← Book details Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 22

Sashe 10

Sanadin Boko Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 4-04 Posted by ANaM Dorayi on 05:15 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na soma kukan farin ciki. "Na yafe maka, dama kuma ni ko kusa ban rike ka da komai ba, saboda ba duka namiji ne ne zaiji furucin da nayi ma kaina lakabi da shi ba, sannan ya saurare ni, sai sadauki, jarumi irinka mai taimako don Allah." Na sake kwantar da kaina a kirjinsa, na ce "Nima ka yafe min bata maka ran da nayi." Ya dago fuskata, ya sumbaci goshi na, sannan ya tsurawa kwayar idona nasa idon. "Na yafe maki, sannan ya sake maida ni kirjinsa da wani kalar salon nuna soyayya. Wayar shi ce ta katse ni, sanda muka yi nisa cikin wata duniya muka sake ajiyar zuciya, sannan yasa hannu ya zaro wayar a aljihu. Ni kuma na zauna, zuciyata kuwa farin ciki ne maras misaltuwa. Ya daga wayar, mahaifinshi ne suka yi magana cikin fillanci na tsahon minti goma sannan suka yi sallama. Ya zo ya zauna kusa dani, sannan ya kira Sagir ya bashi labarin yadda shari'a ta kaya, sannan ya ce zama na gaba ya zo da Shadad. Suka yi sallama, ya ce "To mu fa zamu wuce ne, yanzun haka Abba na jira na saboda tafiyar dake gaban mu zuwa Pakistan." Na ce "To ni in zauna a nan?" Ya ce "Kano za ki koma, ki kwantar da hankalinki, In Shaa Allahu za a bi maki hakkinki, domin na kula Alkalin yana da kokarin kamanta gaskiya." Ya ce, "Amma fa ki barshi gurin sagir kada a zo a dauke shi, na ce to" ya soma hada kayan shi ina taya shi har muka gama. Ya rike hannuwana, "Ko in raka ki Kanon ne?" Na ce "A'a, ka ta fi kiran Abba din." Sai da suka kaini gida, ya cika ni da kudi, sannan ya roki Umar da cewa ya kaini gida baya son na shiga motar haya. Su Baba ma yayi masu alkhairi, sannan ya tafi. Abinda yayi wa zuciyata dadi, yanda na samu mutan gida suna tattaunawa akan shari'armu. Wasu sunje kenan ku yau sunji da kunnan su cewa Munir fyade yayi min. Ade ta dube ni, "Hafsat ina maki murna, Allah ya dora ki a kan shi." Na ce "Ai dama gaskiya tana halinta komai daren dadewa. Sannan masu zagina da masu cewa nayo ciki SANADIN BOKO duk na barsu da Allah." Asabe ta ce "Ba a yi haka ba Hafsat, zance na gaskiya ko mu gidan nan ba wanda bai yi da ke ba, sai dai ki yafe mana, Allah ya baki hakuri." Ni dai nayi daki. Na koma Kano naci gaba da zuwa Makaranta, wata uku jal ya rage min in kammala HND dina, tun tafiyar abubakar bamuyi waya ba sai dai text yake turo min. Cewar inyi hakuri wai abubuwa sunyi masa yawa shi yasa, amma zai kira ni ina ranshi. Cikin bacci naji karar wayata da faduwar gaba na tashi, sai da na kalli agogo karfe 2 da minti 40 sannan na dauki wayar na duba sadeek dina na furta a hankali sannan na daga wayar a hankali na furta "Amincin Allah a gareka" ya amsa da cewa " Ameen kema amincin a tare dake, na tashe ki a bacci ko? Nayi rigingine tare da matse filon a kirjina, nace ka isa kayi fiye da hakan" Ina jiyo sautin mumurshinsa ya ce tunaninki ya hana ni bacci,kewar muryarki ta dame ni shi yasa na yanke shawarar kiranki. Na ce Nima kewar ganinka nake yi yaushe za ka dawo? ya ce, da gaske kin kosa ki ganni? na ce um, ai ganinka ya fiye min komai a rayuwa Sadeek dina. Ya numfasa"Me ki ka tanadar min kafin nazo? Me ka ke so mijina? Ya ce, ke kadai nake so. Na sake tausasa murya,Ni taka ce mijina,zan zama mai binka a kowane lkc. Ya ce Na gode Hafsat,zan nuna miki kalar soyayyata,za ki sha mamakina. Na katse shi,"Wace iri ce ka fada min. ya ce a"a sai in nazo za ki ga zahiri,yanzun zan sunbace ki in kin amince. Na ce Bismillah. Sai kawai naji sumbarshi a cikin dodon kunnena har cikin karamin yatsana, ya ce kiyi bacci da mafarkina mai dadi. Na ce ba zan iya ci gaba da bacci ba, zan tashe ne in nuna murnata ga Allah,tare da yin addu'a ya tsare min kai, ya baka duk abn da kaje nema,ya kuma dawo min da kai lfy. Da sauri ya ce, Amin-amn sweet heart . Na ce Wannan Sunan Fadima ne, zan fi so nima kasa min nawa. Ya ce, To shi kenan. Kusan sakon hudu sannan ya ce, ki kashe wayar,na ce kai ne babba kai ya kamata ka kashe,ya ce na gode. Abin tamkar cikin mafarki, wai ni ce matsalolina ke ta kwakkwancewa a hankali. Na tashi cikin farin ciki nayo alwala nazo na zube gabn Ubangijina, addu'o'i nake tare da nuna godiyata ga Allah. Na kuma yi wa mijina shima, Allah ya dawo da shi lfy,ya biya mishi dukkan bukatarshi na alkhairi,tare da dukkan Musulmi baki daya. Ta gidan Rahma na biya na ce Lissafo min abubuwan nan da ki ka ce ya dace in yi amfani dasu. Ta dubi ne, Wane abu kenan? na ce, Na Amare.. -Ta sheke da dariya, sannan ta ce, "Dadina da gobe saurin zuwa, yau ke ce kika zo neman abin da nayi ta binki da shi kina gwasale ni?" Nima 'yar dariya nayi sannan na ce, "Fada min." Na fito da memo da kuma biro daga jakata. Ta ce, "Da gaske ki ke yi? To ai gara kam ki rubuta don ba zan baki hadadde ba, zan fada miki abubuwan da ya kamata ki dinga ci." Na ce to. (Fruits ne ta yi mata listing including Nono, zuma, madarar shanu, nonon rakum, kokumba da gurji) Ta ce, "Kin rubuta?" Na ce, "Eh! Amma zan ta cin su ne haka ko yaya abin ya ke?" Rahma ta ce, "Kina iya cin su ko ki hada wannan da wancan. Na barki kije ki gwada basirarki." Na natsu ina kara kallon abubuwan, sannan na mike tare da cewa, "Bari in tafi kada Shadad ya dawo ya same ni, amma zan baki mamaki. Sai kin zo gurina rokon in fada miki irin nawa sirrin." Ta ce, "Zamu gani." Na tafi ina dariya. Na cema dan adaidaita don Allah ya kaini kasuwa. Ya ce, Ba komai." Duk abin da na rubuta sai da na siyo su. Ta kan kankana na fara na fere bayan na markade ta har 'ya'yanta cikin blender, na dauko kwakwar da na yanka kanana itama na nika, na daka raken da na yanka kanana. Na fidda ruwan shi na hada su guri daya ban ko tace ba na fasa madara peak na zuba zuma na fasa kankara na jefa, ranar shi ne abincin dare na. Da safe kuma ina da garin alkama, na dama shi da madara na zuba zuma, bayan na dama shi ya zama kunu na sha. Da na dawo makaranta na dafa zogale na yanka gurji a ciki kanana, na kwada da kuli na zuba tumatir. Nan na zauna na ci na koshi, sannan na kora da kunun aya da dabino da kwakwa da madara da zuma yayi kauri na sha na yi kat. Da daren ranar kuma farfesun kaza na yi ruwa-ruwa na lankwashe na sha romon sosai. na yi kat, na zauna ina cin apple (Hhhhhh, lallai Hafsa da gaske take yi 'yan uwa, shan romo har da lankwashe kafa? Washegari hadin kazar amare na yi ta tamkar yanda na taba ji. Tun daga ranar ruwan 'ya'yan itace shi ne ruwan sha na, dukkan abubuwan da Rahma ta lissafo min na maidasu abincina, abin sha na. Kafin sati daya ni da kaina na yarda cewa na hadu, kai ina mamakin kaina idan na tuno irin kalaman da nayi ma Abubakar idan ya kira ni. Shi kan shi Abubakar din baya iya daukar awa 3 ba tare da ya kira ni ba, lallai na amince iya yin lafazi mai kyau ga miji yana sa mace ta mallake mijinta, nuna damuwa ga damuwar miji tana sa miji ya kara son ki. Ana gobe za su dawo na shiga kasuwa na yo cefane, duk da bani da tabbacin cewa Kano zai sauka, Na damu ya zo don shirina da nayi ya soma damuna. Ina kwance bayan la'asar na kira layinshi ya daga, cikin sauri ya ce, "D only! Yaya ne?" Na ce, "Hayate don Allah ta nan zaka biyo?" Na yi maganar cikin sigar shagwaba. Ya ce, "Muna tare da Abba yanzun, zan kira ki in mun rabu dashi kin ji?" Na ce, "Toh." Ba'a fi koh minti 10 ba ya sake kirana. "D only kina jina?" Na ce, "Eh!" Ya ce, "Muna tare da Abba ne kin ga ba dama mu rabu ko? Kuma Fadina tana sa ran zuwana." Na ce, "Kai Hayate (cikin shagwaba nake maganar) Ba fa nan ka tashi ba, don Allah ka min adalci in ganka kawai ka wuce, ko ba ka zauna ba." Zai yi magana na ce, "Please Mr Cool, bana jin zan iya kwana 2 ban ganka ba, sorry pls." Sai naji yayi ajiyar zuciya tare da cewa, "To yanzu yaya zan yi da Abba?" Na ce, "Ya san kana da ni fa a Kano, in kace zaka zo ai bana zaton cewa zai yi fada." Ya ce, "Bana son ayi zargin cewa nafi sonki amma zan dan yi dabara in zo din ko ban kwana ba, muka ga juna sai na wuce." Na ce, "To na gode Mr cool. Sai na ganka." Hmm! Ranar da zai dawo ko Makaranta ban je ba, tun safe na ke hada mishi sinasir da miyar alayyahu, simmer fish, meat bolls, meat into potatoe da peppered chicken. Na yi fruit salad na yi coslow, jus din cocumber, sai kuma na yi masa coconut drink. Nan na shiga jera masa duk abubuwan da na tanadar masa. Jus din na soma zuba masa ya sha sannan na bude masa dukkan abubuwan da na girka na ce, "Wanne zan soma zubawa?" Sai da ya hadiyi miyau sannan ya ce, "Kowanne kadan." Tun da ya soma yake fadin, "Alhamdulillah Masha Allah, na yi dace kam." Dadi nake ji tamkar in
Chapter 10 · 0% Book details