← Book details Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 17

Sashe 12

Sanadin Besty Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Besty wai me na maka ne ka share ni? Tun ranar da abin nan ya faru sau biyu ka kira ni"? Fadeelah ta faɗa tana fashewa da kuka, shiru ya yi bai ce komai ba, sai da ta yi mai isar ta sannan ya bata haƙuri ya ce idan ta fito ta kira shi za su haɗu, ai kuwa jiki na ɓari ta shirya, Anty tayi ma sallama ta ce ta tafi shago, tana fita ta kira Adnan, nan da nan ya zo ya ɗauke ta zuwa hotel kamar yadda suka saba, wannan ƙaron ma sai da ya ƙara yin sex da ita, sai dai bataji zafi ba kamar na farkon, haƙuri ya bata na rashin kiran ta da bayayi saboda aiki ya mai yawa a yan kwanakin nan, sai yamma ya mayar da ita gida tare da alƙawarin zai zo gobe da daddare.

Washe gari ne Fadeelah ta koma shago gudun kar Anty ta je shagon watarana bata ganta ba ko a ce bata zuwa, dan ta san Anty da bin ƙwaƙwafi, ai kuwa ta sha faɗa a wajan Madam Cynthia, aikin ranar gaba ɗaya ita ta yi shi, sai karfe shida ta koma gida, gaba ɗaya a gajiye ta ke, da kyar ta iya yin sallar magriba ta ci abinci, Adnan ta kira ya tabbatar ma ta da zai zo bayan isha'i, har zata katse wayar ya ce

"Emm Baby yau kar ki saka kaya, hijab kaɗai za ki saka ɗan yau a matse na ke" Adnan ya faɗa har da kashe ido kamar tana gaban shi, da to kawai ta amsa mai sannan ta yanke kiran, tashi tayi ta nufi daƙi ta gabatar da Sallar isha'i, sannan ta saka wasu pant da bra masu kyau da ɗaukar hankali, katon hijab ta saka ta fesa turare a jikin ta.

Misalin takwas da rabi Adnan ya kira ta ya sanar ma ta yana waje, sallama ta ma Anty ta fice, wajan rumfar shanu suka nufa ganin anguwar ba mutane kamar kullum, ciki ta shiga shi kuma ya tsaya ta waje, matsowa ta yi ta É—aga hijabin, ai kuwa yana kyalla ido ya ganta hankalin shi ya tashi, wasanni suka fara yi sai da ya samu nutsuwa da ita ya ma ta sallama ya koma gida, itama gida ta koma cike da farin ciki domin tana son kasancewar su a irin wannan yanayin...

VOTE

COMMENTS

SHARE

✍️
BADAWEEYERH

💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐

L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️

R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)

G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)

M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻

https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐

Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ

Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️

Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ

Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ

Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

PⒶⒼⒺ 1️⃣4️⃣

Yau ya rage saura sati ɗaya bikin Noor da Raudah, kuma a yau ne aka kawo lefen Raudah gidansu, lefe ne na gani na faɗa, sosai Raudah ta ji daɗin kayan domin Noor ya gwangwaje ta, a waya ta kira shi ta mai godiya, ko da ta nuna ma Besty bidiyon kayan ta waya shima ya taya ta farin ciki ga shi dama duk wani kayan da ta ɗinka sai da ta siya ma Besty shadda colour ɗin kayan, wasu kuma ƙananan kaya ta siya mishi saboda ta ce bikin nasu ne.

Ranar Laraba aka yi henna party inda ƙawayen suka saka lifaya bayan an kammala musu lalle ja da baƙi, sosai suka yi kyau cikin lifaya kalar sararin samaniya, ita kuma amarya ta saka baƙa, musamman aka kira Bebeji mai hoto ya zo ya musu hotunan, Masha Allah don duk wanda ya ga hotunan sai ya yaba domin sun yi komai cikin tsari da wayewa, a gidan Anty Salimah suka yi henna party ɗin, tun da Besty ya ga hotunan Raudah ya ke koɗawa cewar tayi kyau, ba abin da ta ke yi illa murmushi da jin daɗi ko ba komai ya wanke mata baƙin cikin Noor domin shi da ta tura masa emojin murmushi kawai ya aiko mata wanda hakan ba ƙaramin baƙanta ranta ya yi ba, washe gari Alhamis su kayi freind's of honour, nan ma amarya da ƙawayenta sun sha kyau har sun gaji, kuma Besty ya halarta, ko da Noor ya ga hotunan su tare da Besty ran shi ba karamin ɓaci ya yi ba amma ya danne a cewar shi kwana nawa ne ta zama mallakinsa.

Ranar Juma'a suka yi kamu a flourish event center, amarya Raudah da angonta Noor sun sha kyau sosai, duk motsin da Noor zai yi sai ya galla ma Besty harara, shi kuma sai ya yi murmushi ya waske, Raudah na kula da yanayinsu amma ba ta ce komai ba, a haka aka saka Raudah a lalle, sai a lokacin ne gabanta ya fara faduwa ganin fa da gaske gobe ne auren, nan da nan jikin ta ya yi sanyi, a haka dai aka yi kamun aka gama amarya ta koma wata shiru-shiru, ai kuwa dangi suka saka ta a gaba da tsokana wai munafurci ne ita dai bata iya cewa komai, sai wata matar abokin Abba ce mai tare ma ta.
Washe gari ya kama Asabar da misalin ƙarfe biyu da rabi dubanin jama'a suka shaida ɗaurin auren Nuradden Mukhtar Baba tare da amaryar sa Raudah Adam a babban masallacin ƙofar fada, a kan sadaki naira dubu ɗari da hamsin, bayan an gama ɗaura auren ne ango ya dinga gaisawa da jama'a yana washe baki kamar wanda aka ma gafara, can na hango Besty shima ya sha shadda blue sai ɗaukar ido ta ke yi yana ta hura hanci, a lokacin ne kuma Besty ya kira Raudah ya sanar da ita an daura,

"Amarya ayuriri!!! Yau kin zama matar aure" Besty ya faÉ—a cike da zolaya, kuka Raudah ta fashe da shi hakan ya sa ya kashe kiran saboda ba zai iya jurar jin kukanta ba, daga nan wajen cin abinci aka nufa inda aka ci aka sha aka yi hani'an....

Misalin ƙarfe biyar na yamma jerin motocin ɗaukar amarya suka tsaya a daidai ƙofar gidansu Raudah, a lokacin tana tsugunne gaban dangi tana rusa kuka, addu'ar zaman lafiya mai ɗorewa ake mata daga nan Anty Salimah da Anty Hassana ƙanwar Abba suka kama ta suka kai ta ɗakin Abba, shi da abokansa da kuma yan'uwansa ne a ciki, nasiha mai ratsa jiki suka yi mata sannan aka fito da ita aka nufi wajen Mommy, addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba Mommy ta bi 'yarta da shi, da ƙyar aka ɓamɓare Raudah daga jikin Mommy zuwa cikin mota, har aka dangana ta da katafaren gidanta da Noor ya gina mata ba ta daina kuka ba, kowa sai santin gidan ya ke yi, a haka aka shigar da ita, daga nan kuma aka fara shirin sallar magriba saboda daga gidan za a shirya tafiya wajen dinner.

Wajen dinner ya cika da yan'uwa da abokan arziƙi ta kowane ɓangare, ango da amarya sun sha kyau har sun gaji, ranar kam an yi rawa da kuma watsi da kuɗi, da gangan Noor ya taka ma Dee ƙafa lokacin da ya shigo yi ma Amarya manni, shi har ga Allah ya tsani yaron, amma ba komai ai ya zo ƙarshe, abinci serve your self ne, can na hango Sanadin Besty Fan's 1 sun sha anko suna ta ɗibar kaza har da masu sakawa a leda nace to! Su kuma waɗannan gayyar wa? Ban gama mamaki ba na hango Sanadin Besty Fan's 2 suma an ba su fili suna taka rawa na ce yau kam Raudah'n Besty an sha gata, ta ba da Sanadin Besty Fan's sun miki kara, sai dai fa sun kwashi gara.
Ba'a tashi a dinner ba sai ƙarfe shabiyu na dare daga nan kowa ya watse ya koma inda ya fito, ƙawayen amarya kuma aka mayar da su gidansu Raudah saboda Abba ya ce babu mai kwana ba ya son wanan ƙaƙalen kawai a bar ango ya shiga gidanshi...

Adnan kam soyayya mai ƙarfi ce ta ƙullu a tsakanin shi da Zeenat, domin har ya kai kuɗin aure an saka rana, bai da wani buri da ya wuce ya same ta a matsayin mata, ya ma manta da wata Fadeelah don ko ta kira shi a waya ba ya ɗagawa, shi ya sa ta ɗan daga mai ƙafa kwana biyu.

Yau Fadeelah ta tashi da matsanancin ciwon kai, ga zazzabi, ko'ina a jikinta rawa yake, ga shi komai ta ci sai ta amayar, gaba ɗaya ta galabaita, ganin zazzaɓin ya ƙi sauka ne ya sa Anty ta shirya ta suka tafi asibiti, bayan likita ya gama mata aune-aune ya miƙa ma Anty result yana faɗin

"Congratulations, tana É—auke da ciki tsawon sati shida"

"Ciii meee?" Cewar Anty ta faɗa tana zazzaro ido, tabbatar mata da cewa Fadeelah na da ciki likita ya yi, jin haka ya sa Fadeelah ƙwalla wani uban ƙara ta faɗi ƙasa sumammiya...

**** **** ****

A daren da aka kai Raudah Noor bai mata komai ba saboda kulle ƙofar ɗakinta da take yi kamar yadda Besty ya ba ta shawara, ai kuwa ba ƙaramar ƙuluwa Noor ya yi ba, amma ya tabbatar da cewa duk randa ta shiga hannunsa za ta gane ba ta da wayo, a haka sai da ta shafe sati ɗaya tana kulle ƙofar idan dare ya yi, ranar kuwa da ya sace ta ya riga ta shiga sai da ta faɗa ma masu anguwan garinsu, don sai da ya sauke ma ta sannan ya samu nutsuwar, kwana Raudah ta yi tana kuka, daga bisani kuma ta warware suka ci gaba da shan soyayyarsu kamar za su mayar da juna ciki, sai yanzu ne ta kuma tabbatar ma da kanta cewa tana ƙaunar Noor fiye da tunaninta, duk da halayen shi na i don't care ba wai ya daina ba ne, ganin shi ba mai irin wannan ra'ayin ba ne ya sa ta rage damun kan ta....
Chapter 12 · 0% Book details