Sashe 4
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 4-02 Posted by ANaM Dorayi on 06:37 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya daddogara yafito, bayan sun gaisa, sai yace dama yazone da batun yaro, wanda 'yarshi ta haifa, baba yace banganeba? Munnir yace, baba baka ganeniba? Ninefa munnir saurayin hafsa, kuma dan data haifa nawane, shine na ganshi gurin bikin nan. Dady Yace, duk abinda aka kashe zan biya, munzone mu sulhunta abamu yaron,ran baba ya baci,ckn xuciyarsa kuma yaqi yadda da yadda suke so.Tun farko matsalar me yana kawo cuta da cin xali don suna takama da kudi shine xasu daurewa dansu gindi yayi wa yarinya mugunta?Baba yace gaskiya ni bansan da wannan xancen ba "yata kuma ba a nan take ba a kano take sannan dan da kake magana yana da ubanshi.Daddy ya kalli munnir toh kaji?Munnir fa daddy yaron yayi kama dani sosai.baba yace itace hujjark kawai?nan gaba wannan ba hujja bace don nasha ganin masu kama dani da sai in bisu ince yayana ne? Daddy yace to wai yanxu ina yaron yake?baba yace sun tafi gidansu sai anjima.ya nufi gida daddy ya hau munnir da fada wai ya musu karya.suka shiga mota suka tafi ,shidai munnir ya tabbata danshi ne kuma xai ta bin diddigi sai ya amshi dansa.ya lumshe ido ya tuna kyakyawan fuskar yaron mai kama dashi mai cike da wayo da dabara gami da lfy.Mom tayi jigum dajin cewa xancen ba gaske bane.tace ina ce son yara ne yasaka yin haka toh ai shi kenan.Munnir yace nidai nasan dana ne kuma xan ta bin diddigi har sai na samo shi.Daddy yace in kaje ka janyo rigima kaga dan wani kace naka ne kai xaka kwana ci.mom tace kai dai ka barshi ya san nashine ta kalli munnir kabi diddigi xamu dauko lauyoyi.Munnir yace yauwa mom danAllah ki sayamin donko nasan cewa yaron nan nawa ne.tace kada ka damu kaidai kabi komai a sannu.ya mike ya fita daddy na kara jaddda musu cewa shi fa ba ruwansa. Kasan cewar ban samu bacci ba sai ya xamana na makara, nayi sallah tare da shirya shadad. kaxar jiya na bashi da milk din yaci.sai ga yayan su Rahma yayi sallama na saka hijabi na fita muka gaisa,yace shadad ya fito xai kai su makaranta shi da yayan sa dama mama tace min shi ke kaisu,duk da cewa ba makarantar su dayaba.muka gaisa suka tafi na shigo na gama yan gyare gyare na nayi wanka.ankon bikin rahma nasa ya shigo da sallamarshi hannuwansa dauke da ledoji farrera guda biyu.na fito da sauri na amshi tare da cewa sannu xuwa yace yauwa sai ya sake fita dauke da buhun shinkafa ya shigo.haka ya dinga shigo da kaya ina ta masa sannu da xuwa har ya gama.na shimfida mishi tabarma a ciki ya xauna na gaishe shi ya amsa.ya amsa ba yabo ba fallasa nace mai xaka ci in maka ya dubeni ido cikin ido yace am ok.ya kalli agogo yace jirgin karfe goma xan bi xuwa yola,na kalli agogon bango karfe 8.na dubeshi wani sonshi ke fisgata kamar in sa kaina a jikinsa.kamshinsa mai sanyin dadi ya karade ko ina acikin dakin, muryarshi ta kaseni.""ki duba abubuwan dana kawo in akwai abinda kike bukata babu sai ki gayamin.Bansan me yasa muryata ta dishe ba nace ko ban duba nasan abundaka siyo sunyi.Allah ya kara budi nagode.yasa hannu cikin aljihu ya kirga kudi naira dubu 10 ya bani.ki riqe wannan bani no mai adaidaitar da yake kaiku makaranta na dauko wayata na dauki lambar tare da mika mishi harda wayar ya amsa tare da dubawa.ya kirashi ya amsa .ce masa yayi yana jiransa an nan gidana yace toh.na sake cewa kodai indomie xan dafa ma yace a'aah.ya fito da wayarshi daga aljihusa tana ruri tare da karawa a kunne yace sweet honey. gabana das ya fadi tabbas fadi ce na mike na fita raina daure naje in kwashe kayan daya xubamin.dana gama na xauna waje kan kujera ina son in tuno abin da abubakar yayi min me yake nufi dani? tamkar in bar gidan saboda bakin ciki yanda suke hira da daria.duk da cewa yarensu suke yi sai turanci jifa jifa sunkusa minti ashirin sannan suka yi sallama.wayata dana baro a dakin sai ta shiga ruri ya dauka ashe dan mai adaidaita sahun ne ya iso don haka ya mike yace yana xuwa.ta gabana ya fice,kusan mintin 5 sannan yace ni xan wuce.na ce saboda anagutsirrkah dole kace xaka tafi ,ko kuma ince ka kosa xaka tafi daga wurin maqiyarka.yayi dan murmushi hakan ne"ya cigaba da cewa ni xan tafi kamar yanda nace kuma ba xan cemiki ga randa xan dawo bah sai san da na samu sukuni.haka nan kuma bayan mkrnt ban laminta aje ko ina ba sai an nemi ixini in sani.maganarshita fako ta kona mun rai wai hakan ne kenan ni makiyarsa ce,na dago na dubeshi "wai mai nayi maka ne kake son kuntata wa rayuwata?tun daga ranar dana sake ganin kah na rasa sukunina,meye nufinka dani? :kuka ya subuce min yace "au da ke baki san kinyi wani abu ba ?to duk ba wannan ba ni me na miki.kince mkrnt na dawo dake na baki abinci na baki kudin cefane, na daukin nauyin dake a kanki na dawo dake.me kike so bayan haka?ya sake matsowa kusa dani tare da sausauta murya "fadamin in kina da wata mastalar?nayi shiru ina son tuna me xance?sai ince baka sakar min fuska kuma baka saurarena ?kai gaskiya in nayi haka ba da kai ne...ya katseni dake nake nace akwai sauran matsala?na dube shi ka fini sani.ya sake matsowa ya ce kuntatawar da nake miki ?nace da ban hadu da kai ba hankalina a kwance.yace saboda ba ki sona koh?haushi ya sake cika ni ,son shi ya cika ni ya hanani sakat sannan ga abubuwan da suke biyo baya,amma xai ce wani bana son shi.bansan sanda nace eh!ai tuni nace bana sonka mai yasa ka tursasamin har sai da ka aureni.ya xura min ido.nayi laifi dana raba ki da rayuwar kangi da gantalin bin maxan d akike yi?na mike tsaye ni kada kamin sharri baka ganin a dandi ba.yayi yar daria yace yaro yaro ne koh ba da kanki kika fadamin cewa ke karuwace a nan gidan ba a wurin nan bah.kila ma dan gidan baya magana ne daya shaideni,nalumshe ido ckn takaici na ce magan xarar bunu na nufi daki shikuma in jin fitarshi.nayi kuka mai isata sannan nace laifina nake nina kashe kaina.shi kuma a cikin jirgi yayi jugum gani yake ya xalunce ta, bai dace ya ringa jefa mata magana ba in yai la'akari da ya fa aureta. :Saidai har yanxu yana takaicin kasancewarta karuwa ce ada bai san adadin maxan da ta kwana dasu ba.Don haka kyankyaminta yake yi in ya ganta sai ya tuna lkcn da take gayamasa ita karuwa ce.sai yaji haushin ta.sai dai duk wannan bai hana sonta yayi anbaliya a cikin xuciyarsa ba.ni kam haka nayini da takaici,washegari haka na bufi makrnt tare da yi wa Sa'adatu suleiman godia.na samu duk tayi min test dina.nan suka yi tamin tsokana wai daga xuwa daurin aure sai na bi miji yola nabarsu da katin walima.daria kawai nayi tare da basu hkr.sam bana xuwa ko ina sai mkrnt.daidai da gidan su rahma bana shiga sai dai in aika shadad yace in gaishe da maama.in nayi abincin marmari sai in aika mata koh in ina dawowa daga makarnt sai in siya mata goro in aikamata dashi :Rahma ma ta gaji da tambayata yaushe xanxo sai gata rannar wata lahadi.itace ma na ba wa dinkunana na ce taje dasu ayi min, tace inxo muyi mgn da telan, nace rahma Abubakar ya hanani xuwa ko ina inba mkrnt ba.ta ce toh"xamuyi magana ta waya in yaso sai in baki no telan nace toh!!nagode.tunda ya tafi sai daya kwana biyu sannan ya kirani ,gaisawa kawai muka yi yace in bashi shadad su gaisa na bashi suka yi ta surutun su hardai na tashi naje nayi sallar isha'i sannan suka yi sallama.shadad ya dube ni Anty kinsan me?nace a'aa yace Uncle yace wai da ina da ina kike xuwa bayan mkrnt nace babu koh gidan su maman rahma ma kin dena xuwa.sai yace ki ringa xuwa kina gaisheta.wai kuma ince miki sai da safe ,kuma in muna son wani abu ki fada mashi ta txt.nace shadad tashi kasa kayan bacci,ka kwanta "cikin xuciyata kuwa nace koda xaya kirani ba xan cemi shi bamu da komai bah koda ba mu dashi.:Kullum xai kirani daidai wannan lkc wato bayan sallar isha kenan,tsakaninmu gaisuwa.kuma xai ce in bashi shadad suyi mgn a waya ,wani lkcn ma kwanciyata nake yi in sharesu inyi bacci na.kwatsam ranar wata juma'a a lkcn muna tsakiyar jarabawa na dawo a gajiye ga tarin gajiya don kullum karatun dare nakeyi.na watsa ruwan sanyi,bacci nake ji baxan iya girki ba don haka gari na jikawa shadad da madara na rufe gida na kwanta.banyi nisa cikin bacci ba anji shadad yana jijjigani .Anty a buga gida inje in bude?Anty? da kyar na amsa.shadad danAllah ka barni inyi bacci.Anty ana fa buga gida inje in buda.nace jeka shadad.naci gaba da baccina.ya taka kujera yaje ya bude nan take ya dane Uncle dinshi suka shigo tare.nayi dai-dai kan katifa na dura kaina kan filo tsakiyar kafa funa na saka filo a tsakiya.sanya nake da farar singlet sai wani siket dina mai fadi ,tsawon shi daidai gwiwata,ya tsura min ido lallai hafsat nada durin jiki mai kyau ,kuma daga ganin fatarta xaiyi laushi.shadad ya soma girgixa kafata Anty tashi ga Uncle anty,a firgice natshi don har ckn kaina naji kiran.idanuna jajir nake kallon shadad "menene?ba nace ka daina tashi na ba ya nunamin Abubakar dake tsaye ya kafe ni da ido.da sauri naja hijabina na rufe jikina sannan nace sannu daxuwa "ya lumshe ido tare da amsawa a ckn wata sarkarkiyyar murya.naja xani na daura sannan na shimfida mashi tabarma na dauki hulata na saka na nufi kitchen.dama naxo da kankarar pure water saboda xafin kano kullum nakan xo da kankara in saka cikin kula.da dauko nikarkiyar shinkafa ta wanda na samata kayn kamshi,na tace na saka mata flavour mai kamshin kwakwa naje fa kankara ckn jug.na dora kan tire da kofi naxo na dire a gabanshi.:na tsiyaya masa ckn cup