← Book details Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 22

Sashe 13

Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 4-05 Posted by ANaM Dorayi on 05:17 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Asubanci muka yi tare da su Sagir, Sagir ke tuki shi da Abubakar, ni da Rahma da Shadad muna baya. Sagir na zuba mana hira don shi Abubakar mutum ne bame yawan surutu ba, sai dai mun ta hada ido da shi ta madubi sai ya kashe min ido daya mu yi murmushi, har Rahma ta gane mu ta ce, "Kai ku dai wanna soyayya ko ina sai kun nuna ta?" Na ce, "Kuma ku nuna mana." Kotu ta cika lokacin hankalina na tashe, gani nake shi kenan za'a kwace min da. Bayan gabatarwa Alkali ya bukace mu muka fito ya ce, "Ina yaro?" Aka fito da shi ya ce, "To a musulunce za'a yanke hukunci tunda mu Musulmi ne." Duk muka amince. Alkali ya yanke cewa, "Duk da cewa fyade aka yi mata ta samu ciki, to dan ba dan Sunna ba ne, ma'ana ba ta hanyar aure aka haife shi ba. Don haka in ma ace tayi cikin shege dan nata ne ba a danganta shi da namijin saboda sai da yardarta, don haka wannan ma nata ne, sai dai shawarar da zamu iya bata ita ce ta bawa wannan mutum dan saboda zata fi mutunci, haka nan shi dan ko kuma a ba yaron zabi zai bi Uban nasa shikenan. Sannan hukuncin fyade tunda an ce bai taba aure ba, to za a yi masa bulala dari." Nan fa suka soma kuka, Mom ta zo tana kuka tana rokona wai in basu shi, na ce "Gaskiya ba zan iya bada dana ba." Shi kuma Dad dinsu ya samu alkalin suka kiramu suna ta rokonmu wai tunda gashi shi za'a dake shi, gashi bashi da koshin lafiya. Abubakar ya ce, "In dai yayi hutu za'a ringa kawo shi saboda ya san Ubanshi da danginshi." Suka yi ta godiya muka kame kanmu. Kano muka wuce bayan mun je gidanmu kowa na taya ni murnar cin nasara, daga nan muka koma Kano. Na gama jarabawata ta fita, murna ba a magana yanzun saura service Washegari da gaggawa Abubakar ya zo ya tafi dani Yola. Shadad kuma dama Sagir ya kai shi Kaduna gidan Babanshi suna ta murna. Shi kam da kyar ya lallasu daga kukan da yake sai da Sagir din ya kira ni ya ce in mishi magana. Na ce, "Shadad." Ya ce, "An'am Aunty, ni zan dawo ne ki fada ma Uncle ya dawo da ni." Tausayinshi ya kama ni na ce, "Gidanku ne ai, gidan Babanka da kake ta damuna da zancenshi." Ya ce, "Aunty ban san su ba." Na ce, "Zaka san su kayi hakuri kaji ko?" Ya ce, "To." Munir ya ce ma Mom ta amshi lambata in ya so sai su dinga kira mishi ni. Sagir ya bada lambar sannan ya tafi. Ikon Allah Shadad na ganin gata, tamkar a cinye shi don tarairaya, har an sai mishi waya don ya dinga kirana, ni kam cewa na yi kada su bata min tarbiyyar yaro, saboda su ba su da tarbiyya. Mahaifin Munir ya yiwa Shadad kyautar gidanshi da ke Kabalar road, tunda wai an ce bashi da gadon Ubanshi. Suka bude mishi account ni kam ina can Yola gidan mijina mai sona da gaske. Yau gidan Fadima yake, amma ya kira ni wai zaya zo cin abinci da rana. Na ce, "A'a, sai dai na yarda ka aiko a karba maka, don kada mu shiga hakkinta, Don nima ba zan so amin ba." Ya ce, "To naji." Na yi masa french dish rice serve with grill chicken, sai kuma na masa dan waken rogo da dawa, dama ina da garin, sannan na masa jus din karas, duk san da zanyi girki na kan yi da dan dama saboda mutan gidanmu suna son abinci na. Hakan nan na kan kirkira girki inyi ma Abba da Lamido da kalokin Jus na kan zauna ina kallon tashar girke- girke ina rubutawa na Chanis ko Italia ko Senegal da dai sauransu. Saboda kawai in samo girki wanda ba a saba da shi ba. Fadima ta dube shi, "Ban gane nufinka da amsa abinci gidan Hafsa ba?" Ya dube ta bayan ya dire kofin hannunsa ya cea, "Ta iya girki ga kokarin yi, bata da kuiyar dafa abincin ko kala nawa ne." Ta hade rai, "Ni ban iya ba kenan?" Ya ce, "To ke ko kin iya din ma yaushe kyuya zata bar ki? Ballantana kure girkinki shi ne shinkafa da miya ko taliya. Da zaki daure da kin je kin koyo kafin ta tafi CAMP." Ta harare shi sannan ta ce, "God Forbid in je gurinta koyon girki ka cuce ni, kuma wallahi ba zan yarda ba. A ranar girkina ace abincin ta zaka ci? In an sake kawo min nan zan zubar dashi." Ya ce, "To shi kenan, zan so ki zubar din." Cikin fushi ta shige daki. Duk ranar da yake gidana akwai wasu jus na kankana, Apple, ayaba, madarar ruwa, zuma da kuma garin ridi, in sa kayan itacen a blender in nika in zuba madarar da zumar da kuma garin ridin in sha, in kuma zuba masa ya sha, har dai wata rana ya tambayeni me nake sawa cikin wannan jus din? Don shi kan shi yana jin shi kullum yana kara lafiya da kuzari, yakan kuma ji yanayi daban da in bai sha ba. Na ce 'ya'yan itace ne. Har ma watarana a gabanshi nake hadawa. Wataran kuma in hada rake, zuma, madara peak, garin ridi. Kafin wani lokaci sai gashi na zama Malama ta hada kayan gyaran jiki, in mun yi waya da Rahma in na fada mata wasu sai tayi ta mamaki, na ce, "Dama na fada miki." Abin da yafi bani mamaki, da zan tafi CAMP a Kaduna aka tura ni har da kukan shi da hawaye don damuwa. Shi ya kai ni sannan ya biya ya taho da Shadad ya kai shi gidan Rahma a Kano. zaman sati 2 a camp ko ni na san na yi missing din gwarzon masoya, Abubakar Sadiq. Fadima ta dubi Rukayya, "Kin san Allah ni zan kai karar Hamma gurin Abba, sam baya cin abincina sai na Hafsa. Don gulma har nan zaki ga ta yo ta aiko mishi da shi, kenan ya fada mata cewa ban iya girki ba." Rukayya ta ce, "Ai Hamma ta riga ta gama da shi, ke har su Daada ma in kinji yanda suke yabonta? In ta yo abinci ta kawo ma Abba kiga su Ummi har ma Daada din sai suyi ta yabonta." Ta ce, "To gurin Lamido zanje." Rukayya ta ce, "Kin ji ma inda zaki fi jin dadin kai karanki, kuma zaya ci musu daga shi har ita. Dama ai ba son auren yake ba, kila ma yana kushe auren." Cikin zumudi Fadima ta ce, "Anjuma zan je." Ta shigo gidan da sallamarta suka gaisa da mutan gidan, tsoffin suna mata tsiyar cewa sun kwace miji. Ta shiga gurin Lamido, bayan sun gaisa ta ce dama ta kawo karan Hamma ne. Lamido ya gyara zama ya ce, "Tun kafin aje ko'ina har an soma matsala? To me ya faru?" Ta ce, "Baya cin abincina, ranar da yake gidana sai ya aika nan a karba mishi abinci fa, kuma in nayi magana sai ya ce ta fini iya girki. Shi ne ni na gaji da wannan maganar." Can ya ce, "Shikenan?" Ta ce, "Eh." Ya ce, "To yanzun ina Baban nawa?" Ta ce, "Yana cikin gari." Lamido ya kira shi a waya ya ce ya zo yana nemanshi. Kusan minti 30 sannan ya iso Lamido ya ce masa, "Daga ina?" Bai ji mamakin ganin Fadi ba. Lamido ya karanta mishi laifukan da ta fada, sannan ya tambaye shi ko haka ne? Abubakar ya ce, "Haka ne." Lamido ya ce, "Don me to baka son cin abincin nata?" Abubakar ya ce, "Don bata iya ba, kuma don na amso a gurin Hafsat wadda ta iya bana zaton na yi laifi. Saboda Manzon Rahma (S.A.W) yana amso abinci a gurin Nana Safiyya ya ci in yana dakin kowacce daga cikin matanshi. Don haka ni Sunna na yi." Ta ce, "Amma shi bai yi wulakanci ba." Lamido ya ce, "To naji yanzun dai sai kiyi kokari ki gyara." Abubakar ya ce, "Abin da in riga ta dawo wa kullum sai na fa jira ta ta dawo sannan ta min abincin. Ita kuma Hafsah ko ina zata sai tayi min abincin ta bari in dai tana gari, amma ita wannan sai son jiki." Lamido ya ce, "Ka yi hakuri tashi ka je abinka.Bayan fitar Abubakar Lamido ya ce, "Ke Fadima abin da zan fada miki, kin ga bakuwar yarinyar nan? To ta fiki hankali. Tun yaushe rabonki da gidan nan da sunan ki zo gaishe mu? Ita kuwa ko bata garin nan ta kira mu ta gaishe mu a waya. Girkinmu daban ga girmama mutane, don haka ki nutsu ki zauna lafiya. Ba zan 'kita ba don tana bare, dama ai mugun iri ake tsoro." Fadima dai ta tashi jiki babu kwari ta tafi gida, zuciyarta cike da haushin Hafsah, wato ta zo zata siye dangi? Ta ja wani Uban tsaki. Allah cikin ikonsa mun gama CAMP sai dai Abubakar ya ce zai yi duk yanda zai yi a barni a Yola, ba zan kara nisa da shi ba. Daga baya ma ya ce in na gama bazan yi aiki ba, ni dai ina jin shi ban ce komai ba. Allah ya taimaka da ya shiga ya fita sai ko aka barni a Yola, ni kaina nayi murna don bana son inyi nisa da mijina, Shadad ya dawo Yola shima Abubakar ya canza masa Makaranta mai kyau, duk da cewa Iyayenshi suna ta turo kudi wai na karatunshi. Dad har Yola ya zo kuma ya sanar da abokinshi Mai Martaba Baban su Hashim cewa Shadad jikan shi ne, don haka yaron bai da matsala ko cikin gida, gashi da farin jini. Cikin haka ne FADIMA TA SOMA LAULAYIN NAN, naga rawar kai wurin Abubakar da 'yan uwansa, ganin haka nima na soma zuwa kullum ina dubata, sai ta tsiri cewa wai turarena na sata amai, in daina zuwa. Abubakar ya ce, "Fadima ta ce bata
Chapter 13 · 0% Book details