Sashe 13
Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Satin su uku da aure kullum sai ta yi ma Besty ƙorafin ya ƙi zuwa, yau dai ya yanke shawarar zai zo, bayan ya sanar da ita, murna fal a ranta ta tashi ta hau gyare-gyare da soye-soye, wanda tun da aka kawo ta ba ta taɓa yi ba, bayan ta kammala komai ne ta sakawa gidan turaren wuta ai tuni ya baɗe da ƙamshi, wanka ta yi a gurguje sannan ta shirya cikin wani material, ɗinkin gown ne amma ya mata kyau sosai, ba ta daɗe da zama ba sai ga kiran Dee a wayarta, gate ta je ta buɗe mai kasancewar har yanzu ba su da mai gadi, tun daga wajan gate ta fara zuba mai shagwaba har suka yada zango a parlour'n, bayan ya huta ne ta zuba musu abinci suka fara ci a tare, a dai-dai lokacin ta ji kar'ar buɗe gate, dammm gabanta ya faɗi ta ce
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, na shiga uku Noor ya dawo" gaba ɗaya ta rikice domin zuwan ta da kwana biyu a gidan ya ji tana waya da Besty, ai kuwa ya zaunar da ita ya zana ma ta serious warning, kuma ta masa alƙawarin ba ita ba Dee, wannan dalilin ne ya sa hankalin ta ya tashi saboda ba ta yi tsammanin zai dawo da rana ba tunda sai biyar suke tashi a office .
Shi kam Dee bai ma san tana yi ba kazar shi kawai ya ke ci kamar wani sabon mayunwaci, ci ya ke cike da kwanciyar hankali, cikin siririyar murya Noor ya yi sallama ya buɗe kofar parlour'n ya shigo, kasa ko da ƙwaƙwaran motsi Raudah ta yi jin har ya gama shigowa, bin inda ta ke Noor ya yi da ido ganin ko sallamar tashi ma yau ta kasa amsawa, kallon gafenta ya yi ai bai san lokacin da ya yar da jakar hannun shi ba, ƙarawa ya yi bakin shi na rawa ya ce
"Kai me ya kawo ka gida na wajan matata"? Noor ya tambaya yana nufar inda Dee ya ke, bai tsaya wata-wata ba ya shaƙo wuyan shi yana ci gaba da faɗin:
"Oh ƙawancen naku bai tsaya a waje ba har sai ka biyo ta cikin gidanta na aure? Ko da ya ke ba laifinka ba ne laifinta ne da ta ba ka wannan damar" nufar inda Noor ya ke Raudah ta yi, tana ƙoƙarin cire hannun shi a wuyan Dee da ya shaƙe saboda ta lura Besty'n ma ya kasa magana sai numfashi da ya ke fitarwa sama-sama, tsoron kar ya illata shi ne ya sa ta je ceton shi, ai kuwa tana saka hannu Noor ya wanka mata mari, sannan ya hankaɗa Dee saman kujera ya fara jibgar shi kamar wanda Allah ya aiko, sai ihu ya ke kwararawa sai da hannun Dee ya bada sautin ƙas alamun ya karye kenan, a gigice Raudah ta nufi inda Noor ya ke ganin dukan da ya ke mai kamar baya cikin hayyacin shi, ai kuwa idon shi ya rufe ba ya ji ba ya gani, kamo hannunsa Raudah ta yi tana cewa:
"Yanzu Noor so kake yi ka kashe shi? Haka kawai babu abin da ya maka ka rufe shi da duka? Wannan ai zalinci ne.."
Ai ko kafin ta ƙarasa sai jin duka ta yi, dukan ta ya ke ba ji ba gani yana faɗin:
"Ni ne azzalumin? A kan wannan É—an iskan ki ke kira na da azzalumi? Oh wato bai min komai ba na dake shi? To ki rama mai, na ce ki rama mai"!
A zafafe ya ƙarasa maganar yana ƙara marin na ta, ihu take yi iya ƙarfinta amma ba mai ceto, sai da ya yi mai isar shi sannan ya zauna ya na mayar da numfashi, shi yasa baya so ranshi ya ɓaci saboda bai iya ɓacin rai ba, duk abin da aka mai yana ƙoƙarin danne fushinsa, saboda idan ya yi fushi shi kanshi yana shan wahala, da ƙyar ya iya tashi ya je wajen fridge ya sha ruwa sannan ya dawo ya kwashe su zuwa asibiti....
*** *** ***
Zeenat amarya sai chushe-chushe ake yi, ga wani rashin kunya da ya ke ƙaruwa a kanta, sai rawar kai ta ke yi ita ga amarya, ita da ƙawayenta sun haɗa party a ɓoye, wanda za a fara tun takwas na dare har safiya wanda suke kira (till down), a ɓangaren ango Adnan ma sai rawar kai ya ke yi shi da su Farouk da sauran abokansa, iyayensa kuwa sun saki bakin aljihu sun haɗa lefe na gani na faɗa an kai gidan su Zeenat, iyayen Zeenat irin masu son abin duniyan nan ne kuma ba sa ma Zeenat faɗa, sosai iyayenta suka gwangwaje ta da furniture's na gani na faɗa, sosai suke shirye-shiryen bikin.
Ranar Asabar da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi dubanin jama'a suka shaida ɗaurin auren Adnan da Zeenat a kan sadaki naira dubu ɗari, farin ciki ne kwance a fuskar Adnan, sai dariya ya ke yi domin kuwa yau mafarkin shi ya zama gaskiya, Zeenat ta zama mallakinsa, Allah ne kaɗai ya san yawan son da ya ke wa yarinyar domin tana da nutsuwa da kamun kai abin da ya fi fisgar shi a wajen mace kenan, shi kam ya gama dacewa da mace a duniya.
Ƙarfe biyar na yamma aka raka amarya Zeenat zuwa ɗakin mijinta tare da rakiyar manyan gogaggun ƙarshen ta, sai santin gidan su ke yi tare da ma ta lakca da huɗubar banza wanda ta hau kai ta zauna to dama abu ya haɗu da halinta, ba su bari an rako ango ba suka watse bayan sun ja gefe da wata babbar ƙawar ta ta bata kwalli da wasu ƙwayoyi, daga ita sai cousin's ɗinta aka bari saboda Adnan bai san ta da ƙawaye ba. Basu wani ɓata lokaci ba aka tafi kai ango domin ya matsa musu ayi a raka shi wanda zumuɗin da yake yi sai da ya ƙular da Farouƙ, tsaki kaɗai Farouƙ ɗin ya ke ja yana faɗin:
"Dalla Mallam kar ka dame mu! Ai ba a kanka aka fara aure ba ka zo sai wani rawar kai kake kamar kwaÉ—o".
Cikin haÉ—e gira da jin haushin abin da ya faÉ—a Adnan ya ce:
" Kawai ka ce haushin rashi ne, ko da ya ke yau kai ba sa'a na ba ne, i pass Ur level so I don't have Ur time, ai ban ce dole ka raka ni ba ko?"
Farouk bai sake magana ba ya tashi ya shiga mita sauran abokan suka rufa musu baya, hira suke yi cike da nishadi har suka ƙarasa gidan Adnan, bayan raha da barkwanci a tsakanin su da yan'uwan Zeenat, kuɗi suka basu sannan suka mayar da su gidan iyayen Zeenat ɗin kasancewar a can za su kwana, Adnan na ganin tafiyar su ya rufe get, ya koma ciki, har yanzu Zeenat na zaune a kujerar da ya bar ta, bakinsa ya ƙi rufuwa, cike da jin daɗi ya ke faɗin:
"Amarya ba kya laifi, to ki tashi ki shiga toilet ki canja kaya mana na ga waÉ—annan sun miki nauyi, ni ma bari in je É—akina in shirya kar na takura miki ko?".
Kai ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba shi kuma ya juya ya fice, tana ganin ya fita ta shiga toilet ta gama abin da za ta yi gudu-gudu ta shafa kwallin da ƙawarta ta ba ta sannan ta fesa wani farin abu a gabanta, fitowa ta yi ta ƙara buɗe jakarta ta ciro wani garin magani ta zuba a cikin humra ta jijjiga sannan ta bi kowanne lungu da saƙo na jikin ta da humrar, wasu fingilalun kayan bacci ta saka, komai na jikin ta ana gani sannan ta ɗora hijabi a kai, zama ta yi a bakin gado tana dakon jiran ango Adnan.
Ko da Adnan ya gama abin da zai yi, ɗakin Zeenat ya koma cike da murmushi, a bakin gado ya tarar da ita tana danna waya, cike da kulawa ya ƙarasa gefen ta yana kamo hannunta haɗe da shafa cikin ta yana faɗin:
"Baby babu komai a cikin nan na ki, farin ciki ya hana ki cin abinci ko?" Ya ƙarasa maganar yana lakuce ma ta hanci.