← Book details Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 22

Sashe 18

Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kada ma ka ce xaka kwana can, don ba xan yafe ba.Duk ina jin su, kuma ba gidanta xai sauka ba, saboda randa xai dawo gidana ya tafi.Na ce to koma can din , ya ce ba xan koma ba, tana xaton ban san me nake yi ba?ya share ta muka ci soyayyarmu, dama mun yi rashin juna.Wata juma'a misalin 3 muna cikin bacci wayarsa ta soma kuka, ni ce na farka na daga.Sweet hrt na gnai a jiki na daga, Muryar Goggo Jami naji tace, "Ina Hamma din?N ace "yana bacci "Ta ce to tashe shi Fadi bata da lfy shi bacci ma yake?a raina nace kada yayi? Namatsa kusa dashi na shafa fuskarshi, ya rike hannuna zuwa kirjinshi, nayi masa rada cikin kunne. Mr Cool ka tashi yau twins zasu fito, Fadi zata haihu." Firgigit! Ya mike ya zura jallabiyya ya dauki key din mota. Na ce yanzun zaka fita?" Ka bari a kira Sallah." Ya ce ba komai kada ki damu, na ce to Allah ya raba su lafiya." Ya ce "Ameen the only." Takwas na safe na kira shi, ya ce har yanzu dai shiru, na ce gani nan. Na isa gurin na samu 'yan gidan su, sai su Rukayya. Shi kuma can na hange shi tare da su Hashim da Usman kaninshi. Na gaida su Goggo Jamin, sannan na nufi gurinshi. Rukayya harda cewa 'yan biyun nan suna ba mamansu wahala, Allah yasa kada zuwan wasu yasa abin ya sake rikicewa. Wata da ban san ko wacece ba, ta ce ai mun rike Allah, kuma sai ta sauka lafiya da izininshi. Ban da lokacinsu bare amsarsu, don nasan dani suke, gurin mijina ma ni na nufa. na dube shi har yanzu ko? Na yi maganar ne cikin nuna tausayawa da tausasa murya. Ya ce, wallahi, na matso na kama hannunshi na dama na matsa kadan. Ka da ka damu samu ruwa a tofa mata addu'a, In shaa Allah zata sauka lafiya. Goran Ruwa ya kawo na karanta mata, YA HAYYU YA KAYYUM, YA ZULJALALU WAL IKRAM, BIRAHMATIKA ASTAGISU, sau bakwai na ce ya bata tasha. Da kanshi ya kaimata tasha, ya fito, ko minti ashirin ba a yi ba Nurse ta fito da murna tana fadawa su Goggo Jami ta sauka. Kawai sai naji mutum ya rungume ni a bainar jama'a yana fadin "Alhamdulillah." Usman ya ce "Aunty na Allah ya amshi Addu'armu, sai dai kuma me? Maimakon biyu sai aka fito mana da yarinya katuwa mai kyau. Sai kace mamanta tayi kaki, aka amsa da murna ana cewa ina dayan? Wannan ce Hassana kenan.Nurse ta ce ai daya ce, ita kenan aka haifa. Yanzun haka mai jegon ana gyara mata jiki. Gaba daya sai naga jikinsu yayai sanyi, har shi kanshi angon karnin. Usman ya ce amma 'yan asibitin nan sun cika shegiyar karya, shine suka ce biyu? Doctor ya fito, su Hashim suka bishi suna tambayarshi, "dama daya ne? Ya eh ai dama daya ce duk scanning dinta bai taba nuna biyu ba, wa ya ce biyu ne? Abubakar ya ce "ita ce" likita yayi tsaki ya ce "haka wasu matan suke yi ban san amfanin hakan ba, alhalin sun san cewa akwai ranar irin wannan da za a kure su. Ya dafa kafadar Abubakar "kada ka damu, ka yiwa 'yarka addu'a Allah yasa mai albarka ce." Duka suka ce "Ameen" Masu habaici da rawar kai kowa dai baki tsuu, shiru kake ji. Kullum nake zuwa gidan mai jego har ana jibi suna. Ranar da ya kawo mata zannuwan fitar suna ta ce basu yi mata ba, ranar ce ya amayar mata da takaicinshi a gaban 'yan koran nata. Ya ce "ki bini a sannu, banza makaryaciya, zan maganinki, kuma in na dawo baki dauki kayan nan ba sun zama ba rabonki ba. Ki sani ko bari kika yi zan so shi, bare dan mutum. To meye ribar karyar da kika yi kika sa muma muka yi? Mutuncin ki ya zube a gurina da sauran mutane. Sannan baki isa ki juya ni ba, kinfi kowa sanina. Zata yi magana ta rike kugu, ya ce yi min shiru, in kin furta wata magana zan bata maki yanzun nan. Ta yi tsit, ya fice. Nan ta shiga kuka suna bata hakuri, Rukayya tana cewa sai ta fadawa Dada da Abba. Yarinya taci suna Nana Fiddausi, in da ni kuma na shiryawa Abubakar kalolin girki kusan bakwai da kayan drinks. Suka yi walima, Ummi da kanwata Ummi sune yan taya aiki. Bayan suna da sati daya muka je Kaduna don maida Ummi tare da dauko Shadad daga gurin babanshi. Har da Umminsu ta mana rakiya don sun kulla kawance da Umminmu,saboda xaman mota sai kafafuna suka kumbura,sannan nayi ta shar amai,duk Abubakr ya rude hankalinsa ya tashi.kafin kace haka na kwana shrkaf.muna isa kaduna asibitin Garkuwa ya wuce dani, da gudu-gudu aka kawo gadon tura mara lafiya aka yi ciki dani,likitan yana duba ni yana mishi tambayoyi,tana da ciki ne?ya ce kai bana xatao, sai dai ko in yanxun. likitan ya maida allurar da yayi niyar yi min ya aje,yasa aka tura ni xuwa dakin scanning, kusan min 30 aka fito dani yaxo ya dauko ruwa aka yi wasu allurai a ciki, sannan aka dora ni ,ana da nan bacci yayi gaba dani,likitan ya kalle shi"matarka tana da ciki kusan wata 5 ko ma fi,sai in ta farka nayi mata wasu tambayoyi tukunna. Abubakr ya tsura mishi ido,kace tana da ciki wata 5? likitan ya ce kila ma ya fi. Abubakar dai yayi shiru,amma ba don ya yarda ba, ya kira Umar ya fada masa kusan minti 30 suka iso dasu Baabah.Sannan ban tashi ba, ya ce don Allah yaya umar ya kai su Ummi gida don suna ta kuka,kujera Abubakr yaja ya xauna ya rike min hannu su Baabah sai waje suka fita don kunyar yanda ya tasa ni gaba kamr xai cinye ni.ya kira su Hashim ya fada mishi su Daada ma ya sanar da su,kusan wa daya na farka.Da sauri ya tashi yasa hannunshi a kuskata, yana cewa "Sannu Hafsat sannu.Na ce yauwa Na yunkura xan tashi ya kama ni na xauna ya xauna gefen gado. Ina ne ke miki ciwo yanxun?nace "Ba ko ina yunwa nike ji, bakina ya cika da miyau,na ce xan xubar "ya miko min wata yar tasa sannan yace bari in kira likitan.Da sauri ya fita ya ce ma su Baabah na farka, suk shigo suna min sannu, na amsa na ce ni babu gurin da ke min ciwo,yunwa kawai nake ji (dama cin abinci a gurina tun dana samu cikin nan kmr gara)suka shigo da likitan aka ce su fita Abubakar kuwa xama yayi kusa dani likitan ya ce "Madam cikinki wata nawa ne?Da sauri na kalli Abubakar sannan na sunkuyar da kai.Ya ce "Fada min mana "Na ce na zaton cewa xai kai shidaa."Abubakrya dago idona ina da yaro dan wata shida a gurinki, ina me ban sani ba?likitan yayi daria,'kila tana son ta baka mamaki ne ko?na ce"Ina son in ci abincin. Da sauri likitan ya ce me xa ki ci?na ce "Tea xan sha.Nan da nan yayi waya a kawo min tea.Abubakr kuwa cikin rigata ya xura hannu yana shafa cikina yana min magana a kunne."d only me yasa kika rufe min?na ce To kana fama da mara lfy sai nima in kwanta mu taru mu daga maka hnkl?Ni ba xan iya ba, bana son in ganka ckn damuwa,shi yasa na daure. ya ce "Allah yi miki albarka, dama nasan kece mai son kwanciyar hankalina. bayanna huta ya sallame mu muka nufi gida sai yau naga gidan da aka sai masu Baba a nan dai Abuja Road din ne amma can kasa gurin sabon guri ne kuma gida mai kyau flat. .. Abubakar kam da ya fita sai ya je ya kama masauki, sai dare ya dawo. Ya ce na zo muje, bansan ko ina bane na cewa su Baba ina zuwa. Sai kurum ya kaini masauki, wai nan zamu kwana, na ce "Haba Mr Cool, ka maida ni gida mana su Baba zasu ga rashin kunyata." Ya ce, "Bazan iya barinki ba, bakiji Likita ya ce na kula dake sosai ba?" Sai waya nayi wa su Baba na ce munje gidan wani abokinsa can zamu kwana. Suka ce to, kwanan mu uku, kullum da safe zai kawo ni amma da dare zai zo ya tafi dani. Wata sabuwar soyayya da tarairaya Abubakar ya soma yi min, da zamu koma gida jirgi muka bi. Muna isa ya fara yadawa ina da ciki, dama Likita yace in mun dawo na soma yin awo. Shine ya kaini asibitin ya yankar min kati, a dakin scanning Likita ya ce "Madam kin san cewa 'yan biyu ne?" Na zaro ido "'yam biyu?" Ya ce "kwarai kuma kin gansu duk maza" Na ce ba a fi sati daya ba da akayi min scanning a Kaduna ba a fada min haka ba." Ya ce to yanzun dai gashi nan" na ce to don Allah ka taimake ni kada ka rubuta a cikin sakamakon" Ya ce "don me?" Na ce "Don haka ta faru ga kishiyata, a karshe sai ta haifi mace guda daya."............
Chapter 18 · 0% Book details