← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 17

Sashe 8

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai ya ci-gaba da mita har ya bar parlour'n gaba ɗaya ba tare da ya nemi Abba da Mommy ba, Raudah na ganin ya fita ta miƙe, ta nufi ɗakin ta, zama ta yi a kan bed sai kuma tunanin besty ya faɗo mata a rai, kawar da tunanin ta yi ta hanyar tunawa da nasihar da uncle ya ma ta, ganin kanta na ciwo ne ya sa ta dauƙo magani ta sha, sannan ta ƙwanta, ko a baccin ma babu abinda ta ke yi sai mafarkin Besty, wai gasu a wani lambu mai korayen ganye, tana zaune a saman cinyar shi yana bata hollandia milk a baki sai zuba shagwaba ta ke yi shi kuma yana biye ma ta, suna cikin wannan yanayin ne sai ga Abba da Noor ai kuwa ta ƙwalla ƙara ta farka a gugice ta na share zufa, jin ihun Raudah ya sa Mommy shigowa da gudu cikin ɗakin tun da ta tabbatar Uncle Babangida ya tafi, saboda yana fita ya kira su a waya ya shaida musu yadda su kayi da Raudah'n da kuma roƙar su yafiyar ta, kuma suna gama wayar shima Abba ya koma shago, a guje Mommy ta ƙara so ɗakin, ganin Raudah na zaune a bakin gado tana haɗa zufa ne ya sa ta jingina da jikin Mirror, kallon mamaki Mommy ta ke bin Raudah da shi, a ranta ta ke tunanin ko dai yarinyar nan tana da aljannu ne? Saboda abubuwan da ta ke yi wasu lokutan na bata mamaki ko kuma dai tsabar iskanci ne ohooo, cike da mamaki Mommy ta kalli inda Raudah ta ke zaune, har yanzu bata bar haɗa zufa ba, duk da ta ga shigowar Mommy, sai da Mommy ta gama nazartar ta sannan ta ce

"Wai ke Raudah me yasa kike abu kamar ƙaramar yarinya ne? Ko Arya ba zata yi abinda kike yi ba, ke kenan kullum sai an miki magana? To wallahi ba zan iya ba na gaji da halin ki gwara ma ayi-ayi auren kowa ya huta ki tattara kayan ki ki bamu space ni da mijina ni ma".

Karshen maganar da Mommy ta yi ne ya sa Raudah kallon ta gami da sakin murmushi tana faÉ—in

"Kai Mommy kun gaji da ni kenan?"

Harara Mommy ta galla ma ta, gaba É—aya lamarin na Raudah sai addu'a

"Eh ba dole muyi Allah-Allah ki tafi na ki ɗakin ba, Raudah yanzu kin fara chanza halin ki, tun da ki ka haɗu da wannan ɗan iskan yaron ni ƙaina hakuri na ke yi da ke, Ni dai shawarar da zan baki ita ce gwara ki rufa ma kan ki asiri ki rufa mana mu ma iyayen ki, ki samu ayi auren ki lafiya qlau ba tare da an samu wata matsala ba"

Murmushi Raudah ta yi har da rufe idanu alamar kunya, ganin haka ya sa Mommy girgiza kai kawai ta fita a daƙin tana addu'ar Allah ya raba Raudah da wannan Besty'n, Mommy bedroom ɗin ta ta koma ta fara ninke kayan Arya da almajirin gidan ya wanke.

Mommy na fita Raudah ta tashi, parlour ta fito bata ga kowa ba, hakan ya tabbatar mata da yaran sun tafi madrasah, tunowa ta yi da wayar ta, da sauri ta nufi tsakar gida, a gefe kusa da pampo ta hango jakar ta a yashe a wajan ba zata iya tuna lokacin da ta yar da jakar ba tsabar ƙiɗimewa da ta yi, Allah ya so ta ma ba'a mata dukan da tayi tsammani ba, ai kuwa da Uncle Babangida dukan ta ya yi yau ta san sai an ƙwantar da ita a asibiti dan bata mantawa akwai lokacin da ya daki Sadiya yarinyar shi akan ta yi laifi sai da ta kwana uku a asibiti kafin ta dawo dai-dai.

Nufar wajan da jakar ta ke ta yi, ta da É—auka sannan ta shiga kitchen, dube-dube ta fara yi, wata food flask blue ta buÉ—e É—an ba karamin yunwa ta ke ji ba daurewa kawai ta ke yi, jallof É—in taliya da macroni ta gani, tsaki Raudah ta ja É—an a duniyar nan babu abincin da ta tsana kamar taliya da macroni, rufe abincin ta yi, parlour ta koma, ta zauna a kujera, ganin yunwa ba zata bar ta ba ya sa ta haÉ—a tea.

Wayar ta ta jawo taga twenty missed calls da massages guda biyu, sai da gaban ta ya faɗi, da kyar dai tayi ta maza ta buɗe, ganin Dee ne ya sa ta tura baki gaba ta bude massage ɗin, tambayar ta yake yi tana ina ne? Hankalin shi ya tashi sossai da rashin daga wayar ta, sai da ta gama karantawa sannan ta kunna data, massages ne suka fara shigowa, na besty ne a sama, ya mata massages ya fi goma a WhatsApp, bayan ta buɗe ta gama karantawa sai tayi murmushi mai kayatarwa saboda ko ba komai he really cares kuma ita ma ta san ya zama wani ɓangare na jikin ta, voice note ta mishi, bayan ta labarta mai abinda ya faru ta kara da cewa su rabu kawai tunda ta ma iyayen ta alƙawari kuma gashi sun yanke shawarar auren da ita nan nan da sati biyar, tura mai da voice note din ta yi sannan ta koma gefen status, emoji na kuka ta uploading, tana gama wa ta sauka, cup ɗin da ta sha tea ta ɗauka ta nufi kitchen, wanke-wanke ta hada, da kyar ta iya gamawa, ta na yi tana zumɓura baƙi, har lokacin da ta gama Mommy ba ta fito ba.

Gari na wayewa Fadeelah ta gyara gidan tsaf, suna cikin breakfast da Antyn ta take shaida mata yau za ta je shagon saloon, abin ya ba ma Anty mamaki dan tun da aka saka ta a shagon da zummar ta koyi aiki ba son zuwa ta ke ba, sai Anty tayi ta magana ta ke zuwa shi yasa ta kyale ta taci karen ta ba babbaka tunda ita a rayuwar ta bata san inda ya ke mata ciwo ba,

"Yau kin ga dama za ki je shagon ne"? Anty ta tambaye ta bayan ta gutsuro bread zata saka a baƙi

"Eh Anty jiya ne da daddare nayi tunanin na koma tunda ba wani abun na ke yi a gida ba"

"To Allah ya bada sa'a" cewar Anty, daga haka babu wanda ya ƙara cewa komai har suka gama breakfast, yaran Antyn guda biyu Areef da Areefa Fadeelah ta kai school, bayan ta kaisu ne ta tsaya a hanya ta kira Adnan yana dagawa ta fara kora mai bayani cike da murna

"Haba Bestynah me yasa ka ke wasa da numfashi na"?

Wata iska mai sauti da jan hankali Adnan ya furzar, sai da tsiƙar jikin Fadeelah ta tashi, wani yanayi ta ji ta a ciki mai wuyar musaltuwa, jin ya yi shiru ne ya sa cikin shagwaba ta ƙara faɗin

"Umm ummm wallahi zan maka kuka kaga bana son ina maka magana kana banza da ni, kuma ai na maka text na ce yau za mu haɗu kamar ƙarfe koma, shine kake son daga hankali na ko?"

Tun da ta fara magana har ta gama bai ce mata komai ba sai da ta saka mai kukan gaske sannan ya fara magana

"Am shikenan bana son kukan na hakura shikenan?, Allah ya kaimu ƙarfe goman mu hadu a dai-dai junction din anguwan ku saii na ɗauke ki"

"To shikenan sai mun haɗu" ta na gama faɗar haka ta koma gida, sauran aikace-aikacen ta ƙarasa, tana ganawa ta shiga wanka, duk da gaban ta na faɗuwa amma ya za ta yi? Ba zata iya jure fushin Besty ba, kuma ma tasan ba abinda zai faru tunda shima yana ƙaunar ta, da wannan tunanin hankalin ta ya kwanta har ta gama wanka...

Shirya wa Fadeelah ta yi cikin wata jar after dress yayin da ciki bata saka komai ba daga ita sai pant da bra, bayan ta bi ko wanne lungu da saƙo na jikin ta da turare mai sanyin kamshi, baƙar jaka ta dakko ta saka wayar ta a ciki da yan kuɗaɗen ta sannan ta ɗauko wani bakin flat shoe ta saka, Masha Allah tayi kyau sosai, dan Fadeelah kyakkyawa ce kuma irin dogayen matan nan ne, sai dai ba Siriya ba ce tana da cikar kirji, kallon kanta ta yi a madubi sannan ta fice zuwa ɗakin Anty, guga ta tarar da ita tana yi, zama ta yi a hannun kujera ta ce

"Anty ni zan tafi, sai na dawo"

Tashi Anty tayi zuwa gefen TV stand ta dakko dari biyar ta bata, ta ce

" Ga wannan ki yi kuÉ—in mota kuma ki siya abinci, É—an Allah Fadeelah ki kiyaye bana son na ji wani abu, ki kula da kanki kuma ki tsare mutuncin ki, banda surutun banza da kuma kule-kulen samari, ki gaishe min da Madam Cynthia".

Da to Fadeelah ta amsa ma Anty ta fice da sauri a gidan, tana isa junction ta hango Adnan a tsaye yana waya, yana ganin isowar ta ya yanke wayar, bata nuna mai komai ba ta hau mashin din suka nufi hotel din da suka saba zuwa, dakin da ya kama suka nufa, suna shiga ya É—aga ta chak zuwa toilet ya cire mata kaya, wanka suka yi a tare sannan ya dawo da ita kan gaÉ—o suna rungume da juna, Adnan ya ce

"Fadeelah ba ki san yadda na ke ji a kan ki bane, ke kin san inda bana son ki ma ba zan dinga sha'awar ki ba, to amma bana iya jurewa a duk sanda na gan ki, na kan zauce na rasa tunani na, bana iya samun nutsuwa sai na ji ki a jiki na, dan Allah Fadeelah ki dena mun rowa, mun fa daɗe da zama ɗaya ni da ke" ya ƙarasa maganar yana shafa gashin kanta...
Chapter 8 · 0% Book details