Sashe 14
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
son turarenki ki daina zuwa kawai." Allah yasan na ji haushi, amma sai na share saboda sanin halin Abubakar shi mutum ne sak babu kwane-kwane a tsarin shi, baya rufa-rufa ko kara zance, yanda aka fade ta haka yake daukenta, shi yasa na sha wahala lokacin da na ce mishi ni karuwa ce, har sai da ya zo ya ji komai da kunnanshi na samu sukuni. To yanda Fadima ta ce haka zai fada gaskiya tsagwaronta yake yi ba ruwanshi, don haka na ce, "Shi kenan, na ringa kiranta a waya muna gaisawa." Ya ce, "Hakan zai fi." Daga baya sai ta tsiro cewa ita ba zata iya bacci ba sai in yana gurinta, Ya ce to bari ya same ni. Ina kwance na dawo daga gurin aiki wata makaranta aka turani ta 'yan mata nake koyarwa. Na yi abinci na gama nayi wanka na kwanta, ya zauna na tashi na mishi sannu da zuwa, na dire mishi abinci. Yana ci ya ce, "The only, ina son ki yiwa Fadima taimako daya." Na ce, "Na me?" Ya ce, "Bata samun bacci don Rukayya ta fada min cewa zaune suke kwana. To tana son in dinga kwana gurinta har ta dan murmure."Zancen ya bani mamaki, sannan na fahimci cewa makirci ne, amma sai na ce, "Ba komai." Ya ce, "Dama na san ki baki da matsala." Da dare kuwa ya tafi, haka-haka har sati uku. Sai dai fa in yana da matsala ya yi min sammako ko kuma in ina gurin aiki ya zo ya dauko ni daga baya ya dawo da ni. Ban taba nuna mishi damuwata ba. Lamido ya kira shi ya ce, "Ubana an fada min baka kwana a gidan nan ko?" Ya ce, "Eh, saboda bata samun bacci ne in bana na." Lamido ya yi murmushi sannan ya ce, "An fada min kuma tana zuwa hurin aiki ko?" Abubakar ya ce, "Eh, ai matsalar tata da dare ne." Lamido ya ce, "To, daga yau na hana, kowacce ka dinga kwana gidanta a ranar kwananta, kanta aka soma ciki? An ce ta samu sauki ba shike nan ba?" Abubakar ya ce, "Shi kenan." Har na soma bacci na ji kwankwasa kofa, na zo na ce, "Wane ne?" Ya ce, "Ki bude." Na bude na ganshi na ce, "A'a baka tafi ba?" Ya ce, "Ke ce kika fada ma Lamido cewa Fadima ta ji sauki amma ban daina zuwa ba ko?" Na ce, "A'a bani ba ce." Ya ce, "To wanene?" Na ce, "Ka tambaye shi." Ya ce, "To ni bana son kai kara, don ban soma zuwa ba sai da izininki." Na ce, "To gaskiya ba ni bace." Ya ce, "In ma ke ce din ai yana zuwa kanki, tunda an ce ai haka ciki ke yi muku." Na yi masa shiru don haushi. Abinda bai sani ba nima lokacin ina manne da nawa cikin wata biyu, ina kuma laulayina sai dai bai yarda ni ba, sai dai amai kuma nafi yin shi da rana, kuma ban fasa komai ba. Azumi ya kusanto ya zo ya same ni wai in zo muje gidan Fadi, zai yi wata shawara, na ce to.......... Cikinta ya fito, amma yanda take tike kugu gami da turo cikin ko watan haihuwarta ne sai haka, tana yi da kyar take daga kafa, a dole ga mai ciki shi kuma kallonta yake yana murmushi, ni sai suka ma bani dariya. Ya kamata ta zauna yana yi mata sannu, ita ko sai faman cije-cijen lebe take, na yi 'yar dariya nace, "Maman twins an fito?" Ta ce, "Umm na fito." Muka gaisa ya ce, "Dama saboda zuwan azumi ne ina son in bada sadaka wa kuke ga ya dace in ba?" Fadima ta dube shi, "Kawai honey ka bamu mana, ni ga ma sayayyar da ke gabana na kayan baby." Ya dubeni, "Ke fa?" Na ce, "Ka kai Masallaci ko ka samu mabukata ka basu tunda Alhamdulillah mu muna cikin wadata." Ya yi murmushi, "To dama nima tunanina kenan, don haka zan bai wa masu bukata Zakka, sadaka kuma zan baku ku bada, ko cikin family dinku ko nawa."ta zobaro baki, "Kenan shawarata bata yi ba?" Ya ce, "Eh." Ta yunkura, "To ai da ba'a kirani ba." Ya ce, "Hakkinki na baki da ba sai na zo ba din, don nasan ita zata iya bani shawara ta masu ilmi." Kudi ya zube min dubu dari uku da dari biyar, wai in raba ma masu bukata. A zatonshi zan tafi da shi gidanmu ne in raba ma dangina, sai na tambayeshi zuwa kasuwa ya yarda. Ni da Ummi muka je. Shinkafa kawai na lodo da taliya sai kuma zannuwa, Ummi ta ce, "Aunty me zaki yi da shi?" Na ce, "Sadaka." Ta ce, "Don Allah akwai wasu dangin su Daada dake can wata ruga talakawa ne, jiya ma Abba ya aika musu da gero da sugar na kunun azumin." Na ce, "To." Daada din naje na samu na ce, "Sadaka zan raba ta abinci saboda neman falalar wannan wata, to ina so in cire na dangi na can Ruga shine nake so ki cire musu nasu sai na ba makota sauran." Ta ji dadi sosai, tayi ta shi min albarka, duk da ta san cewa shi ne ya bamu kudin, ta ce min ya shawarceta, ita ce ma tace yayi shawara da mu, ta ce ya ban kai dangina ba? Na ce, "Da ku da dangina Daada ai duk daya ne ba wani bambanci." Ta ce, "Allah ya shi min albarka. Ta cire musu sannan na saka 'yan samarin gida mua yi ta mika wa makotanmu wadanda ke da karamin karfi. Dama kananan buhuna ne. Lamido har kofata ya zo yayi min godiya tare da shi min albarka. Abubakar kuwa da ya dawo ya ga makota na ta mai godiya tare da addu'a sai kuwa kanshi ya daure, da yai zaton geron da Lamido ya raba ne, sai da ya je gurin Lamidon shi ne ya bashi labarin abin da nayi sannan ya ce, "Ka rike matarka hannu 2, don ka samu macen da babu irinta cikin yaranmu, Allah ya azurta ku da Yara masu albarka." Abubakar rungume ni yayi tare da min godiya na ce, "Allah shi ne abin godiya." Ashe zakkar shi can ya kai ma su Babana bayan ya dibar ma Innarmu. Shima bai fada min ba sai da Ya Umar ya kira ni ya fada min wai mijina ya kawo wa Baba zakkar kudi naira miliyan 2, Inna dubu dari biyar, in masa godiya sannan yana son mu yi shawarar abinda za'a siya. Na ce, "Yaya Umar ku nemi dan madaidaicin gida ka sai ma Baba kawai." Ya ce, "Nima haka na ce, kuma shima Baba zai so hakan. Allah ya saka masa da alheri." Na ce, "Amin. Kuka na saka da muka gama wayar, ban san ko kukan me nake yi ba, na farin ciki ne? na son mijina ne? na barin iyayena baya ne? Oho. Inna ma ta kirani ta ce in masa godiya na ce to. Da ya dawo kuka na sa tare da rungume shi, ya rude ya firgice yana tambayata, "Me ya faru D Only? Wa ya taba ki?" Na ce, "Ba kowa, na gode da taimakon da ka yiwa Iyayena, Allah ya saka makada alkhairi, Allah ya kara budi, ya tsare ka daga dukkan sharrin abin ki, ya kuma bani ikon binka sau da kafa." Ya shafa kaina, "Amin Masoyiyata, game da batun Zakka kuwa ba sai kin min godiya ba hakki ne na Allah na cire." Na ce, "To da ka cire din da kaga dama ai wani zaaka ba." Ya ce, "To shike nan." Da dare muna kwance ya ce, "Wai ya za'ayi da sayan kayan Sallanku? Kudin zan baku kuje kasuwa ku siyo?" Na ce, "A'a da kai zamu je saboda ka zaba mana son ranka." Ya ce, "Bari sai na ji ra'ayin Fadima." Ya janyo wayarsa ya kirata, "Sweet heart." Ta amsa da, "Na'am Sweet honey." Ina jin muryarta, don ina jikinsa ya ce, "Gobe zaku shirya ne mu shiga kasuwa tunda bani da aiki?" Ta ce, "To, daga nan sai mu siyo kayan Babys din tunda an ce mace da namiji ne?" Ya ce, "To sai ki shirya zamu shigo wuraren 11am saboda kada ki sha rana ko?" Ta ce, "To Honey sai kun zo." Ya ce, "Yauwa, ki shafa min Babys." Suna yin sallama na kankame shi, "Yan biyu zamu samu?" Ya ce, "Eh, dazun da ta dawo asibiti take fada min wai an ce 'yan biyu ne mace da namiji." Na ce, "Kai na yi farin ciki, ina son twins shi ne baka min albishir ba?" Ya ce, "Na same ki kina kuka yaya zan tuna da maganar 'yan biyu?" Na ce, "Allah ya sauke mana ita lafiya." Ya ce, "Amin, kema Allah ya baki ina son in ga kin haihu, duk wannan dina har yanzun ba ciki, ko dai zamu je asibiti ne?" Na ce, "Haba dai, duka yaushe aka yi abin? Ko fa shekara banyi ba." Ya ce, "Don Allah ki daina zancan nan, yara nake so sosai, yanzun kin ga zan fara da biyu na zo daidai da Kanina Usman, in kin haihu ko da daya ne kin ga na fishi ko? Balle ma kema biyun zan baki." Na ce, "Oh! Kai ne ma kake badawa?" Ya ce, "Allah ne zai bani ni kuma in baki." Na ce, "Dama kun gaji 'yan biyu ne?" Ya ce, "A family ni zan fara, shi yasa kowa ke doki, jiya kinga yanda 'yan uwa ke murna?" Na ce, "Ai abin so ne, Allah ya bamu masu albarka." Har zuciyata na taya shi murnna. Katon super market muka shiga, gefen zannuwa, lesuka da shaddoji zuwa yaduka, ya ce mu zaba, na ce, "A'a ka zabo mana." Sai cewa Fadima ta yi, "Ni zan zabi abina." Na ce, "To ni ka zabo min." Duk wanda ya miko min ko bata kamfanin ba amsa nake in ce yayi kyau. Ya ce, "To dama atamfa ce nake da irin wadda nike so, amma sauran zabi." Da muka gama sai na zabar wa Ummi atamfa da Shadda da leshi Rukayya ma haka. Daada kuwa yawan namu na daukar mata, ya bini da kallo itama haka