← Book details Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 22

Sashe 1

Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 4-01 Posted by ANaM Dorayi on 06:21 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Kalmar ta dake ni tamkar saukar aradu jikina yayi sanyi matuka.Tsam na mike daga gabn madubi na koma gado na zauna cikin matsanancin kunan rai.Sai naji tamkar mazaunan nawa ba zasu iya rike ni ba, don haka sai na kashingida tare da lumshe ido. Duk iya kokarin da nayi don na tsaida hawayen idona abn d yaci tura,sai da suka sulalo ta gefen idona, idon haguna kuma hawayen ya biyo ta karan hancina. Yayi dan murmushi ba shi da burin da ya wuce yaga 6acin ran Hafsat,duk da son da yake mata.In ya tuna yanda ta mike tana fada mishi cewa ita karuwa ce sai ya ji tamkar ya binne kanshi don takaici. Ya dubi ni Ki tashi mana kin wani kwanta. Na sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya na ce. Ban san cewa gasar kyau zamu je ba da ban 6ata lokacina gurin shirin tafiyar ba., Kaje ka bata Award din da ka tanada na mika wuya. Ya dan yi shiru. Kila yana nazarin maganar da na fadane can sai ya fita da cewa in kin gama ina jiranki a mota in har ina da izinin bada umurni. Tamkar kada na tashi,amma bani da damar yin haka,dole na koma gaban mudubi. Jallabiyata na saka baka mai ratsin ja, tana da tsukakken hannu shima ja, na nade kaina da dan mayafin, shima yana da ratsin ja. Takalimi da 'yar post din da na saka duk jajaye ne. Na feshe jikina da turare, da na kalli madubi sai nayi dan murmushi don nayi kyau. Zuciyarta ce dai ba dadi sakamakon maganganun da ya ya6a min. Na isa gefen direba in da yake zaune cikin sanyin murya na ce, bari nayi ma su Gwagwal sallama. Ya dago ya dube ni, muka kalli juna cikin ido. Da sauri na rausayar da kaina gefe tare da harde hannuwana a kirji, ya ce to kije mana kin tsaya min kerere. Na dubi shi, "Ai dama umurninka nake jira. Duk sai da na bi kowa gurinta na ce sai mun dawo,duk sun ji dadin cewa gurin Fadima zani. Abin da na lura shi ne, suna son a girmama 'yar uwarsu.Na dawo na shiga gaba kamar yanda ya bude.Tsararran gida ne mai matukar kyau, ga furanni masu bn sha' awa, ina biye da shi hr kyakkyawon falon. Wani dankareren zanen hotonsu ne yake fuskantarka an jingine shi da bango a kasa. Kallo daya na yi wa hoton na kauda kai, tamkar jinsin Larabawa ko Indiya. Ya dube ni ya ce," zauna, bari in kirata."Ya tafi yana fadin "Sweety.," Tamkar in toshe dodon kunne na don kishi. Na nutse cikin kujerar ledar mai kalar siminti. Na dinga bin ko'ina da kallo. Wasu abubuwan ma bn san su ba, ban ta6a ganinsu ba, daga karshe na maida kaina ga dankareren TV bangon da wasu Indiyawa suke ta rawa. Ba rawarsu ce ta birge ni ba, da har na tsura musu ido,tsabar takaici ne ke cina. Amma na lallashi zuciyata da cewa tayi hakur, na sani wata rana dai labari. Hannuwansu sarke da juna suka fito, kama suke sosai da shi,wani abu yazo ya tokare kirjina tamkar in rufe su da duka. Wata zuciyar ta ce, Tashi ki shaketa. Da sauri na ce, "A'uzubillahi minasshaidaninrrajim" sau 3 sannan na ce, Allah ka yaye min wannan duhun da ke zuciyata, ka bani ikon yin dauriya,kasa nafi karfin zuciyata. Suna isowa na mike tsaye,take naji zuciyata wasai, na saki wata fara'a wadda bn san ma ina da ita ba,tare da mika mata hannu. Na ce, Amincin Allah su tabbata a gare ki da rahamominsa da albarkatunsa. Itama ta miko nata tare da cewa, Amin kema amincin Allah ya tabbata a gare ki. Muka sarke hannu.Sannan muka saki na zauna itama ta zauna, ta ce, kullum ina son ki zo mu gaisa. Na ce"To ai yau gani nazo." Ta mike ta nufi gurin da nafi zaton kicin ne, shi kuma ya dauki remote yana canje-canjen tasha. Ya kuma ajiye ya nufi dakinshi, ta iso da kofin tare da kwalin jus a hannu fara'arta dai ba sosai ba. Ta dora kan stool ta dauko shi ta kawo gabana,sannan ta zauna. Na dauki kofin na jingina da kujerar ina kur6a ina kallon TV.Ta mike ta nufin ciki,dakin da ya shiga nan ta nufa. Dakin shi kenan,suka bar ni nan zaune. Tuni na dire kofin jus din don sai naji ya daina zakin sai daci, don tsabar takaici. Kusan minti 10 sannan ta fito shima haka. Ta shiga dakinta shi kuma ya nufo gurina, na kalli agogon bangon falon wanda hoton sune a jiki. Na ce, Tunda mun gaisa zan tafi gida."Ya dube ni "Nan ma gida ne. "Yar aikinta ta soma jera abnci kan dinning. Ta fito ta iso gurinmu "Honey kuzo muci abnci." Ya dube ni " tashi muci abnci . Na ce Tuni naci abnci. Ta ce, Ai kam ba ki isa ba, dole sai kin ci. Ni da ita muka jeru, shi kuma ya zauna saitinta, ta ce In zuba mana? na ce Ban san cikinku ba, yaja plate ya zuna musu. Ya ce ke kuma zuba naki, Ya kalle ta ya daga mata gira tare da kashe mata ido daya. Ta kai masa dan duka cikin wasa, ya cafe ke hannun ta ya sumbaci tsakiyar hannun. Tayi wata 'yar kara na dauke kaina ga barin kallonsu wayata ta soma ringing a cikin pos dina. Na mike na nufi kujear da na taso don nan ma na bar pos din. Ya dube ni Ina za ki? Na ce Amsa waya zan yi. Na dauka, yaya Umar ne. Nayi kasa da murya muna gaisawa ya ce Dama Inna ce za kuyi sallama, suna gidana yanzun zan je in sha mai in maida su." Na ce To yaya Umar. Ya ba Inna muka gaisa. Na ce Ashe tafiya zaku yi?" ta ce," Eh, mun shirya ma yanzun zamu tafi. Dama ina so ne in sake yi miki nasiha Hafsatu!!kiyi zamanki a dakinki, kiyi ta hkr don Allah na roke ki duk rintsi ko yaji bn amince kiyi ba. Ki rufa ma kanki asiri, kin dai ga gatan da Ubangiji ya miki, ya baki miji dan mutunci, ki rufa min asirin nan da Allah. Na fashe da kuka, na ma manta ko a ina nake, take lkcn baya ya fado min lkcn d Innarmu ke rokona cewa in lura da kaina in tsare mutuncina,amma bn yi hakan ba. koda dai ba son raina ba ne, na ce Inna in sha Allahu mutuwa ce kadai zata raba ni da gidan Abubakar. Na miki alkawarin duk rintsi ba zan ta6a yin yaji ba. A hankali nake maganar cikin Kuka. Abubakar ya tsura mata ido daga in da yake yana fuskantata ne. can ya taso ya nufo ni daidai lkcn da muka yi sallama nayi musu fatan sauka lafiya. Na saka fuskata cikin cinyata ina yin kukan takaici, da me zan ji? Da wulakancin Abubakar ko da kishinsa? Ga furucin da mahaifiyata ta min. Muryarshi naji daf da ni. Me ya faru?" ya tambaye ni . Da sauri na dago kaina tare da share hawayen naki kallon in da yake,amma sai na ce dashi. Ba komai. Ya dauki wayata ya shiga duba lamabr da na gamawa wayar yanzun nan. Ya kira hr lkcn wayar na hannu Innarmu. Ta daga ya ce Salamu alaikum, Umar. Inna ta ce, Ba shi ba ne yaje shan mai, mahaifiyarsa ce, Abubakar ya kara rage murya tare da zama. Inna ina yini? Abubakar ne mijin Hafsat. Ta ce Lafiya lau, kuna lfy ko? Ya ce lafiya lau, dama naga Hafsan ce naga ta gama waya kuma tana kuka shi ne na biyo layin in ji ko lafiya??Inna ta ce, Lafiya lau ban kwana muka yi da ita na kuma yi mata nasiha. Ta dan saurara kadan, sannan ta ci, gaba da magana, kai ma don Allah ina son kayi hakuri da ita. ka kuma yi adalci tsakanin matanka,Allah ya tayaka riko. Ya ce Na gode Inna Kuma in sha Allahu zan kula. Ya dube ni bayan ya kashe wayar. Da yake ba kyason gaskiya shi yasa ki ka hau kuka don kawai an miki nasiha. To kiyi yanda ki ke so tunda nasihar ce ba ki so, ai ba yau ce rana ta farko da tace kiyi kaza ki bar kaza ba ki ka ki. , Don haka kiyi son ranki kamar yanda ki ka saba. Ya aje wayar a kan ciyata ya nufi gurin matarshi. Wadda dama duk hankalinta yana gurinmu. Sai dai bana zaton cewa taji abn da muke tattaunawa, sun gama cin abncin su suna ta hirarsu cikin harshensu na Fulatanci suna dariya. Hakan yasa na tsargu cewa zancewa suke yi don haka na maida kaina baya na dora kan majinginar kujera. Na lumshe ido ina son tuno kowace Amarya ce tayi rahin dace irina a cikin dimbin amaran da suka yi aure a ranar dana yi bana zaton za a samu Allah ka bani hakurin da juriya daure wannan abn. Ina gidan hr lkcn da aka kira Sallar La'asar ya wuce ni ya nufi Masallaci, itama ta nufi dakinta ba tare da ta kalle ni ba,tamkar in fita in tafiyata, duk da cewa bn san hanya ba, amma na cije.Me aikinta ta fito na ce ina ne gurin Alwalarsu? Ta ce Duk a bayikan daki suke yi. Na ce, ba ku da ko famfo a waje? Ta ce, ita ma bakuwa ce, jiya ta zo amma taga can fulawoyin can ana basu ruwa, kila akwai famfo a gurin. Na ko samu famfo nayi alwala nazo nan in da na tashi nayi sallata. Ina zaune ya dawo. Ya kalleni, kamar zai yi magana amma sai ya fasa, ya nufi ciki koda suka dawo falo suka zauna. Sam nayi nisa cikin tunani ban san me suke fada ba, suyi da yaransu suyi da turanci, wani lkcn har da hausarsu kamar ta 'yan koyo. Da Magriba ma da ya fita dakin ta nufa da ya dawo ina azkar ya zauna sannan ya kirata da wayarshi. Ta fito ta sake wanka da sabon ado cikin koren yadi mai ratsin ja, doguwar riga ce, tayi kyau sosai, ga kamshi turaren
Chapter 1 · 0% Book details