Sashe 8
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ciki,ko ba haka kika ce ba? Na ce "Ni fana fadi haka ne saboda kawai saboda ina son ka barni.Ya ce"ke dai kika sani,wanda bai ji maganar iyayen shi ba ai dole ne yayi nadama in ko ba haba ba ni ba da aure na ba xa'a je kotu,sai ki tattara dansu ki basu.Na xube gwiwa biyu a gaban shi tare da rike kafafunshi na ce"Don Allah ka taimake ni,in na bashi yarona ya cuce ni,ya toxarta ni a baya. Abubakar xan yarda in ka rabu dani saboda ya xama ajalina akan in ba da yarona. Ya fita fuu a fusace ,kamar minti 15 ya dawo ya dauki shadad ya fita. Na bi shi da gudu har gurin motar Yaya Umar, nace "Ina xaku dashi?Yaya Umar bai tanka ni ba,sai Abubakar da yace ckn fushi.koma ciki ki jira,duk ranar da kika koyi magana sai ki kira wayata,yaron kuma xan kai shi gurin uban nashi,in yaso kije ki dauko shi.Umar yaja mota suka tafi.Kai tsaye kano suka nufa,gidan Raham suka kai shi,sannan Umar ya dawo ,ni ko ina nan sai kuka nike mutanen suna bani hkr,wasu na cewa,in hkr mana,muna huta lkc da abin ya faru baabah taje gurin Babah a asibiti. Da ta dawo kuma sai ta same ni ckn kuka da tashin hnkl,nace"Umar da Abubakar mijina sun dauki Shadad sun kai ma Munnir. Baabah tace kiyi hkr,ki kuma gode ma Allah,dmn wannan wata mafita ce ya baki. kin san hatsarin ba yanxun bane,sai nan gaba yaro yayi girma sai ya tsare ki ina babanshi,me xa ki ce mashi? Don haka kiyi hkr,wannan ma wanke ki ne Allah yayi.Na nisa."ni kam baabah ba xan fa yarda ba,ni kadai nasan halin da na shiga tun daga lkcn da Munnir yayi min fyade har xuwa yanxun,in na bashi yarona yaci bulus. Ta ce "to me xa kiyi?kina ganin kin fisu tunani ne?kada ki manta mijinki ne fa da wanki."na hada kai da gwiwa ina kuka tace."bana son ki sake yin wani abu da za a ce baki kyauta ba,ko yan'uwanki suyi fushi dake..."Yanxun ya ya xanyi"Na katse ta, ta ce "ki nutsu ki bisu,duk yanda suke so.Na ce, shi kenan" Na kira Innarmu na fada mata komai game da abin dake faruwa,har xuwa abin da Baabah ta ce.Innarmu ta ce."Ki kwantar da hnklinki shawarar da Baabarki ta bada ita ce ya kamata ki bi,sannan ki tuna cewa mahiafinki yana kwance a gadon asibiti kada ki kara masa wata damuwar."Na ce "to shi kenan,na hakura.Da dare kuma guraren 9pm,na kira Rahma ashe lkcn suna tare dasu Abubakar shadad kuwa yayi bacci. Tace, gata ta kira, yace kada ki nuna mata cewa mun xo.Bayan mun gaisa ta ce"Ya jikin baba?na ce da suki sosai.Ta ce "ya ya naji muryarki wat iri? "na ce Um! sai kuka tace lfy?nace Munnir yana son kashe ni da raina.Kinsan yanxun ya kunna min wuta wai in ba shi dan shi? su kuma Umar da Abubakr dina suka dauke shi suk kai shi.Ta ce " To yanxun yaya xa kiyi?na ce "Rahma ba ni da abin yi daya wuce addu'a in xura musu ido.Tace "hakn in kika yi shine abin da yafi dacewa."na ce "Um,wai Abubakar ha da cewa ban iya magana ba.Wai in xauna a gida in na koyi magana in kira shi a waya,wai da gaske ne Rahma don Allah ban iya magana ba?Ta ce "to kila shi ne kika sakr ma magana son ranki "na ce "Rahma xan iya rantse miki cewa ban taba sa'in sa d ashi ba tunda na aure shi. Ta ce. To ki lallaba shi sai ya fada miki maganr da kika fada masa mara dadi.Na sauke ajiyar xuciya."shi kenan na gode.Na koma na kwanta.Bayan na yanke ma kaina hukuncin cewa ba xan kira wayarshi ba har sai lkcn daya neme ni.Sam daren ban runtsa ba,washegari jkn Babah yayi sauki,aka sallamo shi ya dawo.Can kusan karfe 4 aka yi sallama,mun xata masu duba baba ne,ashe wai kara iyayen munnir suka kai kotu.Tirkashi!Sai lkcn baba yaji komai, na kira Yaya Umar na ce "To gashi sun yi kararmu to ta me bayan kun basu dansu?ya Umar ya ce kara kuma?na ce kwarai kuwa,ga magatakardar babban kotu yaxo.Ya ce"Ina xuwa ya kira Abubakar lkcn ya koma Yola,bai ko hutu ba don saukar shi kenan,ya ce to yanxun ranar yaushe ne shiga kotun?Umar yace "Monday"Abubakrya ce . to xan xo jibi da lauyana."Umar ne ya fada wa Innarmu komai,itama tace tana xuwa.Inna wanka najiyo muryar Abubakar suna gaisawa da mutan gida.Sannan ya shiga gurin Babanmu , na tashi na dan kintsa jikina,ya ce ya shigo suka gaisa da Baba sannan ya koma gurin Baaba suna tattauna batun rikicin.N ashigo na xauna gaida shi,ba tare da na dube shi ba,ya amsa sannan ya tambayi jkn baba, na ce yaji sauki.Daga nan yace ,to nazo da lauyana xumu kwana nan tunda ance gobe ne shari'ar ko/na ce eh!ya ce ki shirya yanxun muje yayi miki tambayoyi.Ya dubi baba ya ce,Baba ayi mata fada ta fada mishi gaskiya,dmn da ita ce xa'a yanke miki duk wani hukunci.Baba yace."kwarai kuwa in kin fadi gaskiya to kin hutar da kanki,kin hutar da kowa,Allah ya ba da sa'a.Muka fita xuwa mota,lauyan ba xai wuce sa'anshi ba,baki mai yar'kiba kadan,yana amsa suna Barista murtala.In da suka yi masauki nan muka je, amma gurin shakatawar muka zauna.lauya Murtala yace in fada mishi sunana,na fada mishi.Daga nan ya tambaye ni tarihina,Abubakar na xaune na xayyana ma lauyan komai,tun daga haduwata da Munir har xuwa yau.Lauya Murtala yace "kin tabbata haka ne?Na ce ko ckn bacci ka tashe ni xan maimaita maka wannan don ba xan manta da wannan bakin tarihin nawa bah.Abubakar ya ce?Kada dai ki fada man karya,don ke baki iya magana ba.ya ci gaba da cewa."yaya batun xagawa duniya da kika yi?Na ce,"banje ko ina ba,kuma ban da shi da ya min fydae ban taba hulda da kowane namiji ba.Ya ce "in har hak ne fyade yayi mata barista sai in ga kamr shari'ar xata yi sauki ko?Murtala yace "inshaAllau in an gam matsalar yaron sai tayi karan cewa fyden da ya mata,tana son abi mata hakkinta,tunda nasan dole xai amsa laifinsa.Bayan gama gabatar da shari'ar a ranar litinin din da muka gurfana a gaban kotu lauyoyi suka fito,lauyan shi ne yafi bani mamaki, yanda ya kuke kan cewa a ba shi danshi xai biya duk abin da aka kashe.ni dama koda aka tambaye ni dans ne?na ce dan shi ne,ban bata lokaci ba.Lauyana ya bukaci in ba da labarin dangantakata da munir,mijina ne?na vce a'a saurayina ne ,ya ce to saurayinki ya ya aka yi kuka haihu har ma ki ka hana shi danshi?ya dubi Alkalin ya amince nan na xayyano komai har xuwa yau.Jama'a da dama sun xubar da hawaye don tausayin min aka tamabyi munir shima bai bata lokaci ba ya amsa da cewa tabbas fyade ne yayi min.kuma duk abin da na fada haaka ne,sai dai shi bai san cewa na shiga wani hali ba,sannan ko nawa na kashe wa dan xai biya ni.nan dai lauyoyi suka yi ta kafsawa,daga bisani na ce ina son a bi min hakkina na fyaden da yayi min .nan Alkali ya daga kara xuwa sati biyu masu xuwa,kuma ranar ne za'a yanke hukunci,haka muma Alakli ya bukaci a xo da yaron.Muka fito ,Abubakar sai kallona yake yi tamakr yau ya soma ganina,ya ce Umar ya wuce da su Innarmu saboda shi xai tafi tare da lauyan,don in sake mishi karin bayani.Tunda muka xo daidai dakunan su Barista Murtala ya shige nashi,ya rike hannuna xuwa ckn nashi masaukin.tsakiyar dakin ya tsayar dani ya rike hannuwana tare da kallon fuskata ckn matsanancin tausayi ya ce min."Hafsat me ya hana ki sanar dani ainahin abin da ya faru ki ka sa ni ckn kunci nima ni dinga kuntata miki? Na tsura ma fuskarshi ido."Abubakar a lkcn na furta maka haka ne don kawai ka rabu da ni,sam ban san xa ka zama makusancina ba,lkcn bana bukatar wanda xai kusanto ni da gida,ban san lamura xasu xo da sauki haka ba,ya manna ni a kirjinsa, lokaci guda muka sauke ajiyar zuciya, ya ce ki yafe ni, na nisance kine saboda in ina tuna cewa bansan adadin mazan da kika yi hulda dasu ba, ga kuma kishin ki mai wahalar dani......