← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 17

Sashe 4

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin ƙarfe takwas da rabi Adnan ya iso kofar gidan su Fadeelah, sauka ya yi a kan mashin ɗin shi, kasancewar layin nasu shiru ne, ba shi da hayaniya sossai, karasa wa ya yi wajan wata barandar da ake kiwon shanu, akwai wani waje ta gefen barandar kamar lungu a inda ake ajiye abincin shanun, wayar shi ya zaro a aljihhu ya kira Fadeelah ya sanar ma ta ya iso.

Bayan minti biyar sai ga Fadeelah ta fito daga gida da wani zumbulelen hijabi, taku taƙe cike da yanga dan dama ita akwai ƙaudi, iyayi, rawar ƙai, uwa uba kuma yanga,
Idanu ya tsira ma ta har sai da ta ce "matsa mana na shiga ƙar wani ya ganni" ai da sauri ya matsa mata ta shige cikin lungun, tana karasa cire hijabin da ke jikin ta, daga ita sai pant da bra, ganin haka ya sanya Adnan sakin murmushi, janyo ta ya yi, ya fara aika mata da sakkoni, sun yi nisa cikin jin dadin su kawai sai ganin hasken wuta suka yi yana nufo wajan da suke da alama za'a shiga wajan abincin shanun ne...

Toh fa reader's, 🤣😂 wannan shi ake kira da dirimm babban motsi!!!

Yau fa ƙaryar Adnan da Fadeelah ta ƙare dan nasan zasu daku a wajan nan...

VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Nα rαѕα dα wαccє írín kαlmα zαnчí αmfαní wαjαn nunα fαrín cíkí nα α gαrє ku mαѕσчα líttαfín ѕαnαdín Bєѕtч, ѕhαrhín ku nα ѕαkα ní níѕhαdí, nα gσdє ѕσѕαí, Allαh чα вαr mu tαrє Bαєѕtíєє'ѕ Dínα🤪

яєѕρє¢т fσя тнσѕє ωнσ ∂єѕєяνє ιт,иσт fσя тнσѕє ωнσ
∂ємαи∂ ιт 💓💓

яυвву✍️

PⒶⒼⒺ 5️⃣

Da sauri Fadeelah ta mayar da hijabin ta jiƙin ta na ƙyarma, gani haka shima Adnan ya rikice, dagan ganin hasken ya kusa ƙaraso wa wajan da suke, yana daga da karyo kwanar lungun wayar shi tayi ringing

Tsaya wa Mallam Sule ya yi yana amsa ƙiran da aka mishi a waya, hakan ya bama Fadeelah damar fita da sauri ta bayan lungun kasancewar aƙwai maɓoya ta baya,

Ganin haka yasa Adnan matsowa daga wajan lungun shima ya dawo dai_dai rumfar shanun, haska shi Baba Sale ya yi ganin yana zufa kamar sabon ɓarawo yasa ya kasa yadda da shi, gaba ɗaya Adnan ya ruɗe da ganin irin kallon da Baba Sale yaƙe mishi.

"Saurayi me ka ke yi a nan? Baba Sale ya tambaye shi

Cikin in ina da rawar murya Adnan ya ce;

"Am im, da da dama amm ina jiran wani ne"

Ƙara haska shi Baba Sale ya yi sannan ya ce " yaro alamun ka sun nuna kamar baka da gaskiya, kodai irin barayin yaran nan ne kai"?

Da sauri Adnan ya girgiza mai ƙai yana faɗin

"A'a Baba wlh ka yadda da ni, ni ba mugu bane wallahi kaji na rantse maka"

Goro Baba Sale ya ɓantara tare da cewa
"Ahaf!! Yoo mugu yana da kama ne? Ai da yana da kama da matsalar tsaro ta ragu a ƙasar mu"

Ganin maganar ba zata ƙare ba ne ya sa Adnan ciro dari biyar a aljihu ya miƙa ma Baba Sale, Yana murmushi ya ce

"Ga wannan ba yawa Baba, a siya goro"

"Chabdi jam!! Niii na karɓi kuɗi a hannun ka? A'a ba haka nake ba, haka kurum ban san ka ba, ban taɓa ganin ka ba, kai ko me kama da ƙai ban taɓa gani ba, ai hakan ba zai yiwu ba" Baba Sale na gama faɗan haka ya shige cikin lungu ɗan dama ya manta bai saƙa ma shanun da yake kiwo abinci band shine ya fito sai kuma babban ɗan shi ya kira shi a waya.

Adnan na ganin shigar Baba Sale lungun ya sauke ajiyar zuciya, bai ko tsaya ƙara neman Fadeelah ba ya yi tafiyar shi.

Noor yana kwance a ɗakin shi da daddare, babu abinda yake yi sai tunanin halayen Raudah, shi dai yasan yana son ta so na haƙika, kuma itama ya tabbatar tana son shi, to amma wannan yaron da yake barazana da farin cikin shi yana kawo masa tsaiko da ruɗani a cikin soyayyar shi da Raudah, dole ne fa ya nemi mafita tun ƙafin dare ya mishi, wata zuciyar ce ta ce mishi;

"Ai kuna yin aure zata dena tunda a lokacin ta zama mallakin ka gaba É—aya, kaga sai yadda kayi da ita"

Da wannan shawara da kwarin gwiwa da ya samu daga zuciyar shi ya saka hankalin shi kwanciya, ya ci-gaba da ayyukan shi a laptop hankali kwance...

Sai da Raudah da Besty suka kwashe wajan awa uku suna chatting tare da alƙawarin za su haɗu washegari a shagon aɓokin shi tela, sannan suka kwanta bacci kowa zuciyar shi cike da farin ciki...

Da safe tun da asuba Raudah ta tashi daga bacci, bata sake koma wa ba, kasancewar yau tasan Mommy na fushi da ita shiyasa ta fara ayyukan gidan da wuri, karfe takwas ta gama komai har Arya da saleem sun tafi school, Abba ya tafi kasuwa, Mommy ce kaÉ—ai ta rage bata fita ba kuma ita ma yanzu take shirin fita.

Mommy na tafiya maƙaranta Raudah ma ta shirya ta fita, dan tun wuri suka tsara haɗuwar su da besty kafin time ɗin da su Mommy za su dawo daga school tasan har ta dawo ta gama abincin rana tunda tasan ko mutuwa za tayi Mommy ba zata barta ta fita yau ba.

A shagon Mansur tela suka haÉ—u, dan Besty ne ya buÉ—e shagon ma, Mansoor É—in bai fito ba, sun shafe wajan awa 4 a shagon ba tare da sun farga ba, hirar su suka sha tamkar kar su rabu, tana duba agogon wayar ta taga É—aya saura, ai da hanzari ta fara saka takalmi, cikin rudewa take fadin

"Na shiga uku na lalace, besty Wallahi nasan Mommy ta dawo kuma zata ga gidan ba kowa" ta karashe zancen tamkar ta fasa kuka,

"Ki kwantar da hankalin ki, insha'Allah ba ta dawo ba, zo muje na nema miƙi kake napep", Besty ya fada tare da kamo hannun ta, a haka suka jera har baƙin titi, hannun su na manne da juna, juyawar da Raudah za tayi ta hango Abba yana nufo wajan su, ai bata san lokacin da ta yi ihu ta hanƙada Besty ba, sannan ta kwasa a guje, ganin ta ruga da gudu shima Besty yabi bayan ta yana gudu tare da kiran sunan ta , ba tare da ya san gudun me take ba, dan shi bai san Abba ba sai a hoto kuma bai gane shi ba yanzu...

Yau za'a sha gudun famfalaƙi, ga Raudah, ga Besty ga kuma Abba 🤣🤣

VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Ku yi hakuri da ni d'an Allah , biki ne ya sha kaina shi ya sa ku ka jini shiru, amma kuna raina a koda yaushe... Luv U oll...

💓💓∂σи'т ωαѕтє уσυя тιмє ωιтн ρєσρℓє ωнσ ѕєєк αттєитισи тнєу αяє נυѕт вσяє∂ ωιтн тнєяє ℓιfє.

✍️
яυвву

PⒶⒼⒺ 6️⃣

Ganin irin gudun da su raudah su ke yi ne ya sa Abba ya koma wajan motar shi, shiga ya yi shima ya tayar a dari ya bar wajan, É—an yana da tabbacin gida Raudah za ta je .

Ganin Raudah ta ƙi dena gudun ne ya sa Besty fara yin ihun a tare_ a tare ɗan duk a na shi tunanin aljannun ta ne su ka tashi, ganin babu wanda ya yi yunkurin tare tan ne ya saka shi neman waje ya zauna ɗan shi dai Allah ya gani ba zai iya gudu da aljannu ba, koma mene ne ya je gidan su kawai.

Abba yana barin wajan gida ya nufa, dama yazo bada sako ne, saukar shi kenan a mota ya ga Raudah da wannan yaron da take cewa ɗan ajin su ne, Abin da ya ƙara mishi takaici shine ganin hannun su manne da juna.

Raudah kam duk nisan wajan nan bata gani ba sai da tayi rabin tafiya, gajiyar da ta yi ne ya sa ta tsugunna a gefen titi tana kuka, wayar ta ce ta ke ta ringing amma ba ta da nutsuwar duba wa balle ta iya É—auka, yanke shawarar koma wa gida ta yi, d'an haka da sauri ta tsayar da me keke napep, da kyar ta iya faÉ—a mai inda zata je.
Chapter 4 · 0% Book details