Sashe 15
Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da Besty ya farka ba wanda ya zo ya duba shi sai nurses da ke sintiri, kanshi har yanzu bai daina sara mai ba, ya yi nadamar kasancewar shi Besty, a ranshi yake faɗin "me ma ya kai ni gidanki Raudah? Ga shi nan na ja ma kaina" ganin ya kasa ɗaga hannun shi ne ya duba ya ga hannu a nannaɗe hakan ya tabbatar mai da har karya shi Noor ya yi, nurse ce ta shigo ta ƙara duba shi sannan ta ƙara mai allura, roƙon ta ya yi ta kira mai mahaifiyar shi, bayan ta kira ne ya shaida ma ta yana asibiti, ba shiri ta tashi ta yafa gyale ta taho wajen Dee kasancewar shi ne yaron su ɗaya tal da Allah ya ba su, ko da ta iso ta ga yadda jikin nashi ya yi bayan ya labarta ma ta abin da ya faru faɗa ta hau shi da shi tana faɗin:
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!! Kamaludeeni yaushe ka zama kwarto?" Ta tambaya cike da mamaki, da ƙyar Dee ya iya ɗago idanunsa da suka kumbura saboda yadda kan shi ya ke mai ciwo ya ce:
"Haba Mama kwarto kuma? Kawai ƙawata ce fa shi ne na je na gan ta" ya faɗa yana juyar da kan shi gefe domin ba ma ya son ƙara tunawa, faɗa sosai Mama ta dinga mai kamar ta aro baki sannan ta fita waje ta kira mahaifinsa ta sanar da shi, shima ba shiri ya bar aikin ginin da ya ke yi ya taho asibitin, ko da mahaifiyar Dee ta labarta mai abin da ya faru tashi ya yi ya fice daga ɗakin yana cewa "Allah shi ƙara" tun da shi ya ja wa kan shi.
A haka suka kwashe tsahon kwana uku a asibitin kuma har yau Noor bai shiga ya ga jikin Raudah ba, Abba dai ya duba ta sau biyu amma har yanzu bai ce komai ba, babu wanda ya san tana asibiti a cikin familynsu saboda Abba ya ce wanann labarin ba abin sanarwa ba ne, Mommy na kula da rashin shigan Noor duba Raudah amma ba ta ce mai komai ba, kullum a asibitin yake wuni kuma duk abin da ake buƙata shi yake yi, shima a ɓangaren 'yan gidansu bai sanar da kowa ba, kullum Raudah sai ta yi kuka tana ce ma Mommy dan Allah ta kira ma ta Noor amma ko kallo ba ta ishi Mommy ba sai dai ta bata amsa da cewa "ai ke kika ja ma kanki ba wani ba" .
A zaman da suka yi a asibitin ne mahaifin Raudah suka haÉ—u da mahaifin Dee har suka tattauna sosai, É—an zaman da suka yi har sun saba tare da samar wa da kan su mafita, mahaifiyar Dee ce ma ta lura da shige da ficen su Abba a asibitin shi ne ta tambayi wata nurse, yadda nurse din ta ma ta kwatance cewa tare wani ya kawo su da wata mace hakan ya tabbatar ma ta da ita ce matar da Dee ya je gidanta, shi ya sa ta faÉ—a wa mahaifinsa shi ne ya nemi Abba suka yi magana kuma alhamdulillah domin kuwa sun fahimci juna yadda ya kamata, mahaifin Dee ya so su haÉ—u da, shine Abba ya sanar wa da Noor din amma da ke har yanzu bai huce ba, ya na ganin mahaifin Dee sai ya canza waje .
Ko da aka sallami su Raudah gidansu Abba ya mayar da ita da kan shi, ta ji sauƙi ba laifi, a ranar shi ma Dee mahaifinsa ya ce a sallame su saboda sun gaji da zaman asibitin shi dama karayar da ya yi ne da buguwar da ya yi a kai ba su warke ba wannan kuma sai a hankali, Abba ne ya biya ma Dee kuɗin asibiti saboda Noor ƙin biya ya yi na matarsa kaɗai ya biya ya juya ya bar asibitin, shi kaɗai ya san yadda yake ji a zuciyarsa. Yana son ganin Raudah amma fushin da yake yi da ita ba zai bar shi ya iya ganin ta ba...
Bayan kwana biyu da dawowar su iyayen Dee suka zo tare da Dee gidan domin yin zama na musamman a tsakanin su, da ƙyar Noor ya yarda ya zo don ma yana jin kunyar Abba ne, a babban falon Abba suka zauna, bayan zaman su da kamar minti goma sai ga Raudah ta shigo sanye da farin hijabi har ƙasa, suna haɗa ido da Noor gabanta ya faɗi ganin yadda ya rame sosai kamar ba shi ba, sauke idanunwan ta tayi ƙasa tana tafiya a hankali har ta kai gefen da Noor ya ke ta zauna a ɗan gaba da shi, juyawa ta yi ta hango Dee a ƙasa a gefen ƙafar mahaifin shi dama ta san iyayen shi domin yana saka su a status, kallo ɗaya Noor ya ma ta ya ɗauke kai kamar bai ganta ba, haka kawai sai ya dinga jin haushin ta, Uncle Babangida ne ya buɗe taro da addu'a sannan ya fara da musu nasiha tare da nunar musu yadda addini ya tsara macen da ya kamata ka yi mu'amala da ita da kuma namijin da ya kamata ka yi mu'amala, da haramcin kula wadda ba muharramarka ba da kuma wanda ba muharraminki ba, kuka kawai Raudah take yi saboda jin yadda Allah ya tanadar ma da masu irin halayen ta azaba amma ta biye wa son zuciya, jikin Dee ya mutu murus kuma tun ba yau ba ya yi nadamar abin da ya yi, Abba ne ya katse Uncle Babangida da faɗin:
" Raudah kin ba ni kunya, tun da ki ka taso a gidan nan har kika mallaki hankalin kan ki kin taɓa ganin wani wanda ba ki sani ba ya zo da sunan shi abokin mahaifiyarki ne?"
Girgiza kai Raudah ta yi ba halin magana Abba ya ci-gaba da cewa:
"Ko kin taɓa gani na da wata da sunan ita ɗin ƙawata ce?" Nan ma dai girgiza kai ta yi sannan ya ce:
"Oh to sai ke tsabar shashasha ce ke, ba ki san inda yake miki ciwo ba shi ne za ki biyewa son zuciya da wata shegantaka da sunan wayewa wai Besty ko? To ai gashi nan kina nema ki ɓalle auren ki da hannunki, kuma wallahi wallahi wallahi kin ji rantsuwar musulmi in dai Nuruddeen ya rabu da ke to sai dai wani gidan ba nawa ba". Yana gama faɗar haka ya ja bakinsa ya yi shiru ai Raudah na jin kalmar rabuwa ta ƙara fashewa da kuka ba wanda ya ce mata komai sai da tayi mai isar ta sannan ta yi shiru, mahaifin Dee ya ɗora da faɗin:
" Ni na rasa me zan ce ma wallahi, Alhaji, Hajiya dan Allah kuyi haƙuri dama shi ya sa na ce gwara mu taru mu yi magana ta fahimta, waɗannan yara sam ba su kyauta ba sun yi rashin hankali kuma wannan ba tarbiyyar musulmi ba ne kuma ni wallahi abin da mijin yarinyar nan ya yi ya min daidai domin kuwa ko ni ne zan yi fiye da haka ma" sai ya juya wajen da Dee ya ke ya ce " kai kuma na dawo gare ka mutumin banza mutumin wofi, wallahi wallahi idan baka fita a harkar 'yar mutane ba sai ranka ya ɓaci kai kasan karon mu da kai ai, ba kai ba ita na faɗa maka, ko da wasa na sake jin makamanciyar hakan kai ko ba a kan ta ba ko a kan wata ce na haramta maka zama Besty idan ka ƙi kuwa za ka gane ba ka da wayo".
Share hawaye Dee ya yi sannan ya ce " don Allah don Annabi ku yafe min insha'Allah ba zan sake ba tun daga ranar da abin ya faru na yi nadama kuma insha'Allah ko a kan wata ma ba zan ƙara zama Besty ba domin a "SANADIN BESTY" aka karya min hannuna, hannun da har yanzu ya ki ɗauruwa", ya ƙarasa zancen hawaye na ƙara zubo mishi, rarrafawa ya yi ya je wajen Noor ya roƙe shi gafara a taƙaice, ya amsa mai sannan ya nemi yafiyar Raudah da iyayenta, shi da zama Besty har abada, haka aka musu katangar ƙarfe mai ƙarfi tare da gindaya musu sharuɗa na musamman, sannan ita ma Raudah ta nemi yafiyar iyayen ta da mijinta saboda ta san ta kai su bango tun da har suka iya jure yin fushi da ita, tana hango fushin da Noor ya ke yi a cikin ƙwayar idanunsa amma ya ta iya? Ba ta ankara ba ta ga ba kowa a ɗakin daga ita sai Noor ashe duk sun watse, gefen Noor ta je ta kamo hannunsa tana kuka a lokaci guda ta na cewa:
"Ka yi haƙuri mijina sharrin shaiɗan ne ba zan sake ba, Please forgive me" kallon ta ya yi da rinannnun idanunsa ya ce:
"Why Raudah? Why? Me na miki haka da za ki saka min da wannan? Na dawo gida na na ganku da wani, wani fa Raudah?" Fashewa Raudah ta yi da matsanancin kuka ganin ba zai iya jure saurarar kukan nata ba ya sa shi ficewa daga parlour'n ya bar ta a wajen...
Bayan dawowar mijin Anty da kwana biyu suka tusa Fadeelah a gaba zuwa gidansu Adnan da ke ya taɓa kai ta gidan ta jira shi ya ɗauko abu ya fito, korar kare iyayensa suka musu kasancewar suna da kuɗi sosai, sai a wajen mai gadi suka samu lambar Adnan ɗin da ƙyar, a ƙofar gidan mijin Anty ya mai kira har guda uku amma bai ɗaga ba hakan ya sa suka tafi zuwa police station kai ƙarar Adnan, motar police ɗaya aka haɗo su da shi ta biyo su har gidansu Adnan ɗin aka sanar da mahaifinsa, motar shi ya shiga ya bi su station ɗin yana iƙirarin duk wanda ya ma ɗansa sharri sai ya yi Shari'a da shi, 'yan sandan ne suka ba shi umarnin ya kira Adnan ai kuwa yana liƙe da Zeenat suna ta faman abu ɗaya kiran Daddyn ya shigo da ƙyar ta bari ya fito a gidan bayan ta gindaya mai sharuɗa.....
VOTE
COMMENTS
SHARE
âœï¸
BADAWEEYERH
ðŸ’ðŸ’S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ ðŸ’ðŸ’
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆âœï¸
R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)