← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 19

Chapter 41-50

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Lailah lailah lailah ki fita a idona in rufe ƙwafa tayi ta koma ta kwanta ta dauki wayar ta tana game,


Dariya lailah tayi tace

"Iyeee kin ji Hausa to na fito rufe idonki ta Giwa ,

Pillow cases ta ɗauko ta dinga jifanta da shi sosai lailah take dariya ganin ta kusan cin mata yasa ta buɗe kofa aguje ta fita tana dariya juyowa tayi jin ance


"Lailah Giwa ,

Tace


"Na'am najuwa bauchi yakike yau ke ce a hostel din mu ?"

Eh Wallahi nice nazo gun Fatima bichi ne

Okay ina tayi murna kin kusan barin S.D Giwa midwifery and nursing Wallahi ji nake dama nice zaki koma gida duk wani abu da ake a family ban da kai Wallahi bana jin dadi

Dariya tayi tace

"Kamar yau ne kema haka zaki ga kin gama nifa Wallahi ji nake ranar Monday Giwa midwifery and nursing tayi min kadan saboda murna amma ta wani fannin bana jindadi zan bar abokanan arziƙi ina fanna ?"

Wallahi zan can ki gaskiya domin nima ina tunanin ranar rabuwar mu da fanna tana ɗaki ita tama koroni

Okay ki gaishe mun da ita hmm me hali baya fasawa in kuna abu yawa yara

Zata ji insha'Allah Wallahi najuwa bauchi bakisan fanna ba

Mayafin ta ta gyara tace


"Gani nake duk ke ce da laifi shi yasa ta koroki fanna da take silent ba ruwa ta da magana ,

Hmmm kawe Laila ta ce

ganin ta tafi room 7 yasa itama ta shiga ɗakin su


Sosai hankalin ta ya tashi ganin fanna ta zuba ta gumi da sauri ta ƙarasa bakin gadon ta tace

"Fanna lafiya naga kin zuba ta gumi ?"

A jiyar zuciya ta sauke tace

Lailah mun shiga ukku na ɓallo ruwa

Gu ta samu ta zauna tace

"Ban gane kin ɓollo ruwa ba fahimtar dani ?"

jiki a sanyaye tace

Giwa yana ne mana yan zunnan naga an sa agroup na chemistry kinga reg number bata fa

Da sauri ta amshi wayar zaro ido tayi tace

"To ai naga test ɗin ba shi ne yayi mana ba sir David ne kuma ai mun cinye to me hakan ke nufi ?"

Lailai nima ban sani ba to Allah ya kai mu gobe sai ki raka ni inje gunsa Wallahi yau watana biyu da fara makarantar nan hanyar ofishin sa ma ban sani ba

Ni na sani yana kusa da lab biology

Ajiyar zuciya ta sauke tace


Wallahi Allah yana gani ba halittar da nake tsoron haɗuwa da ita irin Giwa bana so duk wata sabgar da zata hadani da shi ayi fusƙar mutum yawa hadari saboda haɗe rai ba annuri Wallahi Inna Ganshi gabana har waɗuwa yake Dan Allah du beshi yawa basamude saboda tsayi da kiba


Ajiyar zuciya lailah ta sauke tace

"Ke ba ke kaɗai ba kike jin tsoron Giwa,


Wannan kenan


Giwa dazu tsohon ministan manfetur ya samene a office ɗina a kan zancan ka da yar sa

Tuni gumi ya wanke shi da kƴar ya buɗe baki ya ce

Abba jadda Wallahi ko kadan ba zan iya rayuwar aure da Rumaisa ba tarbiyar ta da tawa ba ɗaya ba Abba ku ga farceni insha'Allah na kusan kawo muku surukar ku yanzu ina wani binki ce akan ta

Shiru Abba yayi domin shi a abun na Giwa anya ba aljana ce ta aure shi ba duba ga irin lalurar da take tare da shi a lokacin sun tafi hutu Germany cutar ta same shi yana da shekara goma sha takwas likitoci sun mai gwaji to shine zai ci gaba da addu'a Allah ya tsaremai imanin ɗan sa dama al'ummar musulmi Allah ya kare shi daga sharrin shaidan

Jadda yace

Amma Kasan iya daga kafa mun ma ko da za kace ba ka yarda da tarbiyar taba kai ma naga girman Turaine ko

Ƙasa yayi da idonsa be ce komai ba

Giwa ta shi ka tafi

Da sauri ya tashi ganin bakin tsohowa yana magana da alama wani abu zata ce

Bayan ya bar shashin jadda shashin sa ya nufa sai da ya gama gabatar da uzurin sa sannan ya dauki waya bugu ɗaya aka dauka yace

"Ka sameni a shashina "

Kitt ya kashe

Basma na shiga ukku big brother yana nema na


Hmmm lalle kana cikin matsala.......✍🏼


RASHIN SANI


By

Oum yasmeen
Chapter 8 · 0% Book details