← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunsa ya ware akanta cike da mamakin furucinta, da sauri ya riƙo hannunta gamida fincokata ta faɗa jikinsa ya matseta da ƙarfi sannan ya murmusa ya ce "Ke ba komai bace a wajena Xiang, tunda kika furta nasan zaki aikata min har fin haka, don haka zan aika ki inda ba za ki san abinda nayi ba bare ranki ya ɓaci.."
Kafin ta gama fahimtar inda ya dosa ya zaro ƴar ƙaramar wuƙa a jikinsa ya soka mata a maƙoshi.
Ihu Hadimarta ta kurma tare da yin kukan Kura ta cukume shi tana shirin ɗaukar tashi rayuwar sai dai kash!!! cikin sauƙi itama ya aikata inda ya aika Queen Xiang wato Lahira, sai da yayi mata kaca-kaca da wuƙar sannan ya koma gaban Matarsa ya rungumeta ya kurma gagarumin ihu sannan ya fara Kuka kamar ransa zai fita ....

Ihun da ya kurma bai zame ko'ina ba sai cikin Kunnuwan gudan jininsa wato PRINCE JIEHONG Shigowarsa kenan cikin Masarautar ya dawo daga Farauta , jin haka ya sa shi fallawa da gudu ya nufi sashin Mahaifin nasa.
Kasancewar Yasan inda yake tun kafin ya fita yasa bai sha wahalar iske su ba sai dai tashin hankalin da ya gani bai taɓa Tsammanin irinsa ba a duk tsawon rayuwarsa.
"Maaa!" Ya furta da ƙarfi tare da cukumar gawarta yana duba jikinta, ɗago ido yayi yana yiwa Mahaifinsa kallon tuhuma, da hannu yayi masa nuni da Hadimar Queen Xiang, cikin muryar kuka yace "Itace ta kashe min Sarauniyata! saboda tazo zata kashe ni Queen Xiang ta shiga tsakani shine ta kasheta ba tare da duba yardar da mukayi da ita ba!" kukan ya cigaba da yi na tsawon sakanni kafin ya cigaba da cewa '"Na kashe ta, kuma zan kashe duk wanda yake da sa hannu aciki, sai da na gaya mata ta dena zuwa nan da kowa amma bata ji yanzu kalli abunda ya faru..." Kuka me ƙarfi ya ƙara saki tare da ƙanƙame hannun Queen Xiang.......

Zazzare ido a tsakanin Mutane ukun kawai Prince Jiehong yake yi, yayin da Zuciyarsa take zaɓalɓala, babu ko shakka ba zai taɓa ragawa duk wanda ya zamo silar Mutuwar Mahaifiyarsa ba.......

sun daɗe cikin wannan yanayin kafin Prince Jiehong ya miƙe ya nufi hanyar fita, ganin haka yasa Sarki ya bi bayansa da gudu-gudu yana ɗan murmushi, ya tabbata da ta hanyar Tsafi ya kashe Queen Xiang da sai Yarima ya gane shi ya aikata, shiyasa yayi dubarar saka wuƙa dan ya wanke kansa daga zargi, yanzu kuwa tarkonsa ya kama Zaki.

Kaitsaye muhallin Hadimar Queen ya nufa ya zaƙulo Ƴar Budurwar Ƴarta dake cikin gidan ya watsota waje.
a gaban kowa yayi mata kisan Gilla sannan ya watsar da gawarta ya koma.....

A zahiri King Yizheng nuna baƙin ciki da Alhini yake yi, Zuciyarsa kuwa farin ciki ne fal a cikinta, ya tabbata Ɗansa baya zarginsa sannan kuma a yanzu duk Umarnin da ya bashi da hanyar da ya ɗora shi su zai bi tunda babu me rusa masa shiri.

Kafin ka ce me! Masarauta ta rikice an kasa gane menene yake faruwa a cikinta, hankalin Mutane da dama yayi matuƙar tashi.....
Sai da King yasa aka tara Mutane sannan ya sanar da Mutuwar Matarsa da kuma silar Mutuwar tata,,,, tuni tsanar Duk wanda yasa hannu aka aikata tayi tsiro a zukatan al'uma.
Mutuwar tayi majaujawa da Mutane, Masu kuka nayi masu alhini nayi wasu ma tashin hankalinsu ya wuce suyi kukan.
Ta samu wannan gatan a wajen Mutane ne saboda tausayinta ga talakawanta da kuma Adalci da take yi ga kowa.

*🪻SAWUN KEKE🪻*
season *2*

By INDO

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU....)

WANNAN LITTAFIN NA KUÆŠI NE....
SHARE FISABILILLAH
Ep.........11

Kaitsaye inda gawar Queen Xiang take ya koma gami da tsayawa akanta yana kalla,,, duk da cewar a burkice yake amma sai yaga kamar akwai bambanci da yadda ya barta ɗazu..... kamar wadda aka motsata kokuma ta motsa kanta, Tunowa da yayi cewar lokacin da suka fita King Yizheng ne ƙarshen fita sai ya kwantar da hankalinsa bisa cewar King ne ya motsa ta don dama yana rungume da hannunta.

https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw

Haka akaita Bikin Mutuwar Queen har na tsayin kwanaki biyu sannan Ƙura ta Lafa a lokacin ne King Yizheng ya mayar da hankali wajen fanɗarar da halayen Prince Jiehong tare da dasa masa son Mulki da ƙarfin iko gami da tsanar dukkan wanda yayi yunƙurin dakatar dashi zuwa ga manufarsa...............

Nigeria......

Wannan daren na yau Abee da Kubrah jinsa suke tamkar daren Mutuwarsu duba da yadda yayi musu ƙunci tamkar wanda aka jefa a kurkukun bala'i,.... Kubrah tunaninta akan Abun ƙaunarta ne sai kuma wani yanayi da take ji a jikinta mara daɗi, Abee kuwa abun ya tarar masa da yawa Ji yake tamkar wani gagarumin abu na shirin Faruwa dashi ko kuma ga Ƴar Uwarsa, sai dai duk iya nazarinsa ya kasa gane ko wane irin abu ne kuma ta ina zai ɓullo.

Washegari....

Tun safe ta fita domin HaÉ—uwa da Umar.....
Kaitsaye gidan su Ammar suka nufa kamar yadda Ahmadi ya gaya mata ya koma kwana acan.

Zuwansu yayi daidai da fitowar su Umar da nufin tafiya Kasuwa, Umar yana cewa Ammar "Su Momy sun dawo, na kusa komawa Gida"
Ammar ya ce "Amma da zaka É—auki shawarata kawai ka je ka Auri wadda Mommy tace, ina ganin hakan zai kawo zaman lafiya tsakaninku, saboda........"
maƙalewa Maganar tayi lokacin da idanunsa suka sauka akan Kubrah dake famar kallon Umar kamar wani Jaririn Watan Ramadan.
"Umar gata nan fa!" sai lokacin Umar ya juya saitin inda take don bawa Zuciyarsa tabbacin abunda take gaya masa. Ido ya zuba mata suka shiga yiwa juna kallon-kallo .
Ahmadi ne ya katse shirun da cewa "Tuba nake Uwar ÆŠakina, bamu da isashshen lokaci don nasan akwai dogon bayani a gaba!"
Numfasawa ta yi kafin ta fara takawa zuwa inda yake, cikin takunta irin na Ƙasaita me nuni da zallar izzar dake yawo a cikin jininta.
sai da taje gab dashi sannan ta tsaya gami da kawar da kanta gefe, ta É—an lumshe ido ta buÉ—e sannan tace "Ko zan iya samun lokacinka a yanzu?, ba Umarni bane kana da damar zartar da ra'ayinka!"

Sai da ya sauke zazzafar ajiyar Zuciya sannan ya samu zarrar cewa "Barka da zuwa ƙofar gidanmu... kina da damar dakatar dani daga dukkan wani uzuri da nake dashi domin lokacinki yana da matuƙar Daraja a gareni"
murmushin gefen baki tayi ba tare da ta ce uffan ba.....

shiru ne ya ratsa wajen na É—an lokaci har Ammar ya je ya É—auko Kujerun Roba guda biyu ya kawo ya ajiye sannan ya ce "Ina ganin ku zauna maganar zata fi daÉ—i!"
Umar ya ɗan murmusa kafin ya kalli Kubrah ya ce "Bismillah!" Juyawa tayi ta kalli Ahmadi kallo irin na neman izini ko kuma shawara,,,,, rusunawa yayi yana cewa "Umar Amintacce ne gareki Shugabata!" ɗan matsakaicin numfashi ta ja ta sauke sannan ta ƙarasa kan kujerar ta zauna gami da harɗe ƙafafunta Tamkar a Fadar Kakanta.......

Zama Umar yayi sannan ya ce "Ina saurarenki, Allah yasa ba laifi nayi ba!" jim!! tayi kafin ta ɗan girgiza kai ta ce "A'ah, Kawai dai abunda nake tunani nake son gaya maka" ya buɗe baki zaiyi magana ta katse shi da cewa "Zaka iya zamowa Bango gareni?,,,,,, zaka iya zama Jigona daga yanzu Har Bayan raina?" idanu Umar ya zazzare akanta tare da yin suman Zaune , gabaki ɗaya wutar kansa ta ɗauke ba abunda yake ganewa sai Kalamanta da suke maimaita kansu acikin ƙwaƙwalwa da Zuciyarsa.....
sai da Ammar ya ɗan ranƙwashi kansa sannan ya dawo hayyacinsa, tsananin mamakin Abunda ya ji yasa shi kasa gazgatawa, "Am.... amma Kubrah me yasa kika ce haka, na kasa gane inda kaina yake bare har in fahimci me kike nufi!" ya yi maganar cikin kiɗima, ga wata zuffa da ta fara keto masa kamar wanda yayiwa Sarki ƙarya.......

Murmushin da bai wuce kan laɓɓa ba tayi kafin ta ce "Dama Abee ya gaya min cewa a rayuwarmu ta Ƴan Adam, laifi ne Mace ta furtawa namiji tana son shi, ba Allah ne ya rubuta hakan a cikin Ƙur'aninsa ba,,, mu dai Mutane mu ne muka ɗauki hakan a matsayin laifi, hakan yana jawowa Mace ƙasƙanci da wulaƙanci har da tozarci a wajen Namiji; Amma Umar me yasa baku ɗauki Mace a matsayim me Ƴanci ba?, me yasa sai namiji ne kawai zai cewa Mace yana sonta ita kuma saboda tana da Imani da Tausayi sai ta karɓa har ta zamowa Namiji Gata a rayuwarsa!,,, ko kuna tunanin ita Mace Allah bai halicceta da Zuciya ba? kuma be yi mata Shauki a cikin halittarta ba?; Ba ina nufin ka yi min laifi ba, Tambaya nayi maka ka dawo min da Tambaya saɓanin Amsa, hakan ne ya karya min Zuciya, kai ma Ɗan Adam ne, mai daraja da Ƴanci, sannan kana da shaukin da zai iya bambanta maka ra'ayi Musamman akan rayuwa ta har Abada, kayi Tunani sosai, duk lokacin da ka shirya Amsoshin da zaka bani Sai ka neme ni ka gaya min!"
tana kaiwa nan ta miƙe Da nufin barin wajen............

*🪻SAWUN KEKE🪻*
season *2*

By INDO

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)

WANNAN LITTAFIN NA KUÆŠI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci É—aya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun)

SHARE FISABILILLAH
Ep..........12
Chapter 10 · 0% Book details