← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

PⒶⒼⒺ 1️⃣5️⃣

(Last page)

Ko da ya iso police station ya ga Fadeelah sai da gabansa ya faÉ—i, shi ya ma manta da ita Wallahi, tana ganin shi ta tashi ta cukume rigarsa tana ihu tana faÉ—in:

" Ka cuce ni Adnan haƙiƙa na ga "SANADIN BESTY" Wannan abin kunyar ina zan kai shi?" Haka dai take ta sambatu da ƙyar aka ɓamɓare ta a jikinsa, bayan DPO ya saurari bayananta ne ya tambayi Adnan shin da gaske ne? Shiru ya yi bai ce komai ba Daddy ya ce:

"Ka yi magana Adnan ba shiru za ka yi ba mutanen nan so suke su ƙulla maka sharri, shirun ka ba mafita ba ne don wallahi muddin sharri suke maka sai na ɗaure su", mahaifin Adnan na ta kumfar baki ya tsinkayi muryar ɗansa yana faɗin:

"Daddy ciki na ne, tabbas Fadeelah budurwa ta ce kafin na yi aure".

"Aure? Aure fa ka ce ?" Fadeelah ta faɗa da ƙarfi saboda kalmar ta razana ta, Adnan ya ci gaba da cewa:
"Gwara na faÉ—a maka gaskiya daddy cikina ne a jikinta ba sharri take yi min ba"
A zabure Daddy ya tashi yana cewa "ko ka sha ƙwaya ne Adnan? Ina kai ina yarinyar nan mai zubin mayu? To wallahi ka dawo cikin hayyacinka don ba a gidana ba", yana gama faɗin haka ya miƙe zai tafi, DPO ne ya tsayar da shi ta hanyar nuna masa illar abin da yake yi gwara a bi komai a hankali kada mutuncinsu ya zube, da haka ya koma ya zauna suka tattauna yadda zasu ɓullo ma lamarin, shi dai Adnan ban da ƙyarma babu abin da jikinsa ya ke yi domin minti talatin Madam Zeenat ta ba shi ga shi an hura awa ɗaya yanzu, yana ta jin vibration ɗin wayarta amma ya kasa ɗagawa, matsaya aka samu a kan cewa zai ɗauki nauyinta har sai ta haihu, kuma duk wani dawainiya shi ne zai yi, godiya mijin Anty ya yi wa DPO suka koma gida, ita kam Fadeelah kuka kawai take yi da nadamar abin da ta aikata , ko a yanzu Adnan ya gama da ita ya ma ta illar da ba za ta taɓa gogewa a jikin ta ba, ta bi son zuciya ai kuwa yau ta tabbatar da "SANADIN BESTY" ta ga babban darasi a rayuwarta.

A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau da daɗi gobe babu har cikin Fareedah ya shiga wata huɗu, ba ƙaramar wahala cikin yake bata ba, ga shi mijin Anty ya koma, tsakanin ta da Anty kam abin ba sauƙi, tana gida babu inda take zuwa kuma tun daga ranar da suka je police station har yau Adnan bai sake zuwa ba, tsananin da ta ke ciki ne ya sa ta fara tunanin hanyar da za ta bi ta zubar da cikin, Google ta shiga ta fara browsing ai kuwa ta ci karo da magani kala-kala ba tare da tayi tunanin komai ba ta rubuta su a wata yar ƙaramar takarda ta ɓoye, tunanin inda za ta samu kuɗi ta yi, can sai ta miƙe tana murmushi ta nufi dakin anty domin ta ji fitar ta daga gidan, purse dinta ta buɗe ta ga kuɗi a ciki dubu biyu ta zara sannan ta fice a gidan, machine ta hau ta tafi wani babban pharmacy ta siyo maganin ta dawo, dama sun saba siyar da illegal magani a wajen shi ya sa ba tare da tunanin komai ba suka bata, gida ta koma ta ƙara duba yadda ta ga an rubuta a wayar yadda za tayi amfani da shi ai kuwa haka ta yi amfani da shi tana mai farin cikin za ta rabu da wahala..

Zaman Zeenat kam da Adnan abin ya ci tura, ba wanda yake iya zuwa gidan domin amarya ta hana, shi kam ya ma zama mijin kan ta ce domin kuwa mugun tsoron ta yake ji, ko ba ta ce ya yi abu ba sai ya yi jikinsa na rawa, sai dai ta tara ƙawayen banza su yi ta shaye shaye har maza suke tarawa a gidan, tun da an mayar da mai gida hoto, Farouk ne ya yanke shawarar zuwa ya ga abokin nasa tunda ko wajen aiki ma ba ya zuwa, ai kuwa zuwa ya yi ya tarar da shi kwance ba lafiya ita kuwa uwar gantali ta fita da ƙawaye ta bar shi jiran gida. Asibiti Farouk ya kai shi, a nan aka ba shi gado sannan aka diɓi jininsa don a yi masa gwaji domin gano me ke damun shi, sai dai gwajin farko likita ya tabbatar wa da Farouk cewa abokinsa na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato (HIV), ƙiris ya rage Farouk bai faɗi a gaban likita ba, haka ya kira Daddyn ya sanar da shi suna asibiti, ko da suka iso shi da mahaifiyar Adnan results ɗin ya basu ba tare da ya ce komai ba, zufa daddy ya shiga sharewa yana maimaita kalmar innalillahi a fili, ɗakin da aka kwantar da Adnan suka shiga yana bacci shi kam bai ma san wainar da ake toya wa ba, zaune suke jugum jugum, can mahaifiyarsa ta ce:

"Farouk ni kam ina Zeenat? Na ga tun da muka zo ban gan ta ba?"

"Mommy wallahi ni ma ko da na je gidan ban tarar da ita ba, shi na samu zazzaɓi ya rufe shi, shi ne na kawo shi asibiti. Ina ganin ta je unguwa ne" Farouk ya ba ta amsa domin shi kam ya san halin da abokinsa yake ciki, kawai ba zai iya faɗa musu ba ne. Haka suka zauna a asibitin cike da damuwa don mahaifiyarsa sai kuka take yi, jira kawai suke ya farka su ji daga gidan uban wa ya kwaso wannan ciwo, ai shi Farouk tun da ya ji wannan maganar hankalinsa ya dawo jikinsa, sai istigfari yake yi yana neman gafarar Allah , shi kam ma aure zai yi kar shima ya jono ma kansa masifa.

Raudah na zaune a gidansu tsawon lokacin nan ba wanda ya ce mata koma gidanki, abin duniya duk ya ishe ta ta rasa makomar aurenta, ko ta kira Noor ba ya É—agawa, kullum sai ta tsine ma Besty a fili da zuciya, ta yi nadama mara adadi ga shi ba ta jin daÉ—in jikinta, komai idan ta ci sai ta yi amai, lura da haka ne ya sa Mommy ta sanar da Abba suka kira wata likita a unguwarsu mai suna DR. Zainab ta gwada ta, ai kuwa gwajin farko ta tabbatar musu da zaman ciki a jikinta, farin ciki a wajen Mommy da Abba ba a magana, nan da nan suka rungumo 'yarsu suna saka mata albarka kuka ta fashe da shi, bayan DR. Zainab ta tafi take ce musu:

"Shikenan Abba Noor ya tsane ni, ga shi ina É—auke da cikinsa, na san ya daina so na, kuma komai daren daÉ—ewa zai rabu da ni" ta faÉ—a tana kuka kamar ranta zai fita , Mommy ce ta buga bayanta tana cewa:

"Ki yi haƙuri Raudah, Noor yana son ki, ya yi hakan ne don ganin kin shiryu kuma mu ma mun ba shi goyon baya don mu ga ko kin hankalta, kuma tabbas kin yi nadama insha'Allah Noor zai zo ya gan ki kuma za ki koma ɗakinki kin ji? Gata muke miki" hannu Mommy ta sa ta share mata hawaye sannan Abba ya fita ya siyo maganin da Dr ta rubuta mata, kunu Mommy ta dama mata ko da ta sha sai ta ba ta magani sannan ta kwanta , nan da nan barci ya yi awon gaba da ita.

Abba ne ya kira Noor ya shaida masa albishir, ai ba shiri ya taho gidan cike da farin ciki, Mommy ce ta ce ya shiga ɗakin Raudah'n don ya sa Mommy a gaba yana ta sunkuyar da kai, ai kamar jira yake yi ya miƙe har da ɗan gudunsa ya shiga, barci ya tarar da ita tana yi , hayewa saman bed ɗin ya yi ya kama kissing ɗin ta, kamar a mafarki Raudah ta ji ana ma ta kiss, tana buɗe ido ta ga Noor nan da nan hawaye suka fara zubo ma ta, harshe ya sa yana lashe mata yana faɗin:
Chapter 16 · 0% Book details