "Abokin faɗa yau babu lafiya ko?, na ga ma ba kwa wani jituwa da Abee sosai!" Mariam ta ce "Laifinsa ne wallahi, ya fiye girman kai gashi miskili ne ɗan rainin hankali jin kansa yayi yawa!"
Mammi ta ce "To yau dai kam Babbar giwa ta faÉ—i!"
rasa amsar da zata bayar tayi don haka ta rufe bakinta, Bedroom ɗin Kubrah suka fara zuwa tana kwance ta dunƙunƙune a cikin Bargo sai sautin kukanta ke tashi a hankali.
Jiki a sanyaye Mammi ta janye Bargon tana cewa "Wai ke an ce miki kuka yana yaye damuwa ne? duk wannan ciwon kan da kike yi bai isheki ba sai kin ƙaro wani!"
ƙoƙarin tsayar da kukan ta fara yi tana cewa "Abee fa bashida lafiya!, in nayi laifi ni ya kamata a hukunta ba wai a hukunta shi akan laifina ba" Mammi ta ce "Ke ma ba lafiyar gareki ba fa, kuma ke ce zakiyi ƙoƙari ki sama masa zaman lafiya, gardamarki ce take sawa ake yawan ƙuntata masa, shi da yake bashida wannan gardamar taki ai kin fishi samun zaman lafiya, tunda kin riga kin san irin hukuncin da ake muku"
Mariam ta ce "Kuma haka ne gaskiya ki rage Kubrah tunda kun ga Abbi yana da fushi sosai" shiru tayi don kuwa ba ta san ma abunda zata faÉ—a ba, Mammi ta juya tana cewa "Ki dena kukan nan ya isa haka, kuma ki sha magani kafin kiyi bacci" bata jira amsarta ba ta fice Mariam na biye da ita.
Abee yana zaune a bakin gado ya zubawa hannunsa wanda ya sha wuta ido, Mammi tayi sallama tace "Ga Mariam zata duba ka" da sauri ya janyo Blanket ya lulluɓawa jikinsa kasancewar daga shi sai wando three quarter.
a bakin ƙofa ta coge tace "Sannu Allah ya sawwaƙe! ya kamata ku rage fitina!" zuro kai yayi ta cikin bargon ya zuba mata wani shegen kallo kafin ya ce "Bana son shishshigi ba kwarjini!, abunda ya shafe ni ne nida ƴar uwata , bana buƙatar tsarinki a ciki"
jiki a sanyaye tace "Yi haƙuri, bakin nawa ne akwai surutu amma ba zan kuma ba in sha Allah" Mammi ta ce "Ka sha maganin kuwa?" gyaɗa kai yayi, ta ƙara da cewa "Amma dai baka ƙara yin zazzaɓin ba ko??, kuma ƙunar ta dena raɗaɗi?" "E, yanzu ba inda ke min ciwo" tace "Yayi kyau, sai da safe"
amsawa yayi yana maida hankalinsa kan Mariam wadda jikinta yayi matuƙar sanyi, taɓe baki yayi ba tare da yayi wani sharhi akai ba.
(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)
SHARE FISABILILLAH
Ep.......9
https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw
Umar........
Sai da Ummi ta fara haɗawa da faɗa bayan nasihar da take yi masa sannan aka samu sauƙin damuwar da ya jefa kansa a ciki
Abun ya haɗe masa da yawa ga tunanin su Mommy ga tunanin Kubrah, yayi iya bakin ƙoƙarinsa don ya cireta daga tunaninsa amma ya kasa, sai dai yanzu abun ya ragu ba kamar Da ba don kuwa an ɗauki tsawon sati biyu harda ƴan kwanaki bai ƙara jin ɗuriyarta ba.
"Kamar wani Jariri haka ka zama yanzu" Ammar ne yayi maganar yana ƙoƙarin zaunawa a kusa da shi..
Murmusawa yayi kafin ya ce "Ina iya ƙoƙarina don ganin na jure Hukuncin da ƙaddarata ta yanke akaina, menene kuma abunda banyi ba?" "Na ga ba yau ne farko ba da su Mommy suka tafi wani wajen suka barka, amma naga borin naka da rigima na wannan karon yafi na kullum" Ɗan jim!! yayi kafin ya ce "Kullum fa sa rai nakeyi in ga rayuwar ta canja, burina in ga an samu cigaba amma sai naga baya ake yi, a lokacin da nake cikin damuwa lokacin da ya kamata Iyayena su yi min addu,a su dinga kwantar min da hankali a lokacin ne suke duk meyuwa don ganin sun ƙuntata min kawai don suna fushi dani akan gaskiyata!" Ammar ya ɗan numfasa sannan ya ce "Haƙuri zaka yi, ni ina ji a jikina komai zai dawo daidai"
"To yayi, Allah yasa" Umar ya faɗa sannan ya cigaba da cewa "Nayi Sa'a Allah ya rufa min Asiri ban ƙara ganin Aljanata ba, yanzu na rage tunaninta kuma na rage yin mafarki da ita kamar dai yadda Yayanta ya faɗa"
"Barka da arziƙi , Allah yasa ta tafi kenan, shiyasa naga har ka ɗanyi ƙiba ashe?" Umar ya fashe da dariya yana cewa "Kaji iskanci, wato har nayi ƙiba!, Allah ya shiryeka!"
Cigaba sukayi da hirarsu cikin nishaÉ—i gami da bawa juna kulawa.
haka rayuwar ta cigaba da tafiya a kowane ɓangare wataran daɗi wataran akasinsa......
Ammar yana duk ƙoƙarinsa wajen mantar da Umar damuwar da take barazana ga lafiyarsa.
a É“angaren su Kubrah ma tarzoma ta lafa, Affah yakan zauna su ci Abinci tare su yi hira tare har da Raha, sai dai Æoyayyen sirrin dake tsakanin Kubrah da Abee yakan yi barazana ga farin cikinsu a wasu lokatan.
a ɓangaren Maryam ma tana iya bakin ƙoƙarinta wajen zayyanawa Abbinta duk wani Motsi da akeyi a gidan, cikin sa,a Affah bai gane halin da take ciki ba.