Sashe 16
Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Ihu ta kurma a karo na ba Adadi tare da tattaro dukkan ƙarfinta ta bangaje shi da Ƙarfi har sai da yayi baya taga-taga kamar zai faɗi ............
Bata tsaya jiran komai ba ta falla da gudu tana dafe da ƙirjinta da ya bayyana sakamakon Yaga mata riga da yayi.....
a tunaninta gudunta zai iya tseratar da ita, sai da ta ji ƙafafunta sun harɗe ta faɗi ƙasa tim!! sannan ta gane bahagon tunani take yi. ihu ta ƙara kurmawa tare da yunƙurawa zata miƙe, sai lokacin ta lura wani kalar ganye me yaɗo ne ya ɗaɗɗaure mata ƙafa har ya jaza mata faɗuwa. cikin zafin nama da bata zata tana dashi ba ta fara ƙoƙarin cire ganyen sai taga ya ƙara kame hannunta ya ɗaure, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" ta furta cikin ɗaga murya, tashin hankali ba a sa masa rana,
Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin irin wannan zai faru da ita a rayuwa ba, bata taɓa zaton laifin da tayi zai sa ta girbi irin wannan ɗanyen hukuncin ba.........
Muguwar cafkar da ya ƙara yi mata ce ta dawo da ita hayyacinta, ta saki wani matsanancin kuka tana cewa "Ban yi maka komai ba don Allah kar kai min haka, wallahi ban faɗa ba ka yi haƙuri!!, ba zan ƙara shiga rayuwarku ba, ka duba girman Allah ka ƙyale ni kar ka lalata min rayuwa!"
Idanu ya zuba mata ƙur!!! yana jin wani irin bahagon yanayi yana ziyartarsa.
Idanunsa da suka koma Blue color tuni sun cika taf da ruwan hawaye, wani sashin na zuciyarsa na tunzura shi wani sashin kuma yana shirin fara tausayinta.
Wata gagarumar guguwa ce ta ƙara tunkaro wajen da ƙarfi ta sure shi ta watsar a ƙasa,,, "Abeeee!!!" ta ƙwala masa kira cikin tashin hankali da ruɗani. guguwar tana wucewa ta faɗa kan wata bishiya daga haka ta dena ganin ƙyallinta sai dai jinsa tayi yayi sufa akanta Tamkar wani yunwataccen Zaki.........
Ihu da neman ɗauki gami da jero Addu'o'i shine abunda take iyawa dan kuwa gabaki ɗaya ji tayi kamar an ɗaure mata hannaye da ƙafafunta a cikin ƙasa.......
Tana jinsa yana nashi gurnanin gami da wasu Surutai wanda bata taɓa jin irin Yaren ba a duk tsayin Rayuwarta.
Lokacin da ya gama wulaƙancinsa ya sauka daga kanta ta riga ta zama marabarta da Gawa kawai ita akwai rai a jikinta, sai sa'a ɗaya idanunta da suke a buɗe suna gani dishi-dishi da kuma tunaninta da bai gushe ba..... tana iya ganin lokacin da ya miƙe yana bubbugar kansa da ƙarfin gaske yana kuka , kai tsaye Wajen Tafkin Ruwan da ya ƙawata wannan Yankin na Dajin ya nufa yana tafe yana haɗa hanya, daga haka bata ƙara sanin inda kanta yake ba....................
a ɓangaren Kubrah kuwa tana kwance kan Kushin tana kallon sama sai gani tayi wani turnuƙun harshen wuta ya tawo kanta yana tuƙuƙi gami da hayaƙi..... kafin ta kauce daga wajen tuni ya faɗo yif!!" a saitin ƙirjinta kuma ya shige ciki.
A take tayi kukan kura ta tashi tana zunduma ihu, a take jijiyoyin jikinta suka fara tashi rututu suna bayyana kansu daga cikin farar fatarta sun koma baƙaƙe wulik, idanunta kuwa farin yana nan a farinsa baƙin kuma ya koma Ja da yarfi-yarfi Baƙi.
Miƙewa tayi ta runtuma da gudu tayi hanyar waje.
Babu kowa a Falon sai Mammi, bin bayanta tayi da gudu tana ƙoƙarin riƙota amma ta kasa tuni ta fice ta sa kai cikin Dajin tana falla gudu, ba takalmi ba Ɗankwali.......................
*Last free page*
*ƙarshen fejin kyauta*
*🪻SAWUN KEKE🪻*
season *2*
(*Daga yanzu sai wanda ya biya kudin Karatu ne zai karanta. Naira 400 ne kacal)*
Ga wanda suke son Karantawa ga lambar wayata nan
09079885632
SHARE FISABILILLAH