Sashe 7
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 4-03 Posted by ANaM Dorayi on 06:39 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ki yi bacci mai dadi tare da yin mafarkina." Na ce, "Kullum cikin yin mafarkina ni ke, ina sonka sosai." Na kashe wayar don jin nauyin furucina, na dauki filo na rungume na lumshe ido ina tuno fuskarshi. Shima a nashe gefen ma filon ya manna a kirji yana jin dadi. Nan take kuma sai wata zuciyar ta ce masa, "Yanzu kai saboda yarinyar da ta tabbatar maka da cewa ita karuwa ce ka ke wannan?" Nan take kuma sai ya saki tsaki tare da yin jifa da filon, zuciyarshi ta ci gaba da wassafo mishi cewa, "Ba wani son da take maka, wanda take so shi daya ne, tunda har ta bashi kanta. Kila ma da zai dawo yanzun da ta nemi ka barta ta koma gurinshi." Take ya nemi farin cikinsa ya rasa. Lokuta da dama wannan tunanin ke sa shi jin haushin Hafsah....... A zato na zai shigo da wuri, don haka na shirya masa abin kari, sai ga sakon shi ya shigo, "Madam ki yi hakuri, kila ki zaci zan shigo, zan duba ma Dada wasu daga cikin (super market) dinta. Idan mun gama da wuri zan zo da wuri, in bamu gama ba ki dubi hanyata da rana. Ina fata kina cikin koshin lafiya?" Lallai Abubakar zai cika alkawarinsa na kula da ni, to nima Insha Allah zan kula da shi. Na bashi amsa da cewa, "Lafiya lau (Hayate) rayuwata, Allah ya sa ka gama abubuwan da zaka yi lafiya, ya kawo min kai cikin kwanciyar hankali.".. Duk da cewa har Abubakar ya bar Kano babu wata mu'amala ta auratayya da ta hada mu, ban damu ba saboda ya nuna kulawarsa gare ni. Ya bani kudi, ya canza min waya zuwa (BB), ya kara min abinci. Haka nan ko da ya tafi ya kan kira ni sau 3 a kullum, nima kullum na ke kiran Mahaifanshi da safe in gaishe su, haka nan Lamido da Matanshi kullum sai na kira su cikin girmamawa na gaishe su har muka kammala Jarabawa. Lokacin yayi tafiya zuwa India akan harkokinsa, na ce mishi, "Tunda muna hutu har da Shadad ina son inje Kaduna da Funtuwa da Malumfashi." Ya ce shi kam bai yarda in je Kaduna ba, amma in je Funtuwa gurin Inna in kwana 2, Malumfashi kwana 2. Sagir zai sani jirgi in wuce Yola. Na ce masa, "To na gode." Don na lura baya son gayya. Washegari Sagir ya zo ya bani kudi dubu talatin, wai inyi tsaraba in ji mijina. Na yi godiya shima na tura masa da sakon godiya, sannan na ce, "Ko zan iya zuwa kasuwa mu yo musu tsaraba?" Ya ce, "Ki je amma ga sharudda na, ki saka katon hijabi, sannan ki kausasa murya yayin cinikayya da maza." Dariya sosai na yi, sannan na tura masa cewa, "Zan kiyaye Insha Allahu." Innarmu ta yi murna sosai da ganina, mun yi hira sosai mijinta da 'Ya'yanshi ma sun nuna jin dadinsu da zuwana tamkar sun sanni. Na bata tsarabar ta, kwanana biyu na wuce Malumfashi, daga can na dawo Kano. Sagir da Rahma suka sani a jirgi sai Yola. Hashim ne na samu yana jirana ni da Shadad, masu aiki ne suka taya ni gyaran sashen. Daga nan na fitar ma da 'yan gida tsarabarsu. Washegari da muka yi waya na ce masa, "Zan je gidan su Dada." Suma na kai musu tsarabar su Sabulai, turarurruka da 'yan kunnaye. Ummi kuma na sai mata wata doguwar riga mai kyau, tayi ta tsalle tana rungumeni, Rukayya kam sai fushi da harare-harare. Ban so jikina ba na amshi Dada da girki, dama ita da Rukayya ne, da kyar ta barni, Rukayya na ganin Daada ta fita itama sai ta bita, ta ce, "Koma mana ku gama." Ta ce, "Toh!" Da ta dawo sai ta samu guri tayi zamanta tana latse-latsen wayarta. Ummi ta shigo, "Aunty yaronki yayi bacci." Na ce to. Ta ga ina yanka albasa ta amsa. Shinkafa ce fara da miya, kuma ba mai yawa bace tunda basu da yawa a gidan, nan da nan muka kammala. Lallai girki hannu ne ba cika kayan miya ba ne, to duk abin da suke sawa suka bani amma sai gashi suna ta santi, illa Rukayya da takici wai ita sai dai ta dafa Indomie. Daada kuma ta ce bata isa ba. Na kai har bayan la'asar sannan na shirya muka koma. Daada da Abba sunata shimin albarka. Ai hutun nan na saki jiki cikin dangin mijina don jan su nake jikina, na kuma saki hannuna, kyauta tana sa dangin miji su soka.Wata rana matar wani wansu ta haihu,ya kaira ni na fada mishi, yace duk abin da ya faru nan ckn danginsa to inje.ummi ce taxo muka je barka,ranar suna ma ita ce taxo kafin na shirya na bata kudi ta siyo min kayan baby na hada da turmin xani na shirya muka je.Mai jego tana ta godia,duk wanda yaxo sai a ce ga kayan barka da Amaryar hamma ta nbata,sai godiay ake min.can muna shirin tafia sai ga Fadima ta shigo cikin isa da jin kai,da muka hada ido sai na fadada fara'ata,duk da cewa gabana ya fadi.Itama nata gaban ya fad, in anyi la'akari da aynda nan da nan ta canxa.ta zauna can kusa da yan'uwansu,huk da haka na bita na gaisheta,da kyar ta amsa ba tare da ta kalle ni ba kuma ciki-ciki.Sai yatsina taka tana harare-harare,ni dai sai mana mike nayi musu sallama na fita na kira Ummi muka tafi.Duk wata kulawa Abubakar yana bani,ko da ya dawo gidana ya sauka,gadona ne kurum baya kwana.Ni kuma ban taba nuna mishi ba,du da cewa hakan yana damuna,hutuna ya kare ya maida ni Kano.Ya siya min gado da sauran abubuwan bukata,ya kuma yimin alkwarin cewa in yaxo xaya dinga koya min mota saboda ya saya min don xuwa mkrtn.duk da cewa karatun nawa karashe ne kowa ya ganni sai yace nayi kyau Wata rana Umar ya kira ni yace jikin Baba ya tashi, yanxu haka suna asibitin Dutse.A rude an kira Abubakar a ways, yace in jira shi yaxo gobe muje, sai nasa masa kuka tare da cewa yayi hkr in je yau.Ina ta rokonshi yace shi dama baya son motar haya ne, amma in tafi in kuma kula da kaina,tare da shadad muka tafi,Baba yana jin jiki,na yi ta kuka su Babasuna ta bani hkr,wai ai jkn ma da sauki.WashegariAbubakar ya iso,nan take ya kira liktansu don suna da asibiti nan kaduna.Cikin awa guda aka canza masa asibiti.Masha Allah, zuwa washegari jiki yayi kyau. ABUBAKAR YA XUBE MIN KUDI MASU dama sannan,ya tafi.baba dasu Baabah sai godia. Na zo na zuna ina tunanin dame xan saka ma Abubakar, abubuwan da yake min? gashi yaki ya bani dama in nuna masa irin dumbin son da nake masa. na fito dga asibitin ina rike da hannu shadad muna jiran mashin don xuwa gidan Umar. Wata dirkekiyar mota ta tsaya gabana, nan nan na hade rai tare da cewa yan'iskan mutane ba dama suga mutum su kyale. kofofin motar suka bude a lkcn guda,sai kawai naga Munnir. nan take wani irin bacin rai ya xiyarce ni. Yace"Hafsy manya" nace cikin ihu kai!kai! mallam kada ka akra kiran sunana. naja hannun shadad muka yi gaba, ya biyo ni. Ki tsaya ina so ne muyi mgnr dana? Cak!na tsaya tare dayi mishi wani mugun kallo."Ba ka da daa gurina, ka fita hanyata in ko ba haka ba xaka hadu da nadama. Na tare dan mashin muka hau ba tare da an fada masa in da xanje ba. Dare muna gidansu baaba sai gashi da Mom dinsa da dadynsa,muna cin abinci da sakina itama taxo tana jiran mijinta xai xo ya dauke ta da mashin... Raina ya baci,suka gaisa da mutan gida. Mom tace "Don Allah Hafsa nake nema, nace gani. Sakina ta bata kujera Ta kure shadad da ido,da kyar na amsa gaisuwar da take min,tace "ikon Allah!! Lallai wannan yaron Munnir ne,kamannin har ya baci."Ta dube ni"yar nan nazo ne mu daidaita, wannan yaron dai jikana ne, "cikn daga murya na ce "Dana ba jikanki ba ne. na fasa kuka nan mutanen gida suka taru nace "ki fitar mana daga gida.na daga waya na kira yaya umar, sai ga shi ban taba ganin fadansa ba irin na ranar.ya ce sun san dansu ne can da ba su xo ba sai yanxu?nan fa itama Mom ta shiga masifa har waje,Munnir wai shi sai ya shigo gidanmu ya dauki dansa. Umar ya ce, shigo mu rusa maka kai, dan iska mara kunya"kai, ranar naga tashin hnkl shi kanshi shadad din ma kuka yake, ganin ina yi.Na kira Abubakar ina kuka na fada masa cewa sun xo wai xasu dauke shadad. Yace "xa suyi me?to kan me?na ce nima ban sani ba, yayi shiru can yace "xan shigo gobe. Washegari ko asibiti na kasa xuwa, sai kusan sha biyu Abubakar ya iso.lkcn kuwa Munnir suna waje tare da Umar,wai ko a ba su yaro ku su kai kara kotu,kuma su dauki lauya.Abubakar ya kalli Munnir tsaf,nan take ya ji ya tsane shi.ko shakka babu wannan shine Baban shadad.Ya ce " kan wane dalili kake son a baka yaro?"yayi mishi wani duba,sannan kai tsaye yace, Dana ne"Abubakar yace "ka taba aurenta ne?ya ce ai kowa yasan cewa budurwata ce a da. Ran abubakar ya sake baci,ya ce"don kawai tana budurwarka a da yanxun sai kazo kce danta naka ne?yace ita tasan komai ai.Umar yace to sai dai in ku ku kai karan mu amma babu wanda xai baku yaro.Abubakar yace ina Hafsat din? Umar yace tana ciki.ya shiga gidan ranshi a bace,ya same ni dakin baabah. Cikin fushi yace"wannan kadan kika gani kin xabi son xuciyarki kin bar tafarkin Allah, dole kiga kaico.Sai ma wani ya sake xuwa yace shima dansa ne tunda kin xama bola mai dibar sharar kowa, ba ki san adadin maxan daki ka bi ba a rayuwarki."Namike tare da fashewa da kuka na ce,"sam ni babu wani namiji dana taba bi a rayuwata, ko shima fyade ya min ai shi ya sani."Ya ce to da bakinki kika sanar dani cewa ke karuwa ce kuma a yawonki ne na karuwanci kika yin