← Book details Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zazzafar iska ya furzar gami da yamutsa Ƴar sumar kansa da ta fara fitowa, "Wai me yasa iyayena suke ɗaukata tamkar babu alaƙa koda kaɗan a tsakaninmu?" wani sashi na Zuciyarsa ne ya jefo masa tambayar, daga wani sashin kuma ya samu amsa da cewa "Saboda kana kula Talakawa kana Abota dasu!" murmushin takaici ne ya suɓuce masa, a sarari yace "Tunda kuwa haka ne lallai ina da sauran aiki, yana da muhimmanci gareni in ganar da iyayena Muhimmancin ɗan Adam a rayuwa, gashi tin kafin tafiya tayi nisa na yi Gamo da wata ban san ma wacece ba gashi tunaninta ya tsaya min a raina"

A ɓangaren Ammar ma haka yaje gida
sharaf-sharaf jikinsa duk babu ƙwari, koda Ummi ta tambayi lafiyarsa sai yace ba komai.

_______________________________________

Cike da fargaba Abee yake takawa tare da kutsa kai cikin wani makeken Falo wanda tsayawa zayyano irin kyawu da kayan alatun dake tare dashi aiki ne babba.
a duk takunsa ɗaya Zuciyarsa ƙara gudu takeyi yayinda tsoro yake ƙara ɗarsuwa a cikinta.

Lokacin da ya iso tsakiyar Falon ya lura babu kowa don haka ya sauke kyakkyawar ajiyar zuciya tare da sauya akalar tafiyarsa zuwa Bedroom É—in Kubrah da nufin yaje ya kwantar da ita.

"Abee!" zazzaro idanu yayi tare da fizgar numfashinsa da kyar.....
sai daga baya ya gane Mammi ce me kiran, ɗan gyarawa Kubrah zama yayi akan kafaɗarsa sannan ya juyo tare da ɓoye duk wani tsoronsa, cikin ƙarfin hali yace "Rankiyadaɗe!" fuskarta babu alamum wasa ta ce "Menene haka!?, ina kake shirin zuwa, kuma daga ina kake?, me ya sameta da ba zata iya tafiya da kanta ba?"

ɗan murmushin ƙarfin hali yayi cikin son kawar da zancen ya ce "Mammi tambayoyin sun yi min Yawa " "Ya zama dole ka amsa min su, idan ma baka bani amsa ba za....." bai barta ta ƙarasa ba ya katse ta da cewa "Don girman Allah Mammi kiyi haƙuri!, Yawo ta tafi yi a Daji shine na dawo da ita"

Ɓoyayyar ajiyar zuciya Mammi ta sauke kafin ta ce "Ɓace min da gani, ka je ka ajiyeta ka fito ka nemo min Su Zahra"
da "To " ya amsa tare da juyawa ya ci gaba da tafiya cikin gaggawa.
Yana ajiyeta ya fito domin aiwatar da abunda Mammi ta Umarce shi.

Sai da aka fara kiran Sallah sannan ta samu Ƴancin Farkawa daga nannauyan baccin da ya sure ta, bayan ta ajiye addu,ar bakinta "Abee" shine wanda ta fara kira tare da juyawa gefenta da nufin ta ganshi amma sai taga fayau babu kowa.
idanunta ne suka ƙara girma lokacin da ta tuno Fuskar Umar , Nan take zuciyarta tayi wani ƙwaƙƙaran duka wanda ya motsa duk ilahirin masarrafan jikinta, "Yasalam!" ta faɗa tare da ɗora hannayenta duk biyun a kanta.
ta ɗauki tsawon mintuna akalla biyu kafin ta samu ta dena ganin hotonsa da Zuciyarta take haska mata, jiki a sanyaye ta sa ƙafa ta sauka daga kan tafkeken gadon wanda ya sha shimgiɗar alfarma.

Daidai lokacin aka hankaɗo Labulen ɗakin da ƙarfi, sai da Zuciyarta tayi tsayawar wucin gadi sabida tsoro da ya rikito mata tamkar saukar aradu. Sai da Zahra ta ce "Yaya! Ki tashi kiyi Sallah mana!" Sannan ta sauke gwauron numfashi gami da cewa "Zan yi mana, ki dena shigowa ɗaki da sauri haka"
Zahra ta murmusa kafin ta ce "Dake da Yaa Abee yanayinku ya nuna akwai abunda ke faruwa wanda ya kasance sirri a tsakaninku!"
"Zahra ya isa haka!, Affah ya dawo ne?"
"Yana Masallaci, kuma na tabbata gaf yake sa shigowa" Zahra ta bata amsa tare da juyawa ta nufi hanyar fita.

Sai bayan ta idar da sallar ne ta samu nutsuwa har ta iya yin numfashi me dadi.... Bata gama hutawa ba Saim ya shigo cikin sauri gami da cewa "Yaya! Affah na kira" dim!!! Zuciyarta ta buga, idanunta sukayo waje, cikin wani ƙaramin tashin hankali da ta tsinkayi kanta a ciki ta ce "Da gaske?" Yana shirin fita daga d'akin yace "Ai ba zan yi Miki k'arya da irin wannan ba "
Bai jira cewar ta ba yayi gaba.
''Innalillahi Allah gani gareka" ta fad'a gami da yunk'urawa ta mik'e don gudun ƙarin laifi.

(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU!!)

*Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌🏻👌🏻👌🏻 Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.👏🏻 Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................*

PAID BOOK NE......👏🏻

SHARE FISABILILLAH
https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw

🪻SAWUN KEKE Season 2🪻
EP .......3

by INDO

Yana tsaye k'ik'am tamkar wanda ya had'iyi ta'barya, Abee, Zahra, Mammi, Saim, duk suna tsaye a gefe curko-curko kamar wasu zakaru.
Cike da fargaba tace "Affah Good evening!" Juyowa yayi yana fuskantar ta tare da zuba mata idanunsa masu matukar kaifi, murya can k'asa ya amsa da cewa "How are you Princess!" Sai da ta had'iyi wani k'ullutun yawu da yayi kaka-gida a mak'oshinta sannan tace "Am fine!"

Shiru ne ya ratsa Falon na tsawon lokaci kafin Affah ya kalli Mammi cikin murya me cike da barazana yace "Where'd they go today?" 'dan numfasawa tayi kana tace "Basu gaya min ba, sai bayan sun dawo ne na tambayi Abee kuma ya gaya min Kubrah ta shiga Daji ne" "K'arya ya gaya Miki, Kuma Ina bukatar sanin gaskiyar yanzun nan!!" Ya karasa maganar cikin tsawar da ta sa Zahra da Kubrah suka k'ank'ame juna.

Cikin in-ina Abee ya ce "Af... Affah....bab...ba.. nisa muka yi ba!" Cikin rawar baki Kubrah tace "Abee ya fad'i gaskiya"
"Idan zaku kara magana ku tabbatar gaskiya kuka fad'a min; me kuka je d'aukowa a inda kuka je??, waye ya baku izinin fita??!!" Affah ne yayi maganar tare da binsu da kallon da yake nuna tsantsar fushinsa a zahiri.

Abee ya ce "Ni ne , dama......" Tasss!! Ya d'auke Kubrah da wani lafiyayyen Mari Wanda yasa ganinta d'aukewa na wucin gadi, "Don Allah kayi hakuri!!" Shine abunda bakinta ya furta cikin daga murya.......
Da sauri Abee ya dawo kusa da ita gami da rik'o hannunta idanunsa tuni sun kawo ruwan hawaye, cikin d'aga murya ya sake cewa "Affah Ni ne! Laif........." A wannan karon ma kasa k'arasa maganar yayi saboda saukar Wani zazzafan Mari akan kumatunsa.

Cikin sauri yayi gefe da fuskarsa gami da saka hannunsa É—aya yana shafar kumatun nasa...... cikin tsawa Affah ya ce ''Yi bayani mana!!!!"
Cikin k'arfin hali Abee ya kara d'aga baki zai yi magana Affah ya Kuma dakatar dashi ta hanyar kifa masa wani k'erarren Mari Wanda ya tilasta masa sakin hannun Kubrah ya fara laluben iska.
Kafin Affah ya k'ara d'aukar wani matakin Kubrah ta ce. "Zanyi bayani Affah,!!,    Ni ce na fita shi kuma ya bini ya dawo dani, kuma banida wani dalilin fita wanda ya wuce ina son ganin Mutanen da suke rayuwarsu tamkar Sakakkun tsuntsaye!,  don Allah ka yi hak'uri Affah!"  Numfasawa Affah yayi kafin ya bar musu wajen ba tare da ya ce kanzil  ba.

Mammi ce ta kalle su cike da jin zafin dukan da suka sha tace "Ba kwa jin magana!, kun sani ba a shigowa Kuma ba a fita ba tare da izininsa ba, ta yaya ma kuke tunanin zaku iya fita Cikin Dubban Al,uma kuma ku dawo ba tare da ya sani ba?, ba na so ku k'ara maimaita wannan kuskuren"
Cikin k'arfin hali Abee da bai gama warkewa daga rad'ad'in marukan da ya sha ba ya ce "Amma Mammi duk da na baki hak'uri meyesa kika gaya masa?". Cike da tausayawa ta ce  "Da ka lura da tambayarsa ta farko da ba zaka tuhume Ni ba, ba ka ji Ni ya fara tambaya ba?, da ace nayi k'arya domin kare ku nima sai na fuskanci nawa hukuncin" tana kaiwa nan tabi sawun Affah......
Zahra da Saim ne suka temakawa Abee da Kubrah suka mik'e daga k'asa duk suka nufi Bedroom domin Kuwa sai sun ji ruwan d'umi zasu iya jin dama-dama.

A tsaye ta same shi Ya tsirawa window idanu hannayensa goye a bayansa.
'dan gyaran murya tayi sannan ta fara magana cikin nutsuwa..... "Amma Akhee! da yaya rayuwar yara ƙananu haka,,, zata yuwu a killatacciyar Duniya irin wannan?, kenan dai!, su basu da y'ancin yin rayuwa kokuma shiga cikin Mutanen da suka danganci kowane irin nau'i na Mutane??"

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu har na d'an lokaci....
Ganin ba shi da niyyar amsa mata yasa ta zagayo gabansa suna fuskantar juna, idanunta ta wulla cikin nasa kafin ta sake cewa "Ba kowace amsa bace shiru take gamsarwa!, akwai buk'atar fashin bak'i bayan yin shirun,,,, Kodai ka manta cewa Zahra ma ta fi shekara Uku ne?"

Murmushin da bai wuce gefen laɓɓa ba yayi kafin ya ce "Na haifi Y'ay'a ne domin nayi farinciki tare dasu!, ba don Duniya tayi dasu ba..." 'Dan tsahirtawa yayi kafin ya ci gaba da cewa "Ni dake ba mu ishe su rayuwa bane?, Ko kuwa duk dangin da muke dasu basu isa a rayu dasu ba har sai an shiga wasu dangin daban?"
Jinjina kai Mammi tayi sannan ta ce "Tana da kafiya da jajircewa akan abunda take son cimmawa ,na kamu da ts......." Kallo yayi mata me nuni da baya son zancen dole ta had'iye sauran maganar sannan ta tarkata ta fice".

Washegari....

Duk wunin ranar Abee da Kubrah haka sukayi shi cikin sanyin jiki gami da damuwa wadda Basu san asalin ta ba.
Musamman Kubrah duk ta firgice ita kad'ai take zabura har da kaiwa iska naushi.

Bayan kwana Hud'u.......

Kubrah tana zaune a gefen ƙawataccen swimming pool Wanda ke a Tafkeken Garden din gidan, k'afunta suna cikin ruwan tana lilo dasu a hankali a hankali.
Chapter 2 · 0% Book details