← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko a cikin keken ma babu abinda Raudah ta ke yi sai kuka, shi dai mai keke ya tsaya yana kallon ikon Allah, ganin budurwa santalelliya son kowa ƙin wanda ya rasa, amma ta zauna tana zubar da hawaye, koma me yake damun ki Allah ya yaye miki yan'mata, ya fada a zuciyar shi.
Raudah kam ba ta ma san ya na yi ba, gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta, addu'a ta ke yi Allah ya sa Abba ya koma kasuwa, babban tashin hankalin ta ma Mommy ce, in dai Mommy ta dawo ba ta same ta a gidan ba to ta kaɗe, ɗan yau ta san mai ƙwatar ta a hannun iyayen ta sai Allah, ƙara sautin kukan ta yi, ba ta biyo ta titi ba, sai ta saka mai adaidaitar bi ta saman layin su, hakan ne ya sa bata ga Abba ba, d'an shi har ya zai yi kwanar shiga gida wani abokin shi ya tare shi, akan wata muhimmiyar magana da za su yi, hakan ya sa Abba ya shiga gidan abokin d'an su tattauna, amma gaba ɗaya hankalin shi na kan Raudah.

A dai_dai kofar gidan su, Raudah ta ce mai adaidaitar ya sauke ta, sallamar shi ta yi, duk da gaban ta na dukan tara_tara hakan bai hana ta tunkarar gidan ba kai tsaye, da sanÉ—a ta shiga da saleem ta fara cin karo a bakin pampo ya na wanke hannu, da sauri ta karasa wajan da ya ke ta na tambayar shi

"Saleem, Mommy ta dawo?"

Bai amsa ma ta ba illa É—aga ma ta kai da ya yi alamar eh

"Na shiga uku Saleem, ta riga ku dawowa" Raudah ta ƙara tambayar shi, duk ta bi ta rikice, har yanzu jikin ta bai bar rawa ba, kasa motsi ta yi jin muryar Mommy kamar daga sama ta na faɗin

"Daga gidan uban wa ki ke"
Tsaya wa ta yi, ta gaza furta komai sai rawar jiki, bata iya bama Mommy amsa ba d'an ta san ko giyar wake ta sha ba zata iya ma Mommy ƙarya ba, ganin ta yi shiru ne ya sa Mommy ta fara nufo wajan da ta ke ai da sauri bakin ta ya fara magana

"Mommy kar ki ƙara so wallahi shagon tela na je, kira na ya yi wai bai ga kayan da na kai ba, kuma ban dade da fita a gidan ba",
Ganin Mommy ta ki ce mata uffan ne ya sa ta ci-gaba da rantaɓa bayanai kamar an kunna rediyo kaduna

"Wallahi Mommy kuma da na je sai na samu ya fita,shi ne na kira shi ya ce na jira shi, shi yasa na dade"

Wata uwar tsawa mai sa yan hanji su kaÉ—a Mommy ta ma Raudah

"Dan uban ki ni sa'ar ki ce? Ni za ki kalla ki shirya ma karya Raudah? Tun sha daya da rabi na dawo gidan nan ba kya nan, kuma na kira wayar ki baki daga ba, to tukunna ma a ina Abba'n ku ya ganki?"

Ai tuni Raudah ta ji wani gudawa ya taho ma ta, jin ashe ma daddy ya dawo gidan, to amma ai ba ta ga motar shi s kofar gida ba, ƙila ya ajiye ne a kasuwa ya zo a mashin, ganin gudawar da ta ke rike wa na ƙoƙarin zubo ma ta a wando ne ya sa ta suri butar da ke kusa da Saleem wanda ya tsaya kallon su, ai Raudah ba ta tsaya a ko ina ba sai saman toilet, me Saleem zai yi in ba dariya ba, ana cikin haka sai ga Abba ya shigo gidan, a fusace ya ce ma Mommy

"Mommy'n yara Raudah'n ta dawo kuwa?"

Juyawa Mommy ta yi ta na ma Abba nuni da toilet, sannan ta ce

"Abba ta dawo ina mata magana ta shiga bayi, cemin tayi wai daga shagon tela ta ke", Mommy ta karashe maganar cike da takaici dan ita fa halayen Raudah yanzu sun fara ba ta tsoro".

Abba ya ciro wayar shi yana dannawa, sako ya tura sannan ya dago ya kalli Mommy, ya ce

" Kwarai daga shagon tela ta ke, amma ita da wannan É—an iskan yaron da na raba ta da shi jiya, saboda ta nu na min ban isa ba shine ta je wajan shi har su na rike ma juna hannu"

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!! Alh!! rike hannu fa? To Allah ne kaɗai ya san me yaron nan yake aikatawa da Raudah tunda a idon duniya ma sun iya riƙe ma juna hannu, to wa ya san me suke a ɓoye? Tin da dai ba'a shedar yaran yanzu" kana ganin Mommy ka ga wacce hankalin ta ya tashi, to ba dole ba ace an ga y'ar ka da wani hannun su manne da juna...

Ƙasa hakuri Mommy ta yi, dama Mommy ba sai zuciya ba, dan ba ta iya ɓacin rai ba, hanyar toilet ta nufa a zuciye, cikin ɓacin rai ta fara buga ƙofar, d'an Raudah da ta shiga sakata ta sa ka ta ciki, bugawa Mommy ta ke da ƙarfi tana ce wa

"Ki bude ki fito, yau sai kin faɗa min abinda kuke yi ke da wannan shegen yaron da ku ka ƙasa rabuwa da juna"

Jin Mommy na buga kofa kamar zata balla ne ya ƙara hautsina cikin Raudah, ai kuwa tana gudawar ta kara taho wa kamar pampo, ta na yi tana rusa ihu tare da magiya...

😂😂 Fan's ɗin Raudah yau fa besty ya ja ma mutuniyar ku gudawa, da alama sai Mommy ta ɓalla ƙofar za ta bude, Ni dai na tafi kiran besty mu kai agaji gwanda mu haɗu mu rarrashi Abba da Mommy kar su dakan ma na matar besty....

VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

💓💓ѕмιℓє ιи fяσит σf ρєσρℓє ωнσ нαтє уσυ… υя нαρριиєѕѕ кιℓℓѕ тнєм…

✍️
яυвву

PⒶⒼⒺ 7️⃣

Abba ne ya umarci Mommy da ta bar Raudah ta ƙara sa uzurin ta, tunda ai dole zata fito a bayan gidan komai daɗewa, badan Mommy ta so ba ta shige cikin gida ba tare da ta ce uffan ba. Bin bayan ta Abba ya yi da kallo mai ma'anoni daban_daban, shi dai yana jin daɗin yadda Mommy ta ke tsaye a kan tarbiyyar gidansa, a kullum yana ƙara gode ma Allah da ya ba shi mata ta gari, ba kamar wasu matan ba da za kaga suna goyon bayan ya'yan su idan sun yi laifi, wasu iyayen ma idan an ma yaran su faɗa ko an hukunta su, koda kuwa mahaifin su ne ko yayun su, kai koda wani ne daban sai kaga sun ji haushi ko su nuna ran su bai so ba, wasu marasa hakuri ma sai sun mayar da martani.

Saleem dake tsaye har yanzu shima ya bi Abba da Mommy ciki É—an daga shi sai Arya ne a gidan Mubasheer bai dawo ba, su sai karfe biyu da rabi suke tashi saboda lesson É—in da suke tsayawa yi, tunda a shekarar nan zai zana SSCE.

Dee kam gajiya ya yi da zama a baƙin titi, gashi ya gaji sosai, shi anya ma zai iya zuwa gidan su Raudah yanzu? tashi ya yi jiki a sanyaye ya koma shago da zummar ya kwanta, in yaso zuwa yamma sai ya je gidan su Raudah.

Mahifin Noor na office ya ci karo da sakon Abba'n Raudah, hakan ne ya sa ya yanke shawarar kiran shi a waya, domin maganar ta shi mai muhimmanci ce, amma bai daga ba, ganin ya kira sau biyu bai dauƙa ba yasa ya hakura, ya san idan yaga ƙiran shi zai biyo baya, yanke shawarar kiran Noor ya yi, ringing biyu ya ɗaga wayar

"Assalamu alaikum Baba, Barka da rana"
Daga ɓangaren mahaifin Noor ya amsa cike da jin daɗi, yana son ɗan shi, kasancewar Noor yana da biyayya da sauƙin kai, cikin farin ciki Baba ya ce

"Son kana lafiya?".

"Lafiya lau alhamdulillah Baba, ya aiki?".

"To Alhamdulillah, komai na tafiya yadda ake so, amm...dama saƙo ne naga sirikin ka, ya turo min aƙan maganar bikin ku, to amma dai maganar ba ta waya bace, zan shigo a weekend ɗin nan insha'Allah, kai dai ka kasance cikin shiri".

Duk da Noor bai fahimci maganar ba, sai kawai ya sosa ƙeya tamkar yana gaban Baba, cike da ƙunya ya ce

"Allah ya dawo da kai cikin koshin lafiya da aminci Baba".

Sosai mahaifin Noor ya ji daÉ—in wannan addu'ar da gudan jinin shi ya yi, murmushi ya yi cike da farin ciki ya ke faÉ—in

"Amen Nuradden, Allah ya yi maka albarka, ka gaishe min da yan gidan , ko da yake kafin nan ma zan kira mahaifiyar taka".

"To shikenan Abba".

Noor ya amsa cikin ƙwantar da kai da nuna tsan_tsar biyayya ga Baban shi, ko wannen su ya ajiye waya cike da kewar junan su, ɗan akwai soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin iyalan Alh Mukhtar Baba, kan su a haɗe ya ke.

Nuradden shine ɗan su na fari sai Khadijah dake bin shi, sannan Hauwa'u ɗuk matan suna da aure Noor ne kaɗai ya rage ( shima kuma zai amarce da Raudah'n Besty🤣), mahaifiyar su, Mama Hajara mace ce mai dattako da mutunci, tana mutunta kowa, amma fa bata iya ɓoye soyayyar da take wa yaran ta a ko'ina, bata son Abinda zai taba su, duk da haka ba ta lalata yaran ba, ta basu tarbiyya dai_dai gwargwado, ɗuk gidan Alh Mukhtar Baba kowa yafi son Noor, ko dan kasancewar shi kaɗai ne namiji, shi yasa ake ma bikin shi tanadi na ban mamaki...
Chapter 5 · 0% Book details