Sashe 21
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read
uku. Kuma lfy lau, sai murna gurin mijina. Munje Umara tare harda ita, haka nan aikin hajji lokacin cikina ya tsufa. Mun dawo bada jimawa ba ba haihu, 'yar budurwa mai kyau, tamkar inyi tsalle don murna. Ina son 'yar budurwa, itama anyi sha'ani, don lokacin Abubakar ya kara zama (Don). Yarinya taci sunan Daada, Abubakar yace ya yarda in kana taimako Allah yana taimakonka. Budi ta ko ina, sai yanzun na binciki kudin account dina, lallai kudi wawaye ne, in da zaka tara su zasu taru, don haka na kuduri niyar yin abinda zanyi dasu. Kaduna naje yawon arba'in, na dauki babana na kaishi aka yi masa hoton fita, wato international passport. Lokacin aikin hajji kuma na biya masa. Abubakar ya fara min fada wai yana cikin lissafinshi a bana zai biya masu. Na ce yayi hakuri alkawari na dauka, SANADIN BOKO sai na kaishi makkah. Ya ce "Allah ya biya ki" shi kuwa baba da na fada masa na biya masa kujera da kudin aikina sai ya sa kuka. Ya ce gashi SANADIN BOKON nan da nayi ta tsana zanje daki Allah, inda ban taba zaton zuwa ba. Ki yafe ni Hafsa, tuni na gane boko ba dukka ta ba ce illah, tana da amfani." Ya ci gaba da cewa Hafsa na gane hakan ne ta hanyar taimako da wata likita mace tayi ta mun lokacin da na kwanta a asibiti. In shaa Allah su Ummi zasu yi karatun boko, dama dai na addini wajibi ne, zan bisu da addu'a Allah ya tsare su yasa su sami ilimi mai amfani. Ya raba su da sharrin ko hadarin da ke cikin boko, na ce ameen Baba. Ya ce in da zaki yi adalci Innar ki ya dace da wannan kujerar, don ita ce tasha wuyar iliminki." Na ce "ita ma Abubakar ya bata kujerarta da Yayana Umar, kai nidai na gode Allah da nasha wahala yanzu kuma ina cikin gata. Wata rana na matsawa Abubakar muje katsina ina son in sami labrn yaron dr Hindu da yake munsha zuwa gidan nasu lokacin tana raye. Sai ban sha wahalar gano gidan sosai ba. Cikin sa'a ma yaron an kawo shi hutu. Duk sunyi girma, naji dadin ganin su, na karbi adireshin dinsu na Abuja. Nasha alwashin zuwan sannan nayi masu kyauta mai tsoka. A kwana na biyu na nemo Asabe tayi aure da yaranta biyar. Sai dai gaskiya basu dashi, na taimaka mata sosai. Ta ce min tana son zuwa gurin yarta tana tsoro, na ce zanje mata. Wata rana munje Kano Rahma ce tayi haihuwa ta biyu muka je, daga nan ta tambayi inda zan sami hajiya Mairo, Da dare naje gidan bayan isha'I cikin shiga ta alfarma da dankareriyar motar mijina. Da kima ta marabce ni domin tasan daga ganina taga matar gwaska, falon alfarma ta kaini muka gaisa bayan an cika teburin gabana da kayan shaye shaye. Ta ce ban gane ki ba, na eh baza ki gane ni ba daga Yola nake, ni 'yar uwar Asabe ce wadda ta taba maki aiki kuma take da da tare da danki mai sunanki, shine nazo na ganta." Ta ce Allah sarki sai ta soma kuka, na ce "lfy? Ta ce ai dan tilon dan nawa tuni ya mutu, tunda ya dawo daga kasar waje ba lfy inda yaje karatun boko." Na zaro ido "shima sanadin bokon ya rasa ransa?" Ta ce wallahi yar nan can abokai suka bashi wata kwaya mai karfi yasha. Tunda ya kwanta tashin da bai yi ba kenan sai a kiyama." Na ce tabdijam, yanzu ina ita takwarar taki? Ta daga waya ta kira wata tace jeki ki kira min Ummi, ta dube ni yanzu ita nake gani naji dadi. Kinga da na salwantar da yarinyar nan da nafi haka bakin ciki."yarinyar ta shigo cikin kayan bacci, mai kyau da ita, girmanta bai wuce na shadad ba, na rungume ta ina murna. Na ce Allah ya albarkace ki. Hajiya ta ce ameen, na dubi haji kada a barta ba ilimin addini, domin inda addini, boko bazai batar da bawa ba sai wanda ya batar da kansa. Ta ce haka ne 'yar nan ai naga darasi, in sha Allah yarinyar nan zan mata tarbiya irin ta addini,na ce Allah ya sa. Na kawo kudi na bata na ce ki sayi sweet sannan na amshi lambobin wayar su na ce zan ba mamanta. Nima zan dinga kira muna gaisawa, ta ce don Allah ki kaima uwar tata don ta zo ta ganta. Na ce in shaa Allahu ***************** Rayuwata ta zama abin sha'awa a idon wadanda zuka kyamace ni da. Duk wanda na sani taimakonsa nake yi. Mun sami daukaka ta fannoni da dama, 'yan uwana suna hutawa a dalilina. Abubakar yasa na bar aiki na koma makarantar jami'ar Yola, hatta kishiyar mamana sai da Abubakar ya bata kujera.