Sashe 1
Sawun Keke Season 2 Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw
12/4/2025
🪻SAWUN KEKE Season 2🪻
EP .......1
By INDO
(SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU)
*Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌ðŸ»ðŸ‘ŒðŸ»ðŸ‘ŒðŸ» Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.ðŸ‘🻠Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................*
Bismillahirrahmanirrahim.
Ihu ta kurma a karo na ba Adadi tare da tattaro dukkan ƙarfinta ta bangaje shi da Ƙarfi har sai da yayi baya taga-taga kamar zai faɗi ............
Bata tsaya jiran komai ba ta falla da gudu tana dafe da ƙirjinta da ya bayyana sakamakon Yaga mata riga da yayi.....
a tunaninta gudunta zai iya tseratar da ita, sai da ta ji ƙafafunta sun harɗe ta faɗi ƙasa tim!! sannan ta gane bahagon tunani take yi. ihu ta ƙara kurmawa tare da yunƙurawa zata miƙe, sai lokacin ta lura wani kalar ganye me yaɗo ne ya ɗaɗɗaure mata ƙafa har ya jaza mata faɗuwa. cikin zafin nama da bata zata tana dashi ba ta fara ƙoƙarin cire ganyen sai taga ya ƙara kame hannunta ya ɗaure, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" ta furta cikin ɗaga murya, tashin hankali ba a sa masa rana,
Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin irin wannan zai faru da ita a rayuwa ba, bata taɓa zaton laifin da tayi zai sa ta girbi irin wannan ɗanyen hukuncin ba.........
Muguwar cafkar da ya ƙara yi mata ce ta dawo da ita hayyacinta, ta saki wani matsanancin kuka tana cewa "Ban yi maka komai ba don Allah kar kai min haka, wallahi ban faɗa ba ka yi haƙuri!!, ba zan ƙara shiga rayuwarku ba, ka duba girman Allah ka ƙyale ni kar ka lalata min rayuwa!"
Idanu ya zuba mata ƙur!!! yana jin wani irin bahagon yanayi yana ziyartarsa.
Idanunsa da suka koma Blue color tuni sun cika taf da ruwan hawaye, wani sashin na zuciyarsa na tunzura shi wani sashin kuma yana shirin fara tausayinta.
Wata gagarumar guguwa ce ta tunkaro wajen da ƙarfi ta sure shi ta watsar a ƙasa,,, "Abeeee!!!" ta ƙwala masa kira cikin tashin hankali da ruɗani. guguwar tana wucewa ta faɗa kan wata bishiya daga haka ta dena ganin ƙyallinta sai dai jinsa tayi yayi sufa akanta Tamkar wani yunwataccen Zaki.........
Ihu da neman ɗauki gami da jero Addu'o'i shine abunda take iyawa dan kuwa gabaki ɗaya ji tayi kamar an ɗaure mata hannaye da ƙafafunta a cikin ƙasa.......
Tana jinsa yana nashi gurnanin gami da wasu Surutai wanda bata taɓa jin irin Yaren ba a duk tsayin Rayuwarta.
Lokacin da ya gama wulaƙancinsa ya sauka daga kanta ta riga ta zama marabarta da Gawa kawai ita akwai rai a jikinta, sai sa'a ɗaya idanunta da suke a buɗe suna gani dishi-dishi da kuma tunaninta da bai gushe ba..... tana iya ganin lokacin da ya miƙe yana bubbugar kansa da ƙarfin gaske yana kuka , kai tsaye Wajen Tafkin Ruwan da ya ƙawata wannan Yankin na Dajin ya nufa yana tafe yana haɗa hanya, daga haka bata ƙara sanin inda kanta yake ba....................
********************************************
"Yanzu kamar ni in faɗi magana ki ƙi yarda Kyakkyawa?.... kin sa Zuciyata ta tsinke fa"
Murmushi tayi gami da taɓe baki tace "Ai maganar taka ce bata yi kama da gaskiya ba, wancan Abokin naka uban faɗin rai shi ne zai so ni?, da wasa kake yi; kalli fa irin sutturar jikinku ka kalli irin Motar da kuke zuwa da ita Unguwar nan, ni kuwa fa sana,ar Awara nakeyi akan layi ka ga babu haɗi tsakaninmu"
"Wayyo Allah Beauty kina breaking heart na fa!" ya ƙarasa maganar cikin sigar shagwaɓa.
murmushi ta saki wanda ya tawo daga can ƙasan zuciyarta, tana shirin yin magana Ammar ya dakatar da ita da cewa "Ya kamata ki san cewa bamu ɗauka cewar da bambanci tsakanin mu daku ba. In akwai bambanci me zai sa mu dinga zuwa Uguwarku ?, ko ba ki yarda ba har yanzu?"
"Na fara yarda mana" ta faɗa tana murmushi gami da yin ƙasa da kanta.
Ammar ma murmushin yayi gami da kallon inda Umar yake, tare da cewa "Ji mana Abok.....!"
kasa ƙarasa maganar yayi saboda jin wani sauti wanda yafi kama da na takun ingarman doki yana tunkaro inda suke, ganin Umar ya sume yana kallon wajen yasa yayi sauri ya kalli inda Umar din yake kalla don ganin me ya gani....
zumbur ya miƙe tare da dawowa kusa da Umar suka ci gaba da kallonta.
Cikin Wata sumammiyar murya Umar ya ce
"Subhanallah !, Girma da tsarkaka su ƙara tabbata ga Ubangijin da ya halicci Kyau domin ya kasance Adon Duniya da Lahira!"
cikin sanɗa Ammar ya riƙe hannun Umar yana cewa "Kam bala'i yaushe Ƴan China suka fara kafa Masarautu a Nigeria?.
PAID BOOK NEðŸ‘ðŸ»

EP .......2
By INDO
Bismillahirrahmanirrahim.
Waya Umar ya zaro daga cikin Aljihunsa ya fara yiwa Budurwar da take tinkaro su akan Ingarman Dokinta bidiyo, sannan ya bawa Ammar amsa da cewa "Abunda ba zai yuwu ba kake faÉ—a; ni kayi min shiru dalla!"
daidai lokacin Budurwar ta iso inda suke sai dai da tazara a tsakaninsu.
Cak! ta tsaya tana zuba musu zaratan idanunta masu matukar kyau da ƙawa, sai dai kallon da take watsawa Umar yafi kama da na tuhuma ko kuma gargaɗi.
dogon suman da ya tafi saboda kallonta yasa bai fahimci hakan ba.
Ganin yaƙi dena abunda yakeyi yasa Zuciyarta ta fara tafarfasa, cikin sauri ta zaro kibiya dake cikin mazubinta a rataye a bayanta, tana zarowa ta shillata inda Umar yake, Kai tsaye ta sauka akan wayar hannunsa tare da shafar Yatsansa guda ɗaya.
ƴar ƙara ya saki saboda azabar da ta ratsa shi har cikin kansa, ƙasa ya kalla don ganin halin da wayarsa take a ciki, idanunsa ne suka ƙara girma ganin yadda ta tarwatse babu batun za a iya gyara ta ma.
tuni jikinsa ya fara tsuma sabida wani yanayi da ya ziyarce shi , yanayin da ya kasa bambance irinsa.
zai iya cewa duk tsawon rayuwarsa bai taɓa tsintar kansa a cikin makamancin hakan ba.
cikin tsoro da fargabar abunda zai ƙara biyo baya ya ɗago idanunsa da suka kawo ruwa ya ƙara ɗora su akanta.
har lokacin kallo me cike da fushi da ɓacin rai take yi masa, ganin ya ƙara tsura mata ido yasa ta ƙara zaro kibiyar tana shirin ƙara masa.
"Kubraah!!!" kiran gaggawar da aka yi mata ne yasa ta fasa abunda take shirin yi tare da runtse idanunta da ƙarfi.
a sukwano Matashin ya ƙaraso inda take tare da yin tsalle daga kan Dokinsa ya sauka a gefenta ya janyota suka faɗi tim!! a wajen.
"Me yasa taurin kanki yayi yawa ne?!" yayi mata tambayar cikin tsawa. cikin tsawar ta bashi amsa da cewar "Na gaya maka bana so kana yi min tsawa ko?"
"Nayi ɗin mara kunyar banza" Bangaje shi tayi daga jikinta tare da artawa da gudu zata sake hawa Dokinta yayi saurin ƙure mata gudu ya cafkota tare da matse ta a cikin faffaɗan ƙirjinsa.
wutsil-wutsil ta fara yi tana cewa "Ka Sake ni, bana so !!, ni ba zan koma ba"
surutan ta cigaba da yi, tun tana motsawa da karsashinta har ta dena motsi jikinta ya saki salaf.
kallon wani Da yake bayansu yayi gami da cewa "Ahmadi ka tawo da Dokin nata." Ahmadi ya amsa cike da girmamawa.
saɓata yayi a kafaɗarsa tare da yin sufa ya haye kan dokinsa sannan ya kalli inda Umar yake ya ce "Ka kula da kanka!"
Daga haka ya sukwani dokin ya wuce.
Da Ido Umar,, har ma da duk ilahirin Mutanen wajen suka raka su, sai da suka ɓace sannan Umar ya numfasa ya ce "Ammar mu bar unguwar nan" sai a lokacin Ammar ya iya yin motsi ya shiga Mota.
Umar ne a mazaunin Driver amma ya kasa ko motsi da sunan jan motar.
Mutanen wajen kuwa tuni sun karaÉ—e da muhawara tare da maida yadda akai, kowa na tofa albarkacin bakinsa.
"Umar idan ba zaka iya ba ni ka bani in ja" ba musu ya fice daga motar yana shirin zagayawa, ganin haka yasa Ammar ya koma sashin driver, Umar yana shiga ya bawa Motar wuta.
shiru ne ke famar É—awainiya dasu har tsayin wani lakaci, sai da suka kusan shiga Unguwar su Umar sannan yace "Yau rana ta farko da idona yayi tozali da abunda yasa na tsinci kaina cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa"
Ammar yace "Naga alama ai, ni kuma zan iya cewa abunda ban taɓa gani ba yau shi na gani, wallahi suman tsaye nayi, ko wacece wannan Kuma??? kayan jikinta suna da bambanci da kayan da Matan Hausawa suke sakawa a wannnan zamanin, gashi yanayin shigarta yafi kama da na sarauta; Abokina ka manta da wannan yarinyar wataƙila Aljanu ne suka fara shigowa jinsin Bil,adam"
Umar ya murmusa kafin yace "Mantawa da ita ba abu ne me sauƙi gareni ba, wallahi ko Aljanar ce ma na kamu da tsananin kwaɗayin ƙara ganinta"
"A'uzubillah! Umar anya kuwa kana Azkhar yanzu?, ina ga ka dena yi ne shiyasa Aljanar take nema tayi nasara akanka"
shiru Umar yayi don ba zai iya cewa komai akan hakan ba.
Suna yin parking a harabar gidan Umar ya ɓalle murfin Motar ya fice, Ammar ne ya katse masa hanzari da cewa "Gidanmu zan wuce fa!" "Okay see you letter" Umar ya faɗa a taƙaice, wasu lokutan yakanji ba daɗi sabida nuna ƙyama da Ammar yakewa gidansu, sanin Ammar ɗin ya fi shi hujja yasa baya ɗago zancen.
a Falon farko ya tarar da Mommy ta ci Ado ta hakimce kan sofa tana famar danne-dannen waya.
"Good evening Mommy"
ya faÉ—a tare da yin shirin shigewa ciki.
wani mugun kallo ta watsa masa kafin ta ja tsaki tace "Shashasha wanda bai san Mutuncin kansa ba!"
shiru yayi mata, kawai ya dangana da Bedroom É—insa, masauki yayiwa kansa a bakin gado gami da dafe kansa da yake wani irin hargitsi gami da juyawa.