Sashe 17
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 4-06 Posted by ANaM Dorayi on 05:20 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na ce, "Za ka biya ko in biya?" Na fada cikin daure fuska, ya ce, "A'a zan biya in basu amsa ba sai kin san yanda zaki yi da su." Fadima ta ce, "Neman gindin zama." Ban ko kalle ta ba shima bai ce komai ba. Da muka isa gurin da ta sai Shaddoji da Yaduka sai na dibar ma Abba, ya ce, "Dama kin daina wahala na fa san ba zasu amsa ba." Don haushi ban kuma tanka su ba, don Fadi sai dariya take yi, ban fasa dibar musu ba, har turaruka na dibarma Abba, su kuma kayan shafa. Ita kuma muna zuwa gurin kayan Babys nan tayi ta jida, kowanne bibbiyu ni ko nayi ta taya ta. Da muka je gurin takalma da jaka na zaba musu. Da zai sai nashi na zaba ma Abba har huluna ya ce, "Ke baki san lambar takalma ka kina ta diba har da hula." Na ce, "Ido ba mudu ba ya san kima." Ita kuma ta ce, "In da rabon ka tafka asarar kudi ai shi kena." Ni sai na sharesu kawai na ci gaba da lamurana.Mun dawo gida cike da lodin kaya, but din mota shake, kujerar baya shake, da kyar na dan samu gurin rabawa. Dama hakima ta gaje gidan gaba, ita muka soma saukewa sannan muka wuce gida. Muka yi ta jidar kaya zuwa ciki, har lokacin fuskata daure saboda yanda yayi ta gwasale ni, don kawai na ce ya sayawa Iyayenshi kaya. Ba gidan zai sha ruwa ba yau, don haka ina yin sallah na kwanta sai bacci, ban san lokacin da ya tafi ba ma ni. Sai da ya dawo Asham sannan ya biyo gurina, ya samu ina sallar Asham din nima, ya zauna yana kallona. Na idar na gama addu'a ya taya ni shafawa na dube shi, "Sannu da zuwa." Ya ce, "Yauwa, na zo ne inga ko kin huce, naga yau an yi bacci an share ni." Na ce, "Ai bani fushi da kai Mr Cool." Ya yi murmushi na ce, "To yanzun dai sai na dauko maka ka kai musu." Ya ce, "Sai dai ki zo muje tare, dan kuwa ba za'a sace min gwiwa ni daya ba.Na mike na dauko hijabi zan sa ya ce, "Zo nan." Na zo ya dubeni sama da kasa, "Wai wanna kibar fa? Sama da kasa duk kin cika?" Na shafi kumatunshi na ce, "Ka iya kiwo ne." Na mika mishi ledar dan in bagarar da maganar, "Ga wannan mu je." Ni kaina na san cewa na yi kiba, cikina a kirji da hips ya tsaya, marata ba me cewa ina da cikin wata biyar da 'yan kwanaki. Duk a falo muka same su suna kallon Tafsir din Sheikh Amin Daurawa, na zube na gaishe da Daada da Abba, Ummi da murna ta hawo jikina, Daada na mata fada da fillanci. Rukayya ta tabe baki ta gaisheni a dakile. Abba ya ce, "Daga gida ku ke?" Na ce, Eh! Ya ce, "To sai ki basu." Na ciro ledar Daada na yunkura naje gabanta na ce, "Gashi in ji shi." Dama bana iya kiran sunanshi a gaban Iyayenshi. Ta ce, "Me muka samu?" Na ce, "Kayan sallah ne ba yawa." Na mika ma Ummi da na Rukayya sai suka hau murna, Rukayya ta daga kai ta ce, "Hamma ya aka yi kasan kalolin da muke so? Ni komai ja Ummi komai pink." Ya kalleni, Daada ma sai murna take yi tana fadin, "Allah ya shi maka albarka ya baka zuri'a ta gari wadanda suma zasu fita hakkinka." Ya dube ni na kauda kai ina fadin, "Amin Daada." Na mika ma Abba nashi wanda ke kallonmu yana dariya tare da fadin, "Masha Allah." Ya ce, "Har da ni? Ikon Allah Abubakar an yi hankali." Muka sa dariya. Bayan an nutsu ya ce, "Wato Hamma abin da yasa kaji na ce ashe kayi hankali shi ne, ka sani duk kudinmu muna da hakki a kanka, kuma na gode Allah ya kara budi." Muka ce Amin. Ya ce, "Ni fa da har ba zan sai muku ba naga kuna saidawa." Daada ta ce, "Don muna saidawa shi kenan bazaka fita hakkinmu ba?" Ya kalle ni, nayi maza na kauda kai don bana son ya ce nice. Abba ya ce, "Bari Usman ya zo ya kai ma telana su, don da su zan je Idi in Allah yasa mun kai lokacin." Haka suka yi ta shi mishi albarka, tare da yi masa fatan samun zuri'a tagari. Da zamu tafi Rukayya har mota, Rukayya ta ce, "Hamma Allah ya kawo mana 'yan biyu lafiya..." Muka ce Amin. Har lokacin wani gani-gani take min suka juya. Ko nisa ba suyi ba ya wani kankame ni ya rungumeni ya ce, "Na gode D Only, na gode da sani a hanya da kika yi, ni a zatona tunda iyayena suna dashi fiye da ni ba sai nayi musu wata hidima na sai dai in ma danginsu marasa shi daga ciki." Na ce, "Ko sune suke kera kudi wajibi ne ka basu hakkinsu, yi musu biyayya na san kana yi, yi musu alheri kai har abinci ya kamata ace duk wata kana sai musu ko buhu dai-dai ne." Ya ce, "Zan soma daga wannan watan Insha Allah, kai yau naji dadi ashe haka mutum ke samun farin ciki in ya faranta ma Iyayenshi?" Na ce, "Sosai ma kuwa.Ya ce, "Na gode Allah da ya bani mace ta gari, yanzun fada min bayan su ko akwai wadanda ya dace in sai ma kayan Sallar?" Na ce, "Su Lamido da duk kanne da yayin Babanka, ka sai musu kowa wanda ya dace da shi zasu ji dadi."ya ce, "To gobe zamu koma kasuwa kenan." Haka ya kaini gida yana ta shi min albarka, sannan ya tafi gidan Fadima ya kwana. Washegari mun shiga kasuwa harda list din mutanen don kada a manta, lallai kudi sun mutu a ranar, alheri sai bawa ya dage, amma in kayi dadi ka ke ji, shi kuma wanda ka wa yana jin dadi. Ya ce, "To wanene zai kai musu?" Na ce, "Ka samu Hashim ka ware rana kayi ta kai musu." Da suka dawo kuwa Hashim sai labarin yanda Iyayen suka yi ta murna da godiya ya ce Abbanshi, Sarki kenan, har gori ya mishi ya ce, "Hashim kalubalenka, sai ayi koyi da Hamma." Na yi murmushi, na san kowa zai yaba don kaya ne na alfarma da takalma da hula. Hashim ya ce, "Allah ya nufe ni nima." Ranar ma godiya yayi ta min, su Lamido ma suna ta shi masa albarka, wanda ma baya nan in ya dawo gida ya gani sai ya kira waya yana sa albarka. Allah kasa mu dace amin. Saura sati biyu Sallah Abubakar ya ce min yana son ni da shi mu tafi Umara, don haka ma in tashi muje inyi fasfot. Na ce, "A'a da Fadi ya dace kuje." Ya ce, "Ba zata iya zuwa ba." Na ce, "Ina tsoron abin da zai ja min bakin jini cikin zuri'arku, amma ka je ka shawarci Daada." Ya ce, "Shi kenan" Ko da ya samu Daada da batun sai ta ce mishi ya bari mun je aikin Hajji dukkanmu, kada ya zama abin tsegumi ace ya kai bare, amma Hajji kafin lokacin ta haihu. Ya dawo ya ce min bakinku yazo daya da Daada. Na ce, "Ka gani ko? In kaje ka samu a addu'a." Ya ce, "Wannab ba sai kin roka ba. Ni dai na so inje da ke ne saboda mu dan shakata." Na ce, "Wata rana zamu shakata. Koda yanzun ma ai mun sha iska." Ya yi 'yar dariya.da xai tafi ya bar ma kowa komai, na ce xan je kaduna da salla, ya ce a'a in bari ya dawo ma je tare na ce to.su Ummina sun xo min da salla har da Yaya Umar, nayi murna sosai kwanansu 2 suka tafi da Shadad, na ce su bar min Ummi in xamu xo sai mu xo da ita. Bayan sallah da kwana 3 xaya dawo,nasan kuma gidana xaya sauka, domin yana fada min irin yadda yayi missing dina,ko na ce muka yi missing din juna.Tun safe na soma shirya masa girki kala-kala da abin sha, jus nayi mas kusan kala 3 n akuma hada nawa hadin mai kyau nayi ta sha tun safe.misalin 3 ina tsaye gaban madubi nayi adona ckn 1 daga ckn atamfofin daya siya min,sam banji shigowarsa ba,sai dai ji nayi an rungeme ni ta baya kamshin turarensa yasa na gane mijina ne.da sauri na juyo muka makale juna cikn murna, ya sumbaci lebunana, sannan ya ce bari mu isa gidan Fadi, sai in dawo. In na xauna ba xan iya tafiya ba.xamu wuce ne da Hashim daya dauko ni naga ba xan iya wucewa ban ganki ba,na ce to in ka san ba xa ka dawo ba to ka wuce da abinci.Cikin marairaita nayi maganar,ya shafi kumatuna. kada ki damu d only yanxun xan dawo naji gidan na kamshi na ce to "Da sauri ya shige mota suka tafi.kafin ya dawo na kara gyara gidan, na canza kaya doguwar rigar leshi nasa mai kalar sky blue, su hudu suka shigo duk da Hashim.na jera musu abinci da na sha, in adaga daki ina jiyo su suna santi.Hashim ya ce, Hamma gaskiya xan kullo ma Hafsat kawance da Shatu, ina son taxo ta koyi kalolin girkin nan, Dayan ya ce na riga ka a xuci ka riga ni a baki, shi ko dayn ba shi da mata, cewa yayi xaya kawo budurwanchi ta yi hadda.shi kuma Abubakar sai murna da cika baki. fadi ya ke "Matata yar baiwa ce, duk abubuwanta cikin ilimi ne da daraja girkin Hafsat daban ce.Amma fa ba xa ku takura min mata ba, da Ummi taxo tana kwashe kayan bayan sun gama,Hashim ya ce ko dai xan tsaya nan ne Hamma ka tsaya min a bani wannan in kiwatat?Abubakar ya ce "Katon banxa wa xai baka?suka sa daria.Misalin karfe tara saura muna ta shirin kwanciya, Fadi ta kira shi ya daga ta ce"sweet hrt ba nan ka ke ba?ya ce "In ji wa?ta ce Eh!! mana yi lassafi.Ni dai wlhy