← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 16

Sashe 14

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Prince Zhengyu zaune yake kan hamshaƙiyar Kujerarsa ya dafe Sandarsa ta ƙasaita da duk hannayensa biyu. Kasancewar ya lula Duniyar Tunani bai san lokacin da Prince Jiefan ta shigo ba har sai da ta kira Sunansa, cikin nutsuwa ya ɗago idanunsa da suka sauya launi ya zuba mata cikin salon son jin ta bakinta.
"Tunanin me kake yi me zurfi haka?" kawar da kai yayi gefe kafin ya fara magana "Ban san ta yaya akai Ɗan Uwana ya fi ni da komai ba!, gashi ya gaje Kujerar Mulki gashi ya fi ni sanin Sirrikan Tsafi a yanzu, da fa na fi shi iyawa, dole hankalina ya tashi tunda nasan Yaƙata zai yi!" taku biyu tayi ƙwarara cikin ƙasaita fuskarta ɗauke da wani sirrintaccen shu'umin Murmushi, cikin nuna rashin damuwa ta ce "Ba na damuwa akan duk wani motsi na shi, saboda na san ka fi ƙarfinsa!" zumbur ya miƙe kamar an tsunkule shi, ya ɗan ɗaga murya yana cewa "Kin san kuwa illar da Yizheng yake da ita?, da kike magana amma yanzu ya tsere min, gashi yana da ɗansa mai temaka masa, ni kuwa tawa ƴar bata da amfanin komai gareni!, duk abunda nake so bata so, ko ke kina goyon bayana amma ita babu ruwanta sai ma So da ta ɗorawa Jiehong shi kuma yake wahalar da ita, na tabbata da zarar burinsa ya cika kasheta zai yi!"

 
NOTE....
 

(Kar dai a Manta da Yarensu suke magana ba da Yarenmu ba,👌🏼🤓 kasancewar Ni INDO da nake Rubutun ina baku labari da ku masu Karatu dukkanmu Hausawa ne shi Yasa nake yi da Hausa👏🏻🤭 ato kar a dinga tunanin Sinawa ma Hausawa ne lol.......😜😜)

Maganar tashi ta taɓa Zuciyar Princess Jiefan ta yadda da abunda ya faɗa ɗari bisa , lokacin guda fuskarta ta sauya launi daga murmushi zuwa ɓacin rai, "Ya kamata ka yi ƙwaƙƙwaran motsi ka gane me yake shiryawa, don kuwa labari ya sameni cewar akwai shirye-shiryen da yake yi!" "Ni ma an sanar min akwai wani sabon Sirri me girma da ya samu, wanda in ya kammala haɗa shi to Duk Duniya ma zai iya zama me haɗari a cikinta don ba zai bari a zauna lafiya ba, zai ga bayan duk wanda yake son ya ɓatar ba iya ni kaɗai ba!" Prince Zhengyu yayi maganar cike da damuwa. Jim!! ta ɗan yi kafin ta numfasa ta ce "Mu yi ƙoƙari mu gano Sirrin idan zai yuwu sai mu riga shi mallaka!"
kai kawai ya jinjina ba tare da yayi magana ba...........

GABA

"Haka kake gani?" gyaɗa kai yayi ya ce "Ƙwarai kuwa, Kuma yana matuƙar burge ni sosai fa, har ina jin dama Ni ne na Kasance ƊANSA, a gaskiya kin yi sa'ar Iyaye, suna fahimtarki har suna Gatanta ki, amma ni na rasa hakan daga Nawa Iyayen"
Ɗan jim! tayi kafin ta ce "Ban gane me kake son cewa akan su Mommy ba" murmushin takaici yayi kafin ya ce "Shi Daddyna wai shi Ɗan Kasuwa ne, kullum ba shi da lokacin Iyalinsa sai na kasuwanci, sai kuma Mummunar ta'adarsu shi da Mummy wai ba za su haɗa hulɗa da TALAKAWA ba, ni kuma tun ina Yaro ba ni da Aboki a Ƴaƴan Masu kuɗi sai dai Talakawa, rayuwa a cikinsu shi ya fi burge ni, hakan ne ya sa Iyayena suka fara tsangwama ta, tunaninsu hakan zai sa in dawo bin ra'ayinsu in dena kula Talakawa, sai dai har zuwa yanzu ba su yi Nasarar hakan ba don gani nake na fi su gaskiya, Su basa Daraja Ɗan Adam duk Darajarsa indai ba me kuɗi bane; a ɓangaren Ƴaƴansu kuma babu kwaɓa babu Harara, sai su sakarwa Yaro kuɗi kawai yayi ragamar komai nasa da kansa, sannan Basa laifi bare ayi musu faɗa, ina magana ne akan Yasmeen da Yaseer, yanzu gashi nan Yaseer ba shi da aiki sai shan Giya sa Bin Mata, ba ya kwana uku a jere a gida sai ya tafi Hotel ya kwana, Ita ma Yasmin Ƙawaye kala-kala fitinannu za ki ganta dasu, ita ma Mommyn aikinta kenan bin Ƙawayenta wanda na tabbata su suke ƙara ɗora ta akan duk Tsiyar da takeyi; Kin ga asalin Iyayena dukkansu Ƴan Kaduna ne, daga baya suka zauna a Abuja lokacin tun ina Yaro, da ta ƙara cimaɗo su kuma suka dawo Kano shine fa yanzu muke Kano, batun danginsu kuma babu ruwansu dasu, ba wai Talakawa bane kuma, kawai su Sharafin gabansu suke yi, son kansu ya fi son komai, Ba sa neman Danginsu su ma Danginsu ba sa nemansu kawai idanunsu ya rufe akan neman Duniya; To kin ji abunda ya haɗa ni da Iyayena da Ƴan Uwana sam bama Jituwa da juna, saboda na dage sai na gyara musu rayuwarsu!"
gwauron Numfashi ta sauke kafin ta ce "A ganina hakan ba abun damuwa bane, Ka cigaba da yi musu Addu'a in sha Allahu za su dena" "Haka dai Ammar yake faɗa min, Allah yasa hakan zata faru" ta amsa da Amin sannan ta cigaba da cewa "Ina Matuƙar sonka Umar!, Ina tsoron wataran ka gaji da wahalar da Mahaifina yake baka, ka tafi ka barni cikin Masifar So" yayi murmushi me sauti kafin ya ce "Kubrah kenan!, Da izinin Allah ba zan tafi in barki ba, har sai in ke ce kika ce in tafi, ban ƙi ba ko Affah in ya ce in tafi dole zan tafi don ba zan iya karya Umarninsa ba!"
Cikin murya irin ta wanda yake shirin fashewa da kuka ta ce "Koda wani abun zai faru dani ba za ka guje ni ba Umar?, koda ƙaddara ta sa ina daga cikin wani Nau'in halittar?!" sosai Zuciyarsa ta karye musamman da jin Furucinta na ƙarshe, 'Me hakan ke nufi kenan?' ya jefawa kansa tambayar, sai dai duk yadda ya kai ga ƙoƙarin yiwa maganar tankaɗe da rairaya ya kasa, a gefe guda kuwa wutar sonta ce ke ƙara ruruwa a Zuciyarsa, yayi ƙoƙarin ma ya hango ko akwai wani abu da zai sa ya gujeta amma bai ga komai ba sai tsantsar so da sadaukarwa, ya bawa kansa yaƙini kan cewar babu abunda zai sa ya juya mata baya koda kuwa hakan na nufin rasa ransa.
Ɗago idanunsa wanda alamun tausayi ya cika su yayi ya zuba mata kafin yayi magana cikin tattausar murya, "Kubrah ba ni na zaɓe ki ba Allah ne ya zaɓa min ke!, ni kuwa me zai sa in Butulcewa masa akan Baiwar da yayi min?, ki kwantar da hankalinki ni na shirya Rayuwa da ke indai akan wannan tunanin naki ne hakan ba zai tsorata ni ba, ki cigaba da farin ciki abunki kar komai ya dame ki" ta saki lallausan murmushi, ta ma rasa amsar da zata bashi, ji take ina ma tana da damar da zata rungume shi tayi kuka ko zata ji saukin Yaƙin fa ake yi acikin Zuciyarta.

Ahmadi ne ya ƙaraso wajen cike da Ladabi ya ce "Gimbiya Uwar Masu gida ina gaisuwa gami da neman Sulhu!, don na tabbata aiken nawa ba mai daɗi bane Ranki-yadaɗe!" duk suka zuba masa ido suna jiran abunda zai faɗa.... "Tuba nake Gimbiya a Gidanmu!, wato Mai martaba ne ya ce in zo in sanar da ke ba ya kawo Umar Gidan nan bane don ki je ki dinga tarewa a wajensa, don haka ki tashi ki je yana nemanki" Sallama ta yiwa Umar sannan ta tashi jikinta a bala'in sanyaye.
Umar kuwa kuka ne kawai bai fasa ba, kawai sai ya bita ido.

a Haraba ta samu Affah fuskar nan tamkar hadarin da ya gangamo yake kaikoma yana rugunÉ—imi a sararin samaniya......
"Kar na ƙara gani kin je wajensa, ba don hakan na kawo shi ba, bare har ki kai masa Abinci!" ya faɗa yana tsare ta da idanu, gyaɗa kai tayi kanta a ƙasa kamar munafuka.
Tsaki ya doka sannan ya cigaba da Tafiya ya nufi Dokinsa, da alamu fita ze yi.
Da sauri ta shige cikin gida tana raɓe-raɓe don kar ta ƙara katari da faɗan Mammi......

China....

Lisha har ta rame saboda damuwar da ta addabi rayuwarta.... tayi bala'in takaici da aka ce mata Prince Jiehong ya riga ya tafi.
a gefe guda kuwa ganin ta rikice akan tafiyarsa yasa Babanta ZhengYu ya ɗora ransa akan sai ta gaya masa dalilinta na nemansa, ƙarshe ma ya ce ta san inda zai je sai ta gaya masa.
Ta san yin hakan kuma wani sabon bala'in ne shiyasa ta ƙi faɗe ta jurewa Masifarsa , don ba daga nan ba indai wajen Masifar faɗa ne Allah ya hore masa.
A wani ɓangaren kuwa matsanta tsaro da tayi don kar a gane tana da ciki yakan jawo mata mugun damuwa da ƙunci ga tunane-tunane .
Haka nan ta ci gaba da ƙurƙura rayuwa tana famar katangala.

Nigeria
Jiki a sanyaye Ammar ya zame ya kwanta kan Katifa yana kallon sama, fuskar Abokinsa ko ma a ce ɗan uwansa, ita ta fara dawo masa sabuwa fill!,,, idan ya kasance abunda Umar ya faɗa cewar ba lallai na sake ganinsa ba ni kuwa ina na sa ƙafa a rayuwar nan?, wai wacece ma wannan da take wahalar da rayuwarsa haka? Tambayar da yake yiwa kansa kenan sai dai ba shi da amsar.

______________________________________

Prince Jiehong.... Bayan fafatawa da Abokan takararsa akan hanya ya samu Nasarar isowa amma ya sha wahala dan an so hallaka shi, da temakon Dakarun Aljanun Babansa da kuma tsafinsa ya samu ya sha fa ƙyar.
Karo uku ana kawo masa hari, kuma duk masu neman abunda yake nema ne.
Chapter 14 · 0% Book details