Sashe 5
Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
na aje masa,sannan nace "me xa'a dafa maka?ya dube ni ki barshi.Ban san dalilli ba, sai kurrum naga hawaye sun cika idona, idanuna suna kallon cikin nashi nace in maka fruit?ya cigaba da kallon idona, nima ban dauke nawa idon ba.hawayen idona suna sauka a hnkl.Shadad ya katse mu Anty kiyi mishi fruit Uncle da dadi nima xan sha.yayi yar ajiyar xuciya, sannan ya dauke idonshi daga kaina ya maida gun shadad, yace xaka sha da gaske? Shadad ckn xumudi yace xan sha nayi murmushi kadan sannan ya dauki kofin jus din kunun shinkafar ya kurba.sai naga ya hade rai, ya hadiye jus din da kyar.sannan yace wannan fa?haka yake ba sugar.kinsan bakina yasa ba da xaki.nan da nan sai na tuna ashe sabar sauri ne yasa ni ban saka sugar,lemon tsami ba,don haka sai na saka tare da suga da na zuba masa sai naga ya hau sha. Na kira Shadad na aike shi siyan fanta gidan Maman Yusra. Na yanka abarba, gwanda da kankana, bayan na wanke su na 6are ayaba sai na yanka dabn saboda kada tayi baki, in taji sanyi. Na matsa lemun zaki,shadad ya kawo min fanta mai sanyi na zuba mishi a plate mai zurfi tare da cokali. Sannan na kawo ayabar na zuba,shadad ma na zuba mishi. Nasha mmk, kafin wani lkc ya gama da shi, Sai naji sanyi a zuciyata, farin ciki ya cika ta, dama haka mace ke ji a duk lkcn da mijinta yaci duk wani abu da ta sarrafa? Lallai kuwa zan dinga kirkirar abubuwa don na birge shi dasu. Ya katse min tunani da cewa, Zan iya shiga bayanki? Ina son yin sallah,don bn sami Jumma'a ba. Na dube shi a raunane, Me zai hana? sai dai ko in kana kyama, don namu na talakawa ne. Ya mike ba tare da ya ce kala ba, ya nufi bayina,duk da cewa bayin na gargajiya ne, amma wanke yake tsaf, ba zarni ko karni ko ko wari. Khamshin sabulun wabka ne kawai sai ko na omon wankin bayi. Ya fito yayi alwala. Tuni na shimfida masa darduma, don haka ya tada sallah, ni kuma na fada wanka ko da na zo ya idar. Shadad ya kwaso masa takardun mkrntrsa yana dubuwa, na dire tsakiyar katifa ban cire hijabin ba na murtsuka mai bayan na basu baya. Da zan sa kaya sai na diba na fita waje ya bini da ido har na fita,sai da na saka kayan na zauna kan kujera ina daura dankwali. Na kalli madubi,masha Allah! Nayi kyau, daya ne daga cikin dinkunan da na bawa Rahma na saka, riga ne da siket na leshi mai ruwan dorawa da ratsin baki. Na koma kan katifar ina saka turare, na kalle shi shima ni yake kallo. A duk lkcn da idanunmu suka sarke basa son daukewa daga barin kallon juna. Yanzun haka mun kasa ko kiftawa,shadad ya kalle ni ya kalle shi, sam bamu sani ba, sai dariyarshi muka ji sannan ya ce...Uncel ashe kuma kun iya kallon kuda?" shine yayi saurin janye idanunshi, ya dubi Shadad. Me ka ce? Shadad ya ce, Irin kallon kudan da yaran ajinmu suke yi, wai kada a kyafta ido.. Ni kam lumshe ido nayi, bn so shadad ya katse mu ba, domin ina karanta abubuwa da dama a cikin yalwatattun idanunshi., Jikana a mace naja filo na sulale na kwanta, Jim kadan na jiwo wayata sbd jin shigowar text. Na kalle shi, sbd ganin lambr shi ce mai dauke da sakon,shima ya dan kalle ni sannan ya maida kanshi ga Shadad. Na bude sakon,cewa ya yi "KIN YI KYAU." Murmushi ya su6uce min,dadi mara misltuwa ya rufe ni. A hankali na dago kai na kalle shi, shima ya dan saci kallona, sannan ya dauke kai tamkar ba shi ba. Na dinga kallon kyakkyawar fuskarshi, Shadad na ta krt, bana zaton ma Uncel din yana tare da shi, don waya yake dannanwa. Wani sakon ya shigo wai "KALLON FA NA NAWA NE? na kuma dubn shi, sannan na rubuta cewa. KALLON SO NE.na tura mishi,ya dago muka hada ido. Nayi saurin sunkuyar dakai. Ya mike tare da cewa, "Shadad zo muje." Na dube shi, Ina za ku?" ya ce, Tadi gurin budurwata." Na tsuke fuska,ya ce "Shadad zaka gurin Antyn nan me baka ice ream?" Da gudu yasa takalmi "Za ni Uncel, zata bani da wannan biskt din mai dadi?" Gabana ya fadi, ko dai gaske ne? nayi shiru raina 6ace . Abubakar yayi murmushi mai sauti, cikin jin dadi ya ce Zata baka. Suka fice. Na rasa me ke min dadi, Rahma ta kira ni tana min tsiya,wai miji ya dawo in dai kokarta in shawo kanshi. Cikin yanayin tausayi na ce, "Uhm! Wane shawo kai? Mu2min da ke nemn wani auran? Rahma ta ce, Daina fada min wannan zancen,tsokanarki kawai yake yi, duka-duka yaushe aka yi abin? Amma kada in katse ki, menene dalilin da yasa kika fadi haka?" Na ce, "Tun kafin yace yana sona ina jin shi yana cewa za shi tadi, su fita shi da Shadad. To yau ma yana ce ma Shadad za shi gurin Aunty yaro ya hau murna, har da cewa za'a bashi irin wannan biskit din mai dadi!" Rahma ta ce, "Kika sani ko wata mai sai da kayan kanti ce da suke sayayya yake ce mata AUNTY?" Ta ci gaba, "Ke ko bama haka ba Abubakar ba zai tarki wani aure yamzun ba, kiyi aiki da hankali mana. Kishi ya rufe miki ido, baki ga ko ke baki soma cin amarcin ba?" Na yi murmushi na ce, "Ni ko da har naji haushi." Ta ce, "Don Allah kiyi amfani da matantakarki ki fizgi mijinki." Na ce, "To Rahma duk na kasa gane mishi ne, amma yau da sauki tun da har yaba kwalliyata ya yi." Rahma ta ce, "Ki yi wadda tafi ta kafin ya dawo, ki ajiye duk wani taurin kai ko shariya da jan aji, ki zuba basirarki ki samu ki kwato shi gare ki." Na ce, to na gode. Dambun shinkafa na mishi wanda na cuda shi da nama, karas da kabeji gami da koren wake. Gida ya dime da kamshi, na hada mishi jus din kokumba da abarba da kwakwa, na nike su a blender na tace, na saka kankara da flavour. Bayan na kammala na je na tsala wanka tare da yin Sallar Magriba, nayi shafa, wata jar atamfa (java) na saka mai fulawa blue, na gyare gidan tsaf na yi shimfida a tsakar gida na jera masa, na kunna masa turaren wuta ko ina ya dauki kamshi.Shi da Shadad kawai suke 'yan zantukansu, ko nace yake taya shi shirme. Kusan goma saura ta ce, "To Madam ni zan tafi na kwanta." Muka yi masa rakiya, na yi Sallar Isha'i tare da Shafa'i da wutiri na kwanta, zan soma addu'a sai naji shigowar sako, wanda na zata shine wato Abubakar. Na bude, cewa yayi, "Ban taba cika ciki irin na yau ba, abincinki yayi dadi, zan zo in miki kyauta kuma ina son ki zabi abin da zan baki." Na yi murmushi na lumshe ido, zuciyata tana wassafo burina, na rubuta cewa, "Duk abin da ka zaba min da zaka barni ma sai in ce yaba min din da kayi ma kyaute ce a gurina." Da ya karanta sai ya ji dadin lafazin, don haka sai ya sake rubuto cewa, "In sai miki turare? Ko in canza miki waya? Ko kin fi son in canza miki wani gida kafo mai tsarin zamani? Don lafazinki yasa naji cewa dole ne ma in miki kyauta." Na yi shiru ina nazari, wato Abubakar yana so na dinga nuna kulawa gare shi, in ko haka ne zan yi ta nuna kulawata a gurinsa, sai na rubuta cewa, "Duk wannan basu yi min ba, tunda kace in zaba aba abu daya nake so, ka yarje min in fada?" Da sauri amsarsa ta shigo ya ce, "Eh, fadi." "Son ka da kulawarka kurum nake so, in zan samu sun fi duk wani abu na kawa ko na dadi da zaka bani." Ya yi shiru yana maimaita zantukan, sai kurun na ji kira, na daga tare da yin sallama kasa yanda ko wani na kusa da ni ba zaya ji ba, ya amsa min sallama shima cikin wani sauti mai nuna cewa muryata ta ratsa shi ya ce, "Hafsah!" Cikin wani irin sauti ya kirani, har yatsana naji nima nace, "Sadiq!" Ya ci gaba, "Ni naki ne, sona ke kadai yake naci, kuma zan kula dake, wannan kawai kike so?" Na saki ajiyar zuciya, "Wannan kawai shine burina, na gode." Ya ce, "Nima na gode. Ki yi bacci..........