Sashe 20
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sabadin BOKO 4-07 Posted by ANaM Dorayi on 05:21 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya ce to shike nan, ya rubuta komai lafiya amma bai rubuta mace ko namiji ba, bare ya saka 'yan biyu.haka naci gaba da samun kula, yanzun da asiri ya tonu sai cikin ya fito yayi rum. Da da ba a sani ba kuwa lakwam, har cikina ya kai wata takwas ban taba yi masa batun kayan haihuwa ba. Shi ne da kashi ya ce "wai the only baza mu sayo kayan haihuwa ba? Na ce to, sannan muka je ni da shi da Ummi. Wata safiya na tashi da matsanancin ciwon ciki da mara, gashi ya je Lagos amma ranar zai dawo. Da ya kira duk da koakrin da na ke na nuna masa bani da wata matsala sai da ya gane. Ya kira Dada ya ce a zo a duba ni lafiya? Ummi ce ta zo har ta tafi ban bari ta fahimci wani abu ba, tunda ciwon yana yi ne yana lafawa. Kafin dare na jigata, lokacin da ya shigo fayata ta fashe haka suka kwashe ni zuwa asibiti. Da Lamido na fadan me ya sa naki fadin banda lafiya, sai su Gwogwal suka ce ai kunya ce. Lallai ni yar mutunci ce, ni ba fulani ba amma ina da kunya. A raina na ce kunya ai ta dan sunna ce bata Fulani ba. Don haka duk Musulmi mai Imani zai zama yana da kunya. Da kaina na haihu, dana kato zuwa can kuma sai sabuwar nakuda, sai kuma ga wani dan. 'Yan biyu masu kama da juna, sannan duk wanda ya kalle su yasan 'ya'yan Abubakar ne. Tunda Nurse ta kawo na farko Abubakar ya ke ta murna da su Hashim, sai ta ce zaka bani goron albishir ina zuwa. Da tazo da dayan sai suka kama murna, kafin ka ce haka, dangi sun cika asibitin harda su Rukayya. Ni dai na ga lele, Fadi ko leke don ko da ta sami labrin ina da ciki bata zo ba. Lamido har asibiti ya zo, kwanana daya aka sallamoni zuwa gida. Tun a ranar Lamido yasa aka kada Sa aka yanka, nima yan uwana washe gari suka zo tare da su Rahma. Abubakar tamkar ya goya ni don kauna. Ranar suna kuwa fadar shagalin da akayi bata baki ne. Kyauta dai mun samu Masha Allahu, nayi kyau mai zane fulawa ta yarfa min nayi kyau har na gaji. Mun sha hotuna, Abubakar kuwa da abokansa tare akayi suna dasu. Na cii gaba da shayar da yarana kuma ana basu madarar M.S.A, suka yi tubarkallah. Mijina kullum kara son mu yake. Fadi kuwa na sama kanta damuwa, kullum ita kenan fada da miji ko a gaban waye sai tayi ta karta masa rashin mutunci. Yanzun ma sun raba jiha da Rukayya, dangin mijina tamkar su cinye ni don so. Tunda na gama service na samu aiki a gidan TV na Yola, amma Abubakar ya ce sai yara sunyi kwari. Ban ja musu ba, watansu shida na soma zuwa aiki na, bayan ya mallaka mana mota ni da Fadi kowa da tashi. Bani da matsalar rainon yarana don rubibinsu ake yi. Account na bude ina zuba albashi na. Domin akwai burin da naci dasu, tunda ba abindana nema na rasa. Daidai da katin waya sai Abubakar ya zuba min dubu biyar dubu goma, nayi kyau da ka ganni kaga matar so. Gyaran jiki kuwa da sabbin girki ba a magana. Shi kanshi mijina duk wanda ya kalle shi yasan matarsa tana son shi. Kusan in mutun yana cikin kwanciyar hankali daka kalle shi zaka gane, musamman namiji. In kaga namiji a hargitse a rame ton ba halittarsa kenan ba to kila bai dace da mata ba. Duk ranar da babu aiki na kan ce ya kawo min Nana Fiddausi, ina son yarinyar don ina son mace. Fadi bata son ya kawo mata 'yarta gurina. Amma bayanda zata yi, tunda baza ta iya hana shi daukar 'yarshi ya fita da ita ba. Sannu a hankali rayuwa tana tafiya kwanukan mu suna karewa, lamurra suna canzawa. A hankali na rika dora mijina kan hanyar taimako dukda cewa yana yi dama. Lokacin da ya gina sabongida Lamido yace ya saka ni a ciki saboda ya yarda ni na zama daya daga cikin zuri'arsu. Na cancanci in sakata in wala a zuri'arsu, komai sabo ya saka min, gado dan italiya, kujeru na alfarma, kayan kicin na gani na fada. Itama ya sa aka mata fenti ya canza mata kayan daki.Nayi walima ta alfarma har su Rahma sai da suka zo, gidan ya tsaru harda gurin wasan yarana. A ranar farko da zamu kwana a gidan yana zaune yana waya a bakin gadon dakinsa na alfarma. Na shigo sanye da kayan bacci, da hannunshi ya nuna min cinyarshi in zauna, ya ce "Alhamdulillahi, gida ya dace dake." Na ce yanzu saura ka gina dakin Allah (Masallacin Juma'ar) ungwar nan ka sabunta shi. Sannan ka gina wanda za a dinga kamsus-salawati, a wannan layin da muka dawo. Ya ce "an gama gimbiya, yanzun sai ki zabi wanda za a ba kwangilar ginin." Na ce duk wanda ranka ya kwanta dashi. Mai amana." Ya ce "To zan duba." Hakan ce kuwa ta faru nan da nan aka soma gini. Taimako marasa lafiya, gajiyayyu da marayu duk na kwadaita masa yasan zakinsu. Yana mutunta iyayena tare da taimaka masu. ********** Shekarar yarana daya da wata biyu, naji ban gane kaina ba. Hankalina ya tashi matuka. Ranar Abubakar yana gidan Fadima, na mashi text cewa zanje asibiti, ya ce Hassan ne ko Hussaini ba lafiya? Na ce "Ni ce" ya ce sai ga kiran shi, ya ce meke damunki the only? Sai kawai na saka kuka na kashe wayar.Minti ashirin sai gashi ya zo. Kayan bacci ne ma a jikinsa, me aiki na ya samu tana kara goge kicin. Ya ce "ina take?" Ta ce ina ciki sai gashi na tasa 'ya'yan idanuwana jajir, ya ce wai lafiya? Na soma sabon kuka, ya zauna ya jawoni jikinsa yana lallashi na, wai in fada masa meke damuna? Na ce nifa banga al'adata ba, ya ce ban gane ba? Na ce ina da ciki ne fa gashi kuma ban yaye su Hussaini ba. Sai naji ya hau fadin Alhamdulillah, Allah ya amshi addu'ata, don Allah wannan karon ma don Allah twins, na harare shi banfa yaye yarana ba. Ya ce goben nan za a yaye su, na ce tab! Wata ashin da uku fa zasu yi. Ya ce "in basu yi kani ba ba?" Na ce ni dai zanje a bani magani." Ya fita ya ce "Me kika ce?" Nan take ya hada girar sama da ta kasa. "To shike nan kije ki cire" ya fita washe gari na tsi da amai, na sheka shi har na gaji. Nayi ta kuka karshe na kira Rahma na fada mata, ta ce lallai Hafsat samun guri, ni yanzun dakyar na samu Allah ya bani kinsan dai yawon asibitin da nayi. Amma yanzun don Allah yayi maki kyauta shen zaki butulce? To kiyi kokari ki batawa mijinki rai. Sai ta kashe wayarta. Ina kwance jikina zazzabi yaran nata kuka ko wanka ban masu ba. Ranar shine yayi masu wanka ya shrya su, sannan ya zuba su cikin mota da abincin su, sai gidan Dada ya ce mamansu bata da lafiya ina ga ma yaye su za a yi, ta ce me yake damunta? Kai tsaye ya ce ciki ne, tana can tana tana ta kuka ma. Ni dai na kawo su zan kawo kayansu. Dada ta ce to Allah ya bata lafiya. Gidana ya dawo yayi ta lallashi na. "Haba Hafsat, ke da nike kallonki mai ilimi da sanin yakamata? Bai dace kiyi irin wannan tunanin na jahilai ba. Kinsan matsayinki a gurina? Duk yanda kike tunanin matsayinki ya wuce haka a gurina. Kada ki zubar da kimar ki a idona, ina alfahari dake, kuma yayin da kike haifa min 'ya'ya lokacin ne nake kara so da kaunarki." Kunya ta kamani, lallai naso nayi wauta. Yanda mijina ke nuna min baikamata inyi masa haka ba. Ni da na kasance mai bada shawara ba girmana bane in yi haka, don haka sai nace kayi hakuri Mr Cool. Tausayin yaran ne." Ya ce "yanzun ma kayansu zaki hada suna gurin Daada, mu kuma sai muyi rainon wannan ko? Na ce ya zaka kaima Daada aiki, kasan fa barna suke dashi." Ya rike tafin hannu na ya ce "ni suka biyo Dada ta ce lokacin da ina yaro nayi barna, ai kin san kuma ga Ummi ga Rukayya ina kaisu kowacce ta zabi nata, na ce Allah ya raya su." Fadi taji cewa an yaye twins sai ta zargo ko ciki ne dani, don haka hankalinta ya tashi. Har gida sai gata da yake bata taba zuwa ba, tayi ta bin ko ina da kallo, sannan daga bisani muka gaisa. Na ce "Maman Nana yaune kika taba zuwa gidana." Ta ce "to bama zama ko nazo kina gurin aiki, nima haka." Na ce "Amma koda dare?" Ta ce "da dare kowa ya gaji, yanzun dai ba gashi nazo ba." Na ce to na gode" ta ce "can naga su husaini a gidan Daada, wai an yaye su, na ce me ya jawo maki yaye yanzu?" Na ce Abban su ne ya kwashe su ya kaisu. Ta tabe baki lallai sweet heart shine lokacin da zan yaye Nana ya hau yayi ta fada. Na ce to ai kinga ita mace ce, dole ya tausaya mata, ta ce kodai kin sake kunsar wani cikin ne? Na ce to inma hakan ne meye aibu tunda mijina na so? Ta ce kedai fadi gaskiya, kina son kiyi ki cika gida da yara saboda kiyi gado." Ta mike tsaye, "kiyi haihuwarki a sannu dan mu mungaji kudi, so kinga banda matsalar su. Na ce gaskiya ne baki da matsalar kudi, shi yasa na ganki zaune a gida bakya zuwa aiki, sannan suna nan cike da daki a gidanki sai dai ki bude ki diba. Ta ce "inma kina yi min ba'a ne nasan dai na fiki." Ta fita fuuu, na ce "sauka lafiya." Tare muka je asibiti dashi, inda likita ya gwada ni ya tabbatar cikina wata