← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙo a toilet ɗin ma sai da Adnan ya ƙara rage zafi , ganin hankalin shi ya kwanta ne ya sa tayi wanka ta fita daga toilet ɗin ta koma ɗaki, tana cikin sa ƙaya wayar ta dake ƙan bedside ta fara ringing, ganin sunan Anty baro_baro yasa gaban ta dukan tara_tara, ai ba zata iya dagawa ba, sai yanzu ta tuna da aikan da Anty ta ma ta, shine ta biyewa Adnan suka zo hotel,

"Hubbey ka fito Anty nata kira na, kazo ka kaini inda ta aike ni"

Fitowa ya yi yana goge gashin kan shi da towel, ganin ta ya yi a tsaye, matsawa ya yi kusa da ita ya kamo ƙugunta, ƙara narke masa tayi a jiki sai ta juyo ta ƙarbi towel din ta ƙara sa goge mai jikin shi, yana saka kaya ya ɗauki mulkin mashin din shi suka fice a ɗakin.

A kasuwa ya ajiye ta ya wuce shagon shi bayan ya mata alƙawarin dawowa da daddare, da sauri ta shiga kasuwar, da kyar ta samu abinda Anty ta aike ta saboda yamma tayi, wajan ƙarfe biyar ta shiga gida.

Ai kuwa titsiye ta Anty tayi bayan ta haÉ—e rai

"Daga ina kike?"

"Daga ƙasuwa nake Anty"cewar Fadeela muryar ta na rawa

"Kasuwar ubanki!!, Awan ki nawa da fita daga gidan nan? Kin tafi yawon ta zubar ɗin ki ko? Wai Fadeelah me kike so ki mayar da kan ki ne? Ga maneman ki na arziki amma kin ƙi yadda, kin nace ma wannan shegen yaron mai kai kamar saman risho"

Ai kuwa ɓaki na zumɓura jin munanan kalaman da Anty take jifan besty Adnan da shi, wallahi banda yayata ce da yau sai na sumar da ɓakin ta.

Murfin kwanon da ke hannun ta ba tare da na lura ba ta buga min shi, ai kuwa sai da bakina ya fashe , ganin jini na zuba yasa na kwalla ihu tare da barin wajan ina tafiya ina ja mata Allah ya isa, ba baƙin da ya fashe bane ya ba ni haushi, a'a bestynah da ta zaga ne ya ƙona min zuciya, wajan rijiya na nufa na wanke bakina, bayan na gama na shige ɗaki abuna, ummahani yar Anty na gani a cikin ɗakin tana wasa da remote, ai kuwa sai da na mangare ta na ce "shegiya da ido kamar malmo, Allah ya isa dukan da babar ki tamin" ai kuwa ta sa kuka ta fita a ɗakin ganin haka yasa ni ma barin ɗakin kar Anty tazo ta kuma min wata masifar.

Raudah ganin shima Noor bashi da niyyar magana yasa ta kashe wayar, ai kuwa ranshi ya baci,

"Ba komai, zaki shiga hannuna ne" Noor ya fada yana dukan table din office É—in shi.

Ina kashe wayata na saka riga da skirt na wata jar atampha, ban shafa komai ba kasancewar ni fara ce sol kuma ni ba mai ra'ayin kwalliya bace, ko da yake besty ne ya cusa min ra'ayin nan wai shi yafi son ganin fuska na a haka, fita nayi zuwa dakin mom, ganin bata gyara ba yasa na gyara mata sa'annan na share dakin , ai kuwa nasha yabo a wajan ta

"Iyeee!! Yau su Raudah anyi abun kai, chab da alama za'ayi ruwan sama da ƙanƙara, yau kece da gyara dakin nan?" Mommy ta fada cike da mamaki

Murmushi nayi ina wasa da zoben hannuna na ce

"Eh mom ya yi kyau ko?"

"Ah sosai ma Allah ya miki albarka", Mommy ta fada, alamun jin daɗin abinda nayi sun bayyana a fuskar ta ganin ƙamar Raudah ta fara shiryuwa.

Ɗaki na koma na saka gyale na, purse na ɗauka na fice a tsakar gida na iske Mommy na ma ta sallama ɗan zuwa wajan tela, ina fita ƙofar guda na ha motar Noor a waje a hankali na taka har wajan shi ina hu_hura hanci ɗan ban so ganin shi ba,

"Maye", na furta a raina

Cikin ɓacin rai Noor ya ce;

"Raudah me yasa kika kashe min waya"?

A dage nace mai " tambaya kake ko neman sani?

Bai ƙara yin maganar ba, mun kai minti ɗaya a haka, ganin kamar bai da abin fada yasa na ce " kaga malam!! ni ina da wajan zuwa idan kai baka da shi",

"Ina zaki je?" Noor ya tambaye ni, ko kafin na bashi amsa na hango bestyna yasha gayu cikin wasu kananun kaya jeans baƙi da jar riga yana ganin motar Noor ya haɗe girar sama da ƙasa ya samu gefe ta tsaya ya naɗe hannu a kirji yana kallona,

Noor bai ga zuwan Besty ba, ganin ban bashi amsa ba yasa shi faÉ—in

"Ki shiga na kai ki na ce "

"No ka barshi za mu tafi da Dee dina"

Juyawar da Noor zai yi sai ganin Dee ya yi a tsaye yana harar shi, ai kuwa a zuciye ya fito daga motar ya nufi inda yake...

Hahahaha fan's din besty yau fa da alama zai sha É—uka a wajan noor

VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

💓💓вє тнє gιяℓ уσυ ωαит тσ вє 💃 αи∂ иσт тнє gιяℓ тнαт ρєσρℓє ωαитѕ уσυ тσ вє 🙅🏻

✍️
яυвву

PⒶⒼⒺ 3️⃣

Ran Noor a ɓace ya kara sa wajan da Besty yake, ganin haka yasa Raudah tayi saurin bin bayan shi kar yaje ya yi aika_aika, yana isa ya nuna Dee da ɗan yatsa

"Wannan shine warning na ƙarshe da zan maka Kamaludeen, babu kai ba Raudah, ka fita a hanyar ta, tunda ba auren ta za kayi ba,ka bari na zauna lafiya, in kuma ba haka ba wlh!wlh! wlh! Kaji rantsuwa uku ko?za kayi dana sanin sanina!!

A yatsine Besty ya kalle shi, sai kuma ya taɓe baƙi ya ce;

"Lallai Nuradden, kana wasa da lamarin besty, to ga ka ga Raudah nan, ita ya kamata ka kafa ma wannan dokar ba ni ba" ya ƙara sa fada yana dariyar shakiyanci

Tsananin haushi ya sa Noor kasa ce ma sa komai, kawai ya juya ya fisgi mota ya bar wajan, ita kuwa Raudah da ta tsaya kallon ikon Allah bata iya cewa komai ba sai da Noor ya tafi sannan ta juyo ta kalli Besty, dariya ta tuntsure da shi cikin sigar zolaya ta ce

"Kaiii, dama Noor ya zane ka, yau da na sha dariya yadda naga ya zuciyan nan" ta fada tana dariyar kamar wata taɓaɓɓiya, hakan da tayi ba ƙaramin tunzura Besty ya yi ba, kasa ce ma ta komai ya yi a zuciye shima ya bar wajan ya juya ya fara tafiya, ai da wani irin sauri Raudah ta ke bin shi tana mishi magiya da fadin

"Haba better half wasa fa nake maka, so nake kawai na tsokane ka", ganin ya ƙi kulata ne yasa ta fashe da kuka wanda hakan ya sa shi tsayawa chak yana toshe kunne, ƙara haɗe girar sama da ƙasa ya yi kai kace an aiko masa Sarkin garin su ya mutu ne, "To Malama ai sai ki mana shiru ko kada ki cire min doddon kunne", ƙafa ta fara bubbugawa cike da shagwaba take faɗin
" To to ni ba zan dena ihun ba kuma ma .... bai bari ta karasa maganar ba ya kamo hannu ta suka tsallaka titi, da kyar suka samu abin hawa zuwa shagon tela.

Noor yana barin wajan su ya nufi babbar kasuwa, shagon da mahaifin Raudah yake sigar da takalma da yadin maza gami da shadodi ya nufa, a kofar shagon ya ga Abba zaune da abokan shi suna hira, cikin girmamawa da kunya ya tsuguna ya gaishe su , ganin yanayin shi yasa Abba tashi yace su shiga shago

"Nuru me yake damun ka na ganka wani iri, ko baka da lafiya ne?" Abba ya tambaya yana tsare shi da ido

"A'a Abba , kawai na kasa hakuri ne ma shi yasa na ga ba zan iya jira ba har sai nazo na fada maka abinda ya faru yanzu, saboda banji daÉ—in abin ba"

"Subhanallah, Nuru faÉ—a min mene ne ya faru É—an Allah"

"Abba dama ba wani abu bane so nake kawai ka ma Raudah magana akwai wani yaro sunan shi Kamaludeen tana ce masa Dee, to abokin ta ne, sam Abba bana son alaƙarsu kuma nasan da wuya idan kana da masaniyar suna tare, shi yasa nace bari na faɗa maka domin ayi wa tufkar hanci" cewar Noor yana kara russunar da kanshi ƙasa.

Ran Abba ba ƙaramin baci ya yi ba kuma Noor ya kula da hakan , ƙara kwantar da murya ya yi

"Abba ba wani abu bane fa kawai dai magana zaka ma ta" ya fadi haka ne ɗan ya ga Abba ya dauki abin da zafi dama yasan halin Alh Adamu mahaifin Raudah baya ɗaukar raini kuma mutum ne da yaƙe tsaye tsam akan iyalinsa, sa'annan baya magana biyu idan yace eh to eh ne haka idan yace a'a to fa a'a nan ne, shi ya sa mutane su ke ganin girman shi da kimar shi"

Abba ya ce

" Kar ka damu Nuru, ai kai da Raudah duk ɗaya ku ke a wajena, insha'Allah zata gane ƙuskuren ta, kayi hakuri, ina ga ma zan kira mahaifin ka, idan ya shigo ƙarshen satin nan mu zauna a saka ranar auren kawai hankali na zai fi kwanciya"

"To shikenan Abba Allah ya ƙara girma"

"Amen Nuru, Kai kuma Allah ya maka albarka"

"Amen Abba"

Ganin ba wanda ya ƙara cewa komai a cikin su yasa Noor tashi ya ma Abba sallama, ya koma office.
Chapter 2 · 0% Book details