← Book details Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 22

Sashe 11

Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yi tsalle sai sake zuba mishi na ke, ya ce, "Bar shi kada in kasa bacci." Na sirka mashi ruwan wanka, ya ce da na sanyi zai yi na ce, "A gajiye ka ke zaka fi jin dadin wanka da na dumi." Ya ce, "To." Daki ya shiga ina daga waje ya bude jakarshi ya canza kaya, sannan ya ce, "Zo ki raka ni in kama masauki." Na ce, "Nan gidan ba za'a iya bacci ba?" Ya yi dan murmushi, "Zo dai mu je mu dawo." Shahararren masaukin bakin nan muka je ya kama daki, na bata rai. Bayan mun zauna bakin gado ya ce, "Yi min dan murmushin nan mana." Na dan harare shi da wasa, "Ba ka 'ki kwana gidana ba." Ya ce, "To ni nan zaki taya ni kwana." Na zaro ido, "In taya ka me? Tab! Tunda dai na rako ka maidani gidana." Ya ce, "Tsoro nike ji, dakin yayi min girma." Na harare shi tare da cewa, "Da can ba kai daya kake kwana ba?" Ya ce, "To ai yau na soma jin tsoron, ba kin ce kin min tanadi ba?" Na ce, "To ba na baka ka ci ba?" Ya ce, "Daman wai tanadin abinci ne?" Na ce, "Eh mana." Ya ce, "Ammafa ba haka muka yi da ke ba." Na ce, "To yaya muka yi?" Ya mike ya dauko jakarshi, "Zo ki gani." Ya fitar da duk kayan jakar, can kasa ya fito da wasu kaya, kayan baccine 'yan India masu shegen kyau, baki da pink ne. Ya fito da pink din ya ce, "Gwada wannan in gani." Na amsa na daga ina kallo, akwai kyau amma zai fi dacewa da sunan Fandarinki tsirara. Na yi tsaye ina kallonshi yana mai da kayan, ya mike, "Kawo in gwada miki." Na ce, "Zan iya." Na fada toilet na saka, na dubi kai na, zan iya fita kuwa? Na yi ta maza na kama kofa zan bude, sai kurum na ga ya bude ya shigo. Na runtse idona shi kuma ya ce, "Kai cancadi! Zo mu je in miki hoto." Ya rikeni muka fito. Ya zauna bakin gado tare da dorani kan cinyarshi, Kai Subhanallah!!! Abubakar ya fara shafani tun daga wuyana har ya sauko kirjina wanda ba kace na shayar da Shadad ba, ya rude ya shiga kissing dina, anan dai ya dinga yaba min irin goyon bayan da na bashi tare da tanadin da nayi masa, ya dinga min surutai wanda bana gane mai yake cewa, sai dai numfashinsa kawai nake ji, kai ba zan manta da wannan rana ba, son Abubakar da kaunarshi gami da kishinsa sun karu gareni, kai na so in cuci kaina, kuma na yarda cewar soyayyarshi mai tsada ce, amma na kula shima ya yaba da ni matuka. Nan muka yi Magriba da Isha'i munata tarairayar juna, ian kallonshi ya kashe dukkan wayoyinshi, a takaice dai nan muka kwana muna faranta ran juna cikin farin ciki, ko kuda baya son yaji a jikina. Misalin Goma na safe muka dawo don 12 zai nufi Yola, amma sai muka bude sabon shafin soyayya anan gida na, ya dinga lugwiguita ni yana zantuka iri-iri masu wuyar ambato, Abubakar ya dinga santi tare da yabon Hafsa cikin kalamai masu dadi, nan muka kwashe lokuta da dama dan bamu san lokaci ya tafi ba, har ya so ya makara. Ni kam da zai tafi har da kukana, ya lallashe ni da cewa jibi zai zo mu wuce Kaduna don karkare shari'ar nan, da kyar ya lallasheni sannan ya tafi. Kwana daya jal da muka yi ya sani na manta duk wata damuwa da ke raina, lallai Abubakar shine irin mijin da mata ke so, wanda zai shagwabaka, ya so ka kuma ya riritaka, har ka mance a duniyar da kake. (Ohh! Su Hafsah sai sambatu ake) Ya san so yasan sirrin so, ya san yanda ake zama da mace. Haka ya tafi ya barni da kewarsa duk na rikice. Da dare ina kwance tamkar in kirashi amma sai na tuno can mafa yana tare da matarshi, kishi ya isheni, yanzun duk irin kulawar nan da ya bani haka zai bata? Sai hawaye masu dumi suka soma sakko min, can dai na dauko wayata ina kallon hotunan da muka dauka ni da shi cikin soyayya da kauna irinta masoya, lokacin muna cin abinci cikin soyayya da tsokanar juna a masaukinsa, kawai sai na samu kaina da rubuta masa I LOVE U na tura masa. Can har na fara rubuta dogon text na soyayya, sai kuma na fasa na ce abinda baka so a maka kai ma kada kayi ma wani, don haka sai na danne. Kusan 12 sai ga kiranshi, da sauri na daga, a hankali yake magana ina zaton ko Matarshi ta yi bacci ko kuma ta dan fita oho, ya ce, "The only kina jina?" Na ce, "Eh." Ya ce, "Na ga sakonki, ina sonki sosai, ba zan manta irin kaunar da na sha a gareki ba, kin jiyar da ni dadi matuka, inata tunanin kasancewa tare da ke, kiyi bacci kinji?" Cikin Marairaita na ce, "Ba zan iya ba Cool, yaushe zaka zo?" Ya ce, "Zan kira ki anjima kin ji?" Na ce to. Ya ce, "To in kin kasa bacci tashi kiyi mana addu'a Allah yasa mun samu Baby." Na ce, "To Cool, miss U." (Hhhhhh, Su Hafsah an hau duniyar sama an gaza saukowa) Hakan kuwa na yi, da nayi alwala na dauki Al-kur'ani na soma karatu, sai na samu nutsuwa. Kusan 2 na dare ya kirani, "Me ya hana ki bacci d only?" Na ce, "Tunaninka mana." Ya ce, "Nima kina raina Hafsah, da ban same ki ba da nayi asara." Na ce, "Wai! Ni ce zan ce da nayi asara don irinka akwai wuyar samu." Ya ce, "Maza da yawa ba zasu gane ba sun fi kallon kyan fuska, Hakika suna zaban tumun dare." Na yi dariya sannan na ce, "Ka kwanta don Aunty Fadima ma baza ta so muna yin doguwar hira lokutan kwanan ta ba. Sai da safe." Ya ce, "To." Na sake alwala na zo ina Nafila dan wannan sallar tana da Muhimmanci gurinmu, in har zaki yarfe bacci ki tashi daidai wannan lokacin ki fadama Allah, to kuwa duk wata matsala taki zata yaye. Ubangiji da kanshi yake cewa da mai bukata ya tambaye shi Shi kuma ya biya mana, wannan kadai na tsare, ba boka ba mallam ga matsalolina a hankali duk sun warware. Allah ka yaye mana dukkan matsalolinmu Ameen. Ranar Lahadi kuwa ranar da zai zo cewa yayi in masa tuwon semo, sai kuma in masa jus din Shinkafa din nan. Miyar danyar kubewa na yi masa, ta ji bushashshen kifi da nama, na masa jus din shinkafa, sai irin kunun ayan da nike sha mai dabino da kwakwa da zuma. Wando da riga na ci sabbi ne na siyo su, da ina zaton ba zan iya saka wando ba amma daga baya sai na ce kiji kana cewa baka iya kukan mutuwa ba Uwarka ce mata mutu ba. Da kadan ya wuce gwiwata, rigar ma ta dame ni. Kallona yayi ta yi tunda ya shigo na masa oyoyo, da kyar na bambare daga jikinsa don yi masa shimfida, ya ce, "Ya ya aka yi kika san ina son shigar English wears?" Na ce, "Duk abinda ka ke so a kwayar idonka nake karanta, ai ba kallon kawai nake maka ba." Ranar dai mun ciyar da juna abinci, sannan muka shiga wani shafin, daga baya muka yi wanka muka dunguma gidan su Rahma. Shadad kuwa sai tsalle da ya ganmu, da zamu tafi ya so binmu, har zan ce mu tafi da shi sai Abubakar ya ce, "Shadad unguwa zamu, amma gobe zaku taho da Uncle dinka na nan gidan." Ya ce, "To." Muka dawo nan gidan muka kwana. Gaskiya duk macen da ta samu miji kwatankwacin Abubakar, to ta gode ma Allah, mamaki na daya, yanda ya iya kula da mace ta kowanne fanni......
Chapter 11 · 0% Book details