Sashe 15
Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da ya dira a cikin Dajin tare da Ƴan Daban Aljanunsa, hatta bishiyu sai da suka girgiza sakamakon Ɗaurin da aka yiwa Dajin an karya shi lokaci guda,, hakan ya rugunɗima ya bada turnuƙun hayaƙi da guguwa mai ƙarfi.... Tun daga kan tsuntsaye har zuwa wasu ƙananun dabbobin sai da suka firgita suka fara gudun neman tsira....
Yarima Jiehong ya ƙara yin zaman dirshen don rufe ƙofar da ya buɗe, domin kuwa ya lura akwai masu son sace Kubrah ba shi kaɗai bane.
Sai da ya gama sannan suka nemawa kansu Masauki suka haÉ—a Tanti suka yada zango baje-baje hankali kwance.
Ba daɗewa Prince Jiehong ya fito yana ƙarewa Halittun dake cikin Yankin da suke kallo, ya saba ganin Dazuka iri-iri amma sai ya ji wannan ya fita daban a cikinsu.
Tafiya ya fara yi yana kalle-kalle tare da shaƙar iska gami da ƙamshin tsirrai da yake kaɗawa, tuni ya fara lulawa Duniyar tunani kuma bai fasa tafiya ba don bai ma san inda yake jefa ƙafarsa ba bare lissafin komawa Masaukinsa.
Yayi nisa sosai a tafiyar sannan ya farga, ya dakata yana duba ko'ina don ganin ta inda zai koma.
Zuciyarsa ce tayi wani kyakkyawan tsalle saboda Kibiyar da ta tinkaro shi, cikin sauri yayi gefe ta wuce ta gefensa ya juya yana binta da kallo, jiyayi an É—ora tsinin Takobi a gadon bayansa kamar za a huda shi, yayi fakare yana saurarar motsin wanda yake shirin yi masa aika-aika.
Sai da ya shammace ta ya juyo tare da sa ƙafa ya doki ƙwaurinta, ta saki ƴar ƙara tare da yarda takobin tana ƙoƙarin hana kanta faɗuwa, ido ya zazzaro tare da riƙo hannunta yana ƙarewa bayanta kallo, bai yi tsammanin zai ga Mace ba kuma sai gashi ya ganta, juyowa tayi ta tsira masa ido suka fara yiwa juna kallon-kallo, ta rufe fuskarta sai iya idanunta ne a waje, hakan yasa ya fi mayar da hankali kansu, wani irin bugu zuciyarsa ta fara yi mai tashi a hankali a hankali, ga wani baƙon yanayi da yake ratsa shi tun daga cikin idanunsa har zuwa duk ilahirin jijiyoyin jikinsa.......
Gyara tsayuwarta tayi sannan ta fizge hannunta ta yi baya, sanin idan tayi hausa ma ba zai ji ba ya sa ta yi magana cikin Harshen turanci...... "Who are you?!" Kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce "I'm Jiehong from China, please show me your face!"
Cikin zafin nama ta durƙusa ta suri Takobinta tare da kai masa sara, da sauri ya kauce gami da yarfa hannunsa gefe, nan take wata haɗaɗɗiyar Takobi ta bayyana a hannunsa nan fa suka kacame da Kaiwa juna Farmaki......
Mamakin zafin kanta da kuma ƙwarewarta a fannin sarrafa Takobi ya hana shi tasirin komai a kanta, zuwa yanzu ba shi da burin da ya wuce ganin fuskarta don haka yayi amfani da Tsafi wajen ƙwace Takobinta ya jefar gefe sannan ya fincikota ta faɗo ƙirjinsa.
Mutsil-mutsil ta shiga yi tana ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa.
a hankali ya kwance Maɗauron fuskartata ya wurgar gefe kafin ya maida duk ilahirin hankalinsa kanta, ƙuri yayi mata da ido kamar bai taɓa ganin halittar ɗan Adam ba, shi kansa bai yi tunanin zai tsaya kallonta har haka ba amma sai yaji gabaki ɗaya ma ba ya son ɗauke ido daga kanta.
Ita ma kallonsa take yi ba tare da tasan me take tunani ba, sai da Mintuna suka shuɗe sannan ta farga, ta fara ƙoƙarin hankaɗe shi. Cikin wata raguwar murya ya ce "Tell me Your name, Boss Lady!" cikin sarƙewar Murya ta ce "Okay leave me!" sakinta yayi ta ɗan ja baya sannan ta ce "My name is Kubrah!" daga haka ta falla da gudu iya ƙarfinta, Sai da ya kusa faɗuwa ƙasa don yadda zuciyarsa ta buga da mugun ƙarfi, cikin muryar raɗa ya maimaita "Kubrahh!!!" lokaci guda ya tsinci kansa cikin wani irin yamutsi tun daga ƙwaƙwalwarsa har cikin ƙashi.
Sai da yayi da gaske kafin ya nemo nutsuwarsa ya fara neman inda Masaukinsa yake.
Hankalinta bai kwanta ba sai da ta koma cikin Gida, kai tsaye Bedroom ta wuce tana maida numfashi, bata san dalili ba kawai ta tsinci kanta da gaya masa sunan Yayarta wato Kubrah.
Tambayoyi ne da dama gareta a kansa sai dai bata da amsar ba ta da me amsa mata.
______________________________
Masu Kula da Dajin kuwa tuni suka sanarwa Affah wani ya shigo sai dai sun kasa gane waye da kuma inda yake.
Hakan yayi bala'in Girgiza shi, sai dai da ya tuno bayanan Mother sai ya yi banza da lamarin kawai.
Bayan wasu kwanaki........
Yarima Jiehong.....
ya duƙufa sosai wajen neman abunda ya kawo shi, sai dai babu sa'a, duk yawan Tsafinsa da kuma fitinannun Aljanun da suke tare dashi ko Inuwar Kubrah sun kasa gani bare inda take kwana.
a ɓangaren Kubrah kuwa hankalinta kullum yana kan Umar, sosai take shiga damuwa akan irin wahalar da ake ba shi, ta ƙarfin tsiya wai sai an koya masa Farautar Dabbobin Dawa duk da cewar ba aikinsa bane, gashi haɗa shi ake yi da gagga-gaggan Mafarauta kuma a ce sai yayi abunda suka yi, in bai yi ba ya sha rashin Mutunci.
A ɓangaren Umar kuwa tun baya sakin jiki har ya fara don ya lura hakan ya zame masa dole, wataran har ciwo yake ji, amma sai a haɗa shi da magunguna washegari a kuma yin zabarinsa a fita.
Zahra
Tun ranar da ta haÉ—u da Yarima Jiehong kullum ba ranar banza da bata tunaninsa, wani lokacin har gizo yake mata musamman in tana bacci.
Saim kawai ta faÉ—awa abunda ya faru tare da yi masa gargaÉ—i kar ya gayawa kowa, shi ma ja mata kunne yayi akan Dagewa wajen Addu'a musamman tunda in tana bacci ma ganinsa take yi......
*🪻SAWUN KEKE🪻*
season *2*
By INDO
(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)
WANNAN LITTAFIN NA KUÆŠI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci É—aya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun)
don ƙarin bayani
09079885632
SHARE FISABILILLAH
*Ep..........15*
Last Free Page
Yau
Saƙon Gaggawa King Yizheng ya aikowa Prince Jiehong ta hanyar tsafi, akan ganin Gilmin Kubrah da yayi, sannan kuma za ta shigo cikin Dajin, in anjima don haka ya kasance a shirye , shi kuma zai turo da tsafinsa wanda zai hana ta yin tasirin komai har su yi nasarar Saceta........
Abee Cikin shirinsa na fita Farauta ya fito yana takawa ɗaya bayan ɗaya, Yau fuskarsa a sake take babu haɗe rai , hakan ne ya bawa Mariam ƙwarin gwiwar tinkararsa, cikin ɗari-ɗari ta ce "Ina son zuwa inda za ka je" ya ɗan kalleta ya kauda kai sannan ya ce "Ba za ki iya ba!" yana rufe baki ta ce "Zan iya mana, don Allah ka temaka, in na cewa su Zahra ina son zuwa ba sa zuwa dani" murmushin mugunta yayi kafin ya ce "Shi kenan, amma kiyi sauri don tafiya zanyi, sannan kuma ki gaggauta haɗa shirginki ki bar gidan nan na gaji da ganinki!" "To, daman na kusa tafiya, mu je ni a shirye nake ga Hijab ɗina a hannuna" bai ce komai ba yayi gaba, ta rufa masa baya tana murna...
ta daÉ—e tana son shiga Daji ta ji abunda ake ji, amma basa tafiya da ita yau dai kam tayi sa'a.
Mammi ce ta tare su tana cewa "Ina za ka tafi da Æ´ar Mutane??"
"Ita ta ce tana son zuwa" ya faÉ—a yana yin gaba, da sauri Mariam ta ce "Don Allah Mammi ina son zuwa, ki barni please" ba don ranta ya so ba ta ce "'Allah ya tsare" ta É—an É—aga murya ta ce "Kai Abee ka kula da ita sosai" da To ya amsa ba tare da ya juyo ba.
Mariam ta runtuma da gudu don kar ya ɓace mata.
Tun basu yi nisa ba ta fara gajiya, tafiyar mugunta yake mata ya fita sauri amma ba ruwansa da tsayawa saurarenta gashi akwai tudu da kwari a hanyar wani wajen kuma yashi, dole take haɗawa da gudu don a ganinta in ta bari ya ɓace mata sai dai uwarta ta haifi wata.
Sun yi nisa don har sun fara cimma ƙananun Dabbobin Dawa , sai lokacin ya rage saurin tafiyarsa, hakan ya bata damar ƙarewa Wajen kallo, farin ciki ne ya lulluɓe ta ta fara dariya har da tsallen murna, yau gata ta zo inda sai a Film ko a labarai kawai take jinsa.
Murnar ce ta koma ciki saboda ganin wata baƙar guguwa me cike da almara ta yo kansu da mugun ƙarfi, nan take hankalita yayi fitar burgu ya tashi ta tsaya ƙiƙam tana sauraren abunda zai faru.
Tana iya hangen wasu abubuwa tamkar inuwa a cikin guguwar sai motsi suke suna cakusawa.
hankali a tashe ya fisgo hannunta yana ƙwalla mata kira, ƙasa suka zube su duka, Guguwar kuma ta shafe su ta wuce.
Yau É—aya dai ta tabbatar Abee yana É—aukarta a matsayin Mutum don a zatonta a wajensa bata da maraba da Dabba.
Jin yana wani irin ƙaƙari yasa ta zaro ido gami da yin kansa tana tambayar lafiyarsa, ji tayi ya riƙo hannunta da ƙarfi ya janyota cikin jikinsa.
Ta Tattaro dukkan ƙarfinta ta fizge tana ƙoƙarin tashi ya riƙe ƙafarta, ihu ta kurma ko akwai wanda zai iya kawo mata ɗauki sai dai kashh!!.
Ya tashi ya zauna yana zuba mata idanunsa da suka koma wani kala daban kamar ba na Mutum ba, sai da ta kusa sumewa saboda tsoro da tashin hankali, ƙara yunƙurawa tayi zata gudu amma ta kasa don ba ruƙon wasa yayi mata ba, kuka ta fasa tana roƙonsa ya ƙyaleta amma ko a jikinsa sai ma rungumarta da yayi da wani irin ƙarfi, bakin kukan nata ya cafke da nasa bakin ya fara sumbatarta cikin fitar hayyaci.... numfashin kirki ma sai da yaso ya gagareta sai da tayi sa'a ya sake ta da kansa ya fara kiciniyar yayyaga kayan jikinta.
kuruwa gami da magiya ta cigaba da rero masa, ganin hakan ba ya yi masa aiki ya sa ta hankaɗe shi ta tashi.... kafin ta gudu shi ma ya tashi ya ƙara cakumota...