← Book details Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 22

Sashe 2

Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

amarci na tashi. A raina na ce, Lallai wannan sai na dage a gurin kwalliya. Ya zuba mata ido, hakan ne yasa na saki baki, kai Hafsa bata yi sallah ba? ta dube ni.ta ce, Gidan ba bakonta ba ne, ita ce ta ki ta shigo, Ya ce, A"a fadima Fadima gidan nan bakonta ne a yanzun,don bata san in da zata shiga ba sai in ki mata jagora. Nan da nan sai tahade rai ta soma magana cikin Fillanci, shi kuma ya ci gaba da magana da Hausa, yana cewa. Ba wani son kai ko bambancin da na nuna miki, in dai kina son gaskiya. Na ce, don Allah ku bar magana laifina ne, ni ceban bukaci shiga cikin ba. Ya ce, mata,To shi kenan zan nuna mata komai ni. Har zuwa lkcn da muka baro gidan ban sake cewa komai ba. Mun biya gidan su Hashim, matarshi mai kirki, daga nan muka nufi gidan iyayenshi. Ummi tazo da gudu ta rungume ni. Rukayya kam tana ta danna waya ko kallo ban ishe ta ba. Na zube a kasa na gaida Daada, sannan na zauna a gurin .Tayi tayi in hau kujera na ce mata kasan yayi. Ta ce masa daga ina? ya ce Gidan fadi ya kai ta. Ta ce, ya hada mu ya yi mana nasiha? Ya ce, eh, ni dai na sunkayar da kai ina tuna nasihar da ya mana,wai mu zauna lafiya, muyi kishi irin na gidan Annabinmu (S.W.A.) Ya ce wai in bi Fadi don ita ce ya za6a uwargidansa, sannan in girmamata baya son raini, ita kuma wai ta kama girmanta, sannan ta dinga hakuri. Ummi ta katse min tunanina, Anty tashi muje ki gaida Abbanmu yana falon shi. Na mike na bita,shima nayi cikin kunya da girmamawa na gaida shi, yayi mun nasiha da in yi hakuri, in yi biyayya sannan in saba da zuri'arsu. Kada kuma na yi wani abu na 6atanci wanda zai sa zuri'arsu suyi da sun sanin shigowata cikinsu. Nayi godiya tare da yi mishi alkawarin kiyayewa. Da zamu tafi har bakin mota suka raka mu. Daada da Ummi, amma Rukayya sai da ya yi mata magana sannan ta gaida shi. Kafin mu iso gida sai da muka tsaya a wani super store muka yi parking ya shiga. jim kadan ya fito da ledoji kuda biyu ya shiga muka wuce.shine ya ruko ledar har dakina.Na fada bandaki donyin alwalar sallar ishai ina fitowa yacemin shifa xai wuce nace toh,har ya kai da kofar daki nace masa ledar ka manta ya waiwayo sannan yace taki ce.na dauka na duba kaxa ce da kayan lashe lashe na zaki nace ka kara muku ni yayi min yawa tunda kaga ku uku ne duk da yar aikin gidan nikuma ni daya ce.ya juya tare da cewa na fiki sanin mu uku ne ai! ya atfi abinsa na tada salla ta.A randa na cika kwana biyar, misalin tara na dare yace in shiri gobe da taran safe xamu wuce kano ,ina murna harda da dan tsalle na.Allah na gode maka da har nacire rai da karatuna,nan take na soma hada shirgi na.da safe dana gama shiri naje na gaida mutan gida na kuma fada musu xan koma mkrtn yau.duk suka min addu'ar fatar alkairi don doki kasa break din kirki nayi.ya iso sanye da na kalar sararin samaniya.yayi kyau,ni na shirya ya kalli kayana.Uhumm dama duk kin kosa ki koma koh?saboda mu cin namar jikin muke yi koh?na sunkuyar dakai bance komai ba ya dauki babbar jakar niku na dauki karamar da ta ratayawa.duk yan gidna sun min ftan alkairi da sauka lfy usaman kanishi ne yaja motar.shi da hashim suka kaimu filin jirgin sama gabana sai faduwa yake.yau ce rana ta farko da xan fara hawa jirgin sama jikina sai bari yake tayi.ina xaton abubakar ya dagoni sai ya tallafoni xuwa gefen kafadarshi ,na lumshe idanu har muka shiga muka xauna sannnan ya sake ni.jikinsa mai laushi da kamshi wani sonsa ne ya ratsa ni tamkar in kwanta a jikinsa...ckn lkc kankani muka sauka a kanon dabo inda rahma da sagir ke jiran mu.ckn murna na rungeme rahma sukuma suka kama hannu suka gaisha.gidan sagir muka je sai d akarfe uku sannan muka fita. na kosa muje gidan dana ke don inje gidan maman rahma inga shadad. Kai tsaye gidan maman muka wuce muna shiga naga shadad na wasn kwallo.da gudu ya taho sai na bude hannu amma sai yaron nan ya wuce wurin Abubakar ya daga shi sama nikam nayi ciki.mun gaisa da maama inda na amshi dan mukulli sannan nayo gaba.su kuma suka biyo cikin motar sagir daya amsa.mun hadu da wasu makota daidai ku, sun mun murnar aure nayi godia.na bude gidan cikin xakuwar shigarsa.yana nan yadda na barsa.na bude daki xan shiga shikuma yace toh ni xan tafi.nace toh sai ka dawo shi da shadad suka tafi.na gama na sa turaren wuta,shawarar rahma ta fadomin lkcn da muke kulle ckn daki.kafin ya tafi kiyi kokarin janyo shi gare ki ta hanyar ado da sauransu yasan ke mace ce "nace hmm shi da matarshi tamkar india,ga iya ado tamkar dawisu ,har wani burge shi xanyi.tace tabbas xaki birge shi yasn da mai kmr indaiyar yanace sai daya same ki,nace toh hum xan gwada. bayan maghrib suka dawo yana dauke da ledoji suka ajiye suak ce sun tafi yin ishai nima sallar nayi na sake fenta fuskata na sake kaya.riga ce doguwa rahma ta yadi ta bani mai rawa ce sannan ta ilahir jikin duk motsin dana yi sai ya bayyyana.yau ce rana ta farko daya shigo ckn dakin gefen katifa ya xauna shadad ya xauna kusa dashi.ya kalli abubakar yace anty bata ci abinci bah"yace xata ci ya kara cewa uncle in xaku kara tafia ku tafi dani.yace toh xamu atfi da kai.haka suka yi ta hirar su ina ta kallon shi yana satar kallona.na xauna tare da janyo ledar na duba madara mai snayi ce.na dauka na sha.na kalleshi muka hada ido sai ya kauda kai ya ciro waya yana kirar layin matarshi.ya kishingida yana magana cikin fillanci haushi ya kama ni.sai kawai na fita tsakar gida.ya jima sannan ya fito lokacin shadad yayi bacci, yace na kam na tafi masaukina.da suari na dube shi nace masauki?bansan ma ya fito bah yace eh masuakina nace hum!!sai da safe.yace toh takaici ya isheni me yake nufi dani?me yake son mai dani.ina kwance dare ya tsala amma na kasa bacci juyi nake yi kurum a kan katif.ni mutum ce kuma mai lfy ina matukar son ganina kusa da maigidana.naja tsakin takiaci me yasa da ban damu da wani namiji ?wata xuciyar tace lokacin ba kida aure, yanxu kuma kina da miji wanda kuma kina so.daga karshe dai na mike nayo alwala nayi sallah wanda ita kadai ce mai mun magani damuwa. ***** ***** ******** Munnir yashiga gdansu cike da tunanin ta ina zai fara yiwa iyayensa bayani, yace mum, tadubeshi cike da tausayi, don tunda yaci karo da ciwon nan suke tausaya masa, tace lfy munnir meya faru? Yace mom eh....daman...wataran....sai yai shiru, tace kayi mgn mana menene yafaru? Yarike kai, tace ciwo yakeyi? Tazo gabanshi a rude, yace mum wani yaro nagani kuma muna matukar kama, kuma ada maman yaron budurwatace, IYE!!! Mekace? Tazauna gabanshi a kasa, tace yimin bayani yadda zan fahimta, tace inba wani abu yashiga tsakaninkuba toya daga ganin yaro dan yayi kama dakai sai kace abaka? Yace mum shekarun baya zaki tuna wata yarinya datazo gdan nan tace tanada ciki? Tayi shiru tanason tanawa shikuma yayita mata kwatance har saida tagane, yace to itace mum, kuma nasan cikinane tunda nina mata ta karfin tsiya, (oh kuji rashin ta ido) mum tace inane gdansu? yace nan abj road ne, tace to bari dadynku yadawo saina masa bayani. Da dady yazo tafada masa, nan da nan sai yau murna tare da shan alwashin in zai karar da duk abinda ya mallaka saiya amsa jikanshi da namiji, munnir cikin murna yace, dady itace wadda yan yola sukazo daurin auranta yau din nan, cikin mamaki dady yace, kana nufin daurin auren damukaje? Munnir yace eh dady, yayi shiru yana tunani, mom tace, ina ruwanmu don dan abokinka ya aureta? Allah yakaimu gobe, nida kaina zamuje gdan, hakan kuwa ta faru, misalin karfe 10 na safe munnir da dadynshi sukayi sallama kofar gdan baban hafsa. Daman baba yana zaune inda yayi sallar walaha bai tashiba........
Chapter 2 · 0% Book details