← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Raudah ta faɗa da ƙarfi kamar wacce ta ga mutuwa, mamaki ne ya kama Dee ganin reaction ɗin ta, tunanin shi ɗaya dai Allah ya sa aljannun ƙanta basu shiga tsakanin alaqar shi da ita ba saboda shi fa ya rasa gane kanta kwata-kwata dan ko a waya da ta ce mai sun rabu ma kasa yadda ya yi, bai ma bar abin ya darsu a zuciyar shi ba saboda a nashi ganin sharrin aljannun da suka kamata ranar da ta yi wannan gudun ne, duk da ta faɗa mai abinda ya firgita ta yi, amma shi ya fi alaƙanta hakan da aljannu ne ta gani, sai ka ce wanda aka musu farraƙu, kasa ce mata komai ya yi, sai bin ta ya ke da idanu, samun kan shi ya yi da zubewa a ƙasa ya na hawaye, kallon shi Raudah ke yi alamar tausayi da nadamar abinda ta mishi fal ranta, Allah ya so su ma babu mai kallon su ɗan anguwar ba kowa, maza na kasuwa yara kuma na makaranta, dama haka anguwar ta su ta ke ko a weekend's ma anguwar shiru ta ke yi saboda kowa na cikin gida, ganin babu mutane ne ya sa ita ma ta tsugunna ta kamo hannun shi ta fashe da kuka, mai shago ya na cikin shagon shi bai san wainar da ake toyawa a waje ba, shi rediyo ma ya ke ji.

"Raudah me na miki? Me ya sa ki ke barazana da numfashi na? Ko dan kinga na damu da ke ne shi ya sa kike min haka?" Cewar Dee yana ƙara damƙe mata hannu kamar wacce za'a kwace mai ita.

Kuka Raudah ta ke yi wanda ita kanta ba zata iya cewa ga dalilin ta ba, sai dai zuciyar ta na ma ta zafi, tabbas Besty bai cancanci haka daga gare ta ba, ita kanta ta a yan kwanakin nan da basa magana azabtuwa ta ke yi, tunani ta ke yi ma anya zata iya rayuwa ba tare da Dee ba? Kaii da kamar wuya, tsagaita kukan ta yi ta share hawaye tana ƙara kallon shi kuma har a lokacin hannun su na like da juna, Chan kuma kamar an tsigare ta sai ta miƙe ta ce

"Besty an saka auren mu da Noor kamar yadda na faɗa maka kuma Abba ya raba ni da kai, sai dai a wannan karon hakuri na ya ƙare, Nima ba zan iya jurewa ba".

Tana gama faɗar haka ta ƙara jan wani dogon numfashin sannan ci-gaba da faɗin

" Ni ta ka ce, ko da nayi aure ma babu wanda ya isa ya raba ni da kai Dee, ka rubuta ka ajiye, ina tare da kai har ƙarshen numfashi na!!!".

Tana gama faɗar haka ta sake mai hannu ta yi shigewar ta gida tana kuka, murmushin nasara da farin ciki Dee ne ya kuɓce a fuskar Dee, cike da ƙwarin gwiwa shima ya miƙe ya bar wajan...

Tabdijam lallai Raudah kin ɓallo ruwa ni dai babu ruwana idan Abba da uncle Babangida suna miki lugude, Fan's dinki sa kwace ki ah to ni kam na yi nan🏃🏃

VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

PⒶⒼⒺ 1️⃣2️⃣

Ko da Raudah ta shiga gida É—akin Mommy ta nufa, bata gadon kamar yadda ta ganta dazu, dammm gabanta ya faÉ—i

"Kar dai a ce Mommy ta tashi bata ganni ba?" Ta faÉ—a tana zama a kan stool É—in da ke gefen gadon, maganganun Besty ne suke yawo a cikin zuciyar ta, da kuma yanayin da ta ganshi, fuskar shi kaÉ—ai zaka kalla kasan baya hayyacin shi, gaba É—aya tausayi ya bata, ya zama dole su koma kamar yadda suke da, sai su gyara salon su ta yadda babu wanda zai gane suna tare har tayi aure ta bar musu gidan.

Mommy ce ta fito daga toilet, ganin Raudah a zaune ya sa ta É—an dakata bata karaso ba, karantar yanayin da ta ke ciki ta yi, chan kuma sai ta ce

"Raudah lapiya? Tunanin me ki ke yi"?

Firgigit ta dawo cikin hayyacin ta, murmushin dole ta ƙirƙiro, ta ce

"Ah haba Mommy tunanin me zan yi ina da ke", dariya Mommy ta yi koba komai akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin ta da ƴaƴan ta duk da ba ta musu goyon sakalci ba amma dai sun shaƙu sossai, kuma duk wanda ya yi laifi suna hukunta shi dai-dai da laifin shi.

"To ko an fara tunanin rabuwa da mu ne?" Mommy ta tambayi Raudah cike da zolaya

Rau-rau ta yi da idanuwa, kamar zata yi kuka ta ke faÉ—in

"To ni Mommy ki dena cewa za mu rabu, ba kiji yadda gabana ya faÉ—i ba, Allah na ji wani iri" ta karashe maganar cike da shagwaba...

Shiru Mommy ta yi bata kuma cewa komai ba, zama Mommy ta yi a bakin gado ta dauko waya tana dannawa, wayar ta kara a kunne jim kaÉ—an ta fara magana

"Assalamu Alaikum, Hajiya Salimah, fatan kina lapiya"?

Daga chan ɓangaren Hajiya Salimah ta yi murmushi mai sauti sannan ta ce

"Lapiya qlau, Mommy Mubasheer ya gida da yaran?"

"Alhamdulillah, sai dai fa kar ki bari Arya ta ji kina cemin Mommy'n Mubasheer, É—an ta ce ni Mommy'n ta ce ita kaÉ—ai", Mommy ta faÉ—a tana dariya

Hajiya Salimah ma dariyar ta yi sannan ta ce

"Ah ah ai kuwa na tuna kam, na dena faɗa afuwa Mommy'n Arya", su duka biyun dariya suka saka, sai da suka ɗan taɓa barkwanci sannan Mommy ta ce

"Hajiya maganar da na mukayi jiya ne akan bikin Raudah, na ji ki shiru kuma kince da azahar za ki zo har nayi bacci na tashi ban ji ki ba, shine na ce bari na kira ki baeki ko lapiya"?

"Ohhh!!! Na manta ne ban kira ki ba, dama so na ke ayi la'asar sai na zo saboda nima baƙi na yi yanzun nan suka tafi" cewar Hajiya Salimah

"Toh shikenan, Hajiya sai kin zo".

Mommy na gama faÉ—ar hakan ta kashe waya, juyowa ta yi tana kallon Raudah ganin itama ita ta ke kallo ya sa ta ce

"Wai mene ne ki ka saka ni a gaba kina kallo na"?

Ba komai Mommy cewar Raudah, "emmm dama dazu fa'iza ta kira ni wai maganar anko shine na ce ma ta zan kira ta anjima",

Kallon mamaki Mommy ta bi Raudah da shi, rasa me za ta ce ta yi kawai ta mata daƙuwa

"Ungo naki Raudah, na ce ungo na ki, yanzu dani za kiyi maganar ankon ƙawayen ki? Ah lallai kam zamani, sai ki jira idan angon ya zo kuyi maganar tun da ku ta shafa"

Mommy na gama faɗar haka ta fice a ɗakin, tashi Raudah ta yi ta nufi daƙin ta, gado ta haye ta buɗe data, sai gani kawai tayi an saka ta a wani group mai suna "Raudah's bride maid's", murmushi ta yi ɗan ta san wannan aikin fa'iza ne, ai kuwa tana shiga ta duba ta ga duk ƙawayen da take bukata ne a ciki, cousin's ɗin ta kawai ta adding a ciki, sannan suka fara shirye-shiryen yadda biki zai kasance.

Misalin ƙarfe takwas na dare Raudah ta shirya cikin wata maroon color ɗin abaya, stones ne a jikin ta tun daga sama har ƙasa,sai walwali ta ke yi da ɗaukar ido, ba ta yi kwalliya ba domin bata da ra'ayin hakan duk da Noor ya ce ta yi amma fa ita ba zata yi ba, kawai so ya ke ya takura ma ta, head band ta dakko shima maroon ta saka, da ɗan kunne, sai gyalen abayar da ta yafa, maroon ɗin flat shoe ta saka sannan ta fashe jikin ta da turarruka masu ƙamshi, Masha Allah dan ba karamin kyau ta yi ba, kamar ka sace ta ka gudu, fitowa ta yi parlour, a nan ta tarar da Mommy, Arya da saleem, Mubasheer ne kaɗai baya nan, Arya littafi ne a hannun ta, Mommy ma haka, da alama assignment ta ke koya musu ganin ba'a kunna tv ba.

"Mommy bari na je Noor na jira na a waje".

A dawo lapiya Mommy ta ma ta, Arya ce ta ajiye littafin da ke hannun ta, ta je kusa da ita ta na cewa

"Anty zan biki", ba tare da Raudah ta ce komai ba ta kama hannun ta suka fita waje, yana tsaye a jikin motar shi ya saka kaftan Black colour, ba karamin kyau suka mai ba, saboda shima Noor kyakyawa ne, jingina ta yi da jikin motar ita ma tana gaishe shi, amsa wa ya yi ya miƙa ma Arya hannu yana faɗin

"Little zo mana mu gaisa", da sauri Arya ta karasa kusa da shi, hirar su suke ta yi da Arya, hirar ba ta komai ba ce face school, satar kallon Raudah ya yi, yaga tana ta lanƙwasa ƙafa alamun ta gaji, motar ya buɗe ya ciro chocolate ya ba Arya, cike da farin ciki ta ce

"Thank you uncle" tana gama faɗar haka ta shige cikin gida da sauri tana ƙwalawa Saleem kira.

Juyowa ya yi ya kalli Raudah, ba karamin kyau ta mai ba, murmushi mai sauti ya yi, bai ce mata komai ba, kuma a irin yanayin shi ba zai ce ta yi kyau ba, dama ta saba in dai Noor ne, da wuya kayi abu ya yaba, shi yasa ta ke jin daÉ—in Dee komai ya gani ya yi ta koÉ—awa kenan, koda abin bai ma ta kyau ba har sai ta ji ya shiga ranta, gaishe shi ta yi amma sai da ya ja wasu seconds sannan ya amsa, shiru ne ya biyo baya daga bisani ya ce
Chapter 10 · 0% Book details