← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Haba maman baby kar ki sa baby ya ce na ci zalin mamansa, i am sorry! ko kishi ne ya rufe min ido na yi abin da na yi amma ki yi haƙuri komai ya wuce tashi mu koma gida", ƙoƙarin miƙar da ita yake yi ta noƙe, fita ya yi ya je ya samu Mommy ya ce "umm amm...Mommy zan tafi da ita gida tana buƙatar kulawa", ya faɗa yana sosa kai, murmushi Mommy ta yi tana faɗin Allah ya tsare hanya ga ka ga ta nan, tashi ya yi ya koma ɗakinta ya haɗa mata kayanta da maganin da Dr ta bata suka yi wa Mommy sallama ya mayar da ita gidansa, ai kuwa a ranar ta durzu kuma ta sha gata, ita ma ta zage ta nuna mai soyayya domin ƙara samun matsayi a zuciyarsa, Noor haka ya dinga kiran yan'uwansa yana sanar da su labarin cikin Raudah kowa ya yi farin ciki har mahaifinsa da mahaifiyarsa da kansa ya faɗa musu, addu'a suka musu da fatan Allah ya sauke ta lafiya, haka dai suke rainon cikinsu cike da soyayya da tattalin juna.

A gadon asibiti Fadeelah ta farka, ganin hannunta ana mata ƙarin jini ya sa ta rufe ido tana ƙoƙarin tuno abin da ya faru, ta dai san ta sha magani ta kwanta, can kuma ta ji mararta kamar za ta fashe daga nan ta ƙwalla wata ƙara ba ta sake sanin inda take ba sai yanzu, Anty ce a gefenta tana share hawaye, kamo hannunta Fadeelah ta yi tana faɗin:

"Anty da kin bar ni na mutu, rayuwata ba ta da amfani sam, na cuci kaina, kullum cikin baƙin ciki nake, rayuwata ba ta da wani amfani" ita kan ta Anty kuka take yi sai yanzu ta yi nadamar ƙin
jan ƙanwarta ta a jiki da ba ta yi ba, ga shi nan a garin zubar da cikin ta sha magani ba bisa ƙa'ida ba har ta rasa mahaifarta gaba ɗaya, nasiha mai ratsa jiki Anty ta yi mata tare da nuna ma ta muhimmancin yarda da ƙaddara, sannan daga bisani ta faɗa mata matsalar da zubar da cikin ya ja ma ta, domin ita ma Anty ta shigo kenan daga unguwa ta gan ta kwance cikin jini shi ne ta kwaso ta zuwa asibiti da ƙyar aka tsayar da jinin, Allah Ya yi tana da nisan kwana ne amma da yanzu wani labari ake ba wannan ba, sosai jikin Fadeelah ya ƙara sanyi da lamarin duniya ta san Adnan ya gama da ita ya kuma cuce ta, haka dai ta zauna a asibiti aka yi ta jinya har ta samu sauƙi suka tattara suka koma gida ...

A ɓangaren Adnan kuwa ko da ya farka babu wanda ya iya faɗa masa halin da yake ciki, sai dai mahaifiyarsa ta saka shi a gaba ta yi ta kuka, ya rasa abin da zai ce ma ta, idan ya tambaye ta sai ta ce ba komai, Zeenat neman shi take cike da tashin hankali, don babu wanda ya sanar da ita inda yake ga shi boka ya ce kada ta yarda ya yi nisa da ita na tsawon awa arba'in da huɗu, komai zai iya lalacewa, hankalinta sam baya jikinta, shi kam jin shi yake sakayau, ko da mahaifiyarsa ta tambaye shi ina Zeenat ɓata rai ya yi domin ba ya son jin ko sunanta, sai da ya cika sati ɗaya a asibiti aka sallame shi, Farouk ne mai kwana da shi, direct gidansu aka wuce da shi sannan Daddy ya zaunar da Adnan ya faɗa masa halin da yake ciki, cikin firgici yake kuka da maimaita kalmar innalillahi a bayyane, ihu yake yana cewa Zeenat ta cuce shi, bai tsaya jiran kowa ba ya miƙe ya zari key ɗin motar Daddy da ke gefen kujera ya fice daga gidan a ɗari da talatin, bai tsaya a ko'ina ba sai cikin parlour'n gidansa, ai kuwa ya iske Zeenat da ƙawayenta suna ta rawa kamar yadda ya saba, ido rufe ya yi kanta gadan gadan bayan ya kunce belt din jikin shi, karfe belt ɗin ya samu ya dinga dukan ta da shi har sai da gefen idon ta ya fashe, ihu take amma babu mai taimako domin ƙawayen nata ma tuni sun tsere, sai da ya tabbatar ya mata illa sannan ya rubuta mata saki uku ya cilla ta wajen gidan ya rufe gidan ya yi gaba abin shi ....

A haka dai rayuwa ta gangara abubuwa da dama sun faru ciki har da rasuwar Zeenat wadda ta yi hatsarin mota a yawon bin bokaye don su mayar da ita gidan Adnan, iyayenta sun yi baƙin ciki sosai da mutuwarta, shi kuma Adnan yana nan yana karɓar magani, kuma ya je gidansu Fadeelah ya roƙe ta gafara bayan ya sanar da ita halin da yake ciki, tana kuka ita ma take faɗa mai abin da ya same ta na rasa mahaifa da ta yi gaba ɗaya, yanzu ma wani ɗan maƙocin su Baba Saleh ne zai aure ta a unguwar yake matansa biyu ita ce ta uku, kallon ta Adnan ya yi ya ce:

"Hmmmm lallai Fadeelah SANADIN BESTY bai haifar mana da komai ba sai sharri, har yau ina nadamar kasancewa ta a matsayin Besty domin na san abin da muka shuka a lokacin da muke ƙawance shi muke girba yanzu", a haka dai suka gama hira suka yafi juna ta koma gida...

Bayan wata tara Raudah ta haihu inda ta haifi 'yarta mace santalleliya mai kama da Noor, shagali kam an sha a ranar sunan yarinyar nan, inda SANADIN BESTY FANS suka taka rawar gani a sunan nan, don kuwa shinkafar Noor kam haka suka saka buhu guda a gaba suka cinye, ko da Noor ya gan su a gefe suna harraka abinci harara ya dinga zabga musu, a haka aka yi shagali aka watse inda yarinya ta ci suna Hafsat wato ƙanwar Mamman Noor kenan....

Bayan shekaru goma,
Wani na hango sanye da kakin soja da wata mace a gefensa sun shiga shopping mall, wata yarinya ya gani kyakkyawar gaske tana bin wani yaro da gudu za ta amshi teddy, buge shi yaron ya yi ganin ya buge baban mutum ya saka shi yin rau-rau da idanu yana cewa:

"Sorry uncle, Hafsa ce ta ture ni", murmushi wanda aka kira da uncle ya yi ko kafin ya yi magana ya hango wata hamshakiyar mace a tare da wani babban mutum suna ƙarasowa wajan da suke, kallo ya bi ta da shi ya ce:

"Raudah?" Tana dago kai ta ce "Dee" harara Noor ya zabga musu yana cewa:

"Malama ki zo mu tafi ko?" Hannu Dee ya ba shi suka gaisa cikin wasa da dariya bayan sun gaisa yake tambayar Noor waɗanan yaran fa? Noor ya ce mai yaransu ne macen sunanta Hafsa, namijin kuma Muhammad, albarka ya sanya musu sannan shima ya gabatar musu da Fa'iza yarinyar da ya aura wata uku da suka wuce kuma yanzu two star ne shi a aikin soja, murmushi suka yi, nan take Raudah da fa'iza suka ƙulla zumunci, Dee ne ya biya musu kuɗin siyayyar gaba ɗaya sannan suka fito a tare kowa ya shiga motarsa zuwa inda ya fito...
Anyi bikin Fadeelah da maƙocin su Sani kuma suna zaune lafiya da shi, duk da wani lokacin matansa na mata gorin haihuwa sai dai ta shiga ɗaki ta yi ta kuka, shi ma Adnan ya damu wata mata ya aura a asibitin da ya ke karɓar magani....

Zaman Raudah da Noor kam sai son Barka hankalin iyayenta a kwance, ƙannenta ma duk sun girma, wani lokaci idan suna zaune da Noor sai ta tuno da lokacin da Abba ya biyo ta ta shige bayi ta dinga zawo, sai Raudah ta yi dariya tana faɗin:

"Ai SANADIN BESTY ya so ya raba soyyayya, da mun bi ta BESTY da yanzu Allah bai bamu yaranmu sanyin idaniyarmu ba".

Dee ya ce "ai da kuwa na ga asalin SANADIN BESTY dan ni za a cuta, duk abin da Allah da ManzonSa suka hana to guje mai ya fi wayewar duk na banza ne".

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Allah na gode maka da Ka ba ni ikon kammala wannan littafin, kuskuren da na yi a ciki Allah Ka yafe min, alkhairin da ke ciki Allah Ya sa da ni da ku duk mu amfana..

Waɗanda suka bibiya tun da na fara har na kammala ina godiya a gare ku matuƙa, Allah Ya bar zumunci....

Ina son ku sosai Fan's É—ina

Sai mun haÉ—u da ku a sabon novel É—ina mai suna " SOYAYYATA DA KWAMARET" Kada ku sake a ba ku labari domin nashi salon daban yake ....

✍️
ᏒᎪbᎥ'ᎪᏆu ᎪhmᎪᎠ mu'ᎪᏃu
(ᏒubbᎽ)💙
Chapter 17 · 0% Book details