← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 19

Chapter 31-40

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zuba mai ido tayi ganin lokaci ɗaya ya sauya a jiyar xuciya tayi tana so taga ƴa'ƴan sa tunani ta shiga yi


Ganin tayi shiru yace

"hajiyar mu lafiya kika shiga tunani?"

Fir gigit ta dawo hayyacinta tace

"bakomai tashi muje dinner ya kammala "

Badan yayarda bakomai SBD batun yau yake ganin hajiyar mu cikin tunaniba to koma mene zai tayata da addu'a komai ya daidaita yace

"TO, muje ko ya buɗe mata ƙofa yana murmushi bakowa ke ganin wannan tsadaddan murmushin a fusƙarsa ba wasuma cewa suke sa baka dariya sai hamma


Jamai kumatu tayi cikin salon tsokana tace

"Ooni yau she wannan yaron nawa zai girma ko sai Ka kawomin girlfriend din kane ?"

Kwabe fuska yayi kamar karamin yaro yace

"Please hajiyar mu mubar maganar girlfriend Dan Allah ya hada hannuwa biyu alamar rokonta "

huce shi tayi ta barshi tsaye tana nunamai alamun yanzu ta fara kenan ajiyar zuciya ya saki ya fito shima

Tuni kowa ya hallara shikadai ake Jira kujerah ya ja ya zauna ya dubi mahaifinsa mai cike da kamala da nusuwa kallo daya zakai mai kasan hutu da jin dadi ya zauna mai yace

"Abba barka da dare "

Cikin kulawa yace

"yauwa ya aiki?"

Kansa akasa yace

"Alhamdulillah"

Duban Dan nasa yayi yace

🐘Giwa in mun gama cin abinci ka sameni a babban floor

Da sauri ya dago ya dubi mahaifinnasa Allah isa ba wata magana da ta shafi rayuwarsa za aimai ba duk da yasan sarkin tone tone ba lafiya da kyar ya iya cewa

"To amma ba wanda ya fahimci halin tsaka me huyar da ya shiga sai hajiyar mu da abba domin sunfi kowa sanin halinsa mutum na ukku kuwa ko mutsi giwa yayi yasan me yake nufi wato jadda

murmushin gefan baki abba yayi hajiyar mu da take jinsu bata ce kala ba. ta dubi basma tace

Basma yi saving din mu

Tashi tayi tace

"To hajiyar mu cikin nutsuwa take bawa kowa abin da yake so kan giwa ta xo tsayawa tayi ta zuba mai ido domin tasan balalle bane yaci abinci me nauyi ba bakin ta na rawa tace

"Big brother me zan zuba maka? "

da ido yayi mata nuni domin maganar da abba yayi ya daga mai hankali dayake yasaba musu ta fahimci me zaici a zuciyarta kuwa cewa take

"duk wacce ta sake ta aure yayansu ta shiga ukkunta da fi'ili kala kala karkayi wannan wannan nake so ga tsari yawa mace

chips ta zuba mai kadan sai ta tsiyayome fresh milk me sanyi ta bashi


kallo ta yayi yace

"Thanks"

dayake tana kusa da shi ta ji me yace

"Kai ta gyadamai kawe tadauko bowl ta dauko ta zuba farfesun hanta komawa tayi ta zauna ta fara Ci"

ba ka jin sautin komai sai na chokali da a.c sosai kuwa ya nutsu yana cin abinci ban da musu'af wanda sai muzurai yake yasan sarai shirun yayan nasu ba alkhari bane ko fadan daya saba gwara yaji yayi ko zai sami salama domin zuwa yanzu yasan ansanar Mai da abin da ya aikata

Tissue ya dauko ya gige bakin sa ya mike

kan abba a kan kwanon sa yace

''naga ko rabi baka ciba ka tashi ?"

Abba nako shi

Sai a yanxu hajiyar mu ta ga da cewar tayi magana tace


Abban giwa ka manta my son rainon uncle bature ne ?"

Duban ta yayi yace

"Hakane na manta "

Kallo musu'af yayi ya juya ya fita kai tsaye shashin jadda ya huce sai da yayi tafiya me nisa tukunna ya nufi tamfatsaitsan shashin nasa yawa Bana tsohoba ga kayan mure rayuwa sallama yayi

aa me gidana ashe Kai ne yanzunnan muke zancan ka tsohowar matar ta fada kallo daya zakai mata kasan tsohowar yar boko ce

samin kusa da jadda yayi ya zauna ya dauki tufa ya faraci yace

"hmm ya kamata tsohowa tun huri ki nemi mijin ki kin ga yaro me jini ajika kin ce mijin ki "

Pillow case na luxury sofa din ta ta dauka ta jefa Mai tace

Ai kai yaran gidan nan sunkusa fara ce maka kaka tsoho duk kannan ka sunyi aure sun bar Ka

hmm ai aure lokacine ni nawa be zoba

Ta shi yayi daga kishin gidar da yayi ya gyara glass dinsa yace

Ungo sa'eed yayi masa da kuwa

aa bara in tashi yau rigimar tsofaffi ta tashi yana fadar haka ya miki

cikin karfin hali jadda ya jawo shi domin karfinshi yayi rauni hausawa sun ce jiya ba yau....

La aboki bara in zauna kar in karyawa wa su uncle bature tsoho

dariya dadtijon tsuhon yayi duk gashin shi yayi fari amma duk da haka yana cikin hayyacin Shi yace

hmm da baka zauna ba da na karya ka

kai ya jinjina yace

Uhmm tsohon alkhali nan fa ba reburin Shari'a bane

tuni giwa ya motso mai wani abu aransa kalla ta taro a idonsa ya Kamo hannusa yace

"Sa'eed Dan Allah ko bayan raina kane mota ka bata hakuri wallahi kullun da maganar da ta fadamin da ita nake kwana duk da alokacin yarinyar jaririya ce amma wallahi ko yau na ganta zan gane ta sa'eed wannan shine kuskuran danayi bazan taba mantawa da shiba wannan shine tabon da dangin giwa yake da shi amma bakowa ya sani ba sa'eed a gaban ka akai komai sai de kai yarone ba komai zaka fuskanta alokacin ba muntafi mun barta tana kuka duk irin tausayina ban tausamata ba ban cika adalin shugaba ba"

goge masa kallar idonsa yayi yace

"ban taba ganin jajircaccan alkali be Ka mata Dan kayi kuskure daya kadamu kanka ka dinga jawowa kanka ciwo"

hmmmm sa'eed kenan

Cikin i don't care yace

wallahi sa'eed sa'eed sa'eed a kwai lokacin da zan baka mamaki inhar ba kai aure ba a cikin kannan ka zan zabo yarinya karama in hadaku aure da ita kuma kasan dangin giwa ba saki ba yaji

Da sauri ya dubi kakan nasa yasha farar shadda gashi ya tsofa amma zuciyar mazan jiya tana nan sosai yake mamaki rikidiwar kakan nasa cikin karfin hali yace

Jadda komai fa lokacine

Wallahi ina bayanka mijina

to ai daman haka zaki ce ba tunyau nasan bakin ku daya da jadda ba na tafi

muryar abba yaji yace

"Tsaya muyi maganar anan ba sai munje floor na ba "

tambas yau ya shiga tsaka me huya ga wayannan tsofaffin ga abba fita ta sai Allah jikin sa asanyaye ya koma ya zauna

wannan kenan

hello abbie dazu ka kirani mun fita nida Laila kakan su ba lafiya ban Sami damar dagawa ba

ayya kice ina yi masa sannu

Laila Abbie nayiwa jadda sannu

what fanna me kika ce kamar na taba jin sunan mutumin nan amma a American tuni zufa ta karyo mai anya komai baya Shirin tunuwa ba

Wata kila Abbie ai babban mutun ne ae

Da kyar ya iya saita nutsuwar shi yace

"Okay"

lafiya naga muryar ka ta canza?"

na tashi da murane

Allah ya baka lafiya

"Ameen"


Abbie yakuke ina nana ta take ?"

my princess yau aikin kwana nake kowa lafiya ya karatu ?"

Alhamdulillah Abbie

"To, kiyi karatu sai anjima ko banda tsokana

Nide nide kullun ka dinga yimin kallon matsokaniya

Hmm nasan halinki mamana tunkina yarinya a kula banda saurayi

Turo dan karamin bakinta tayi kamar yana ganinta tace

"To

Okay ahuta lafiya bye

Bye

lumshe idanuwanta tayi tace

"Laila wani zubin nakance nafi kowa sa'ar mahaifi yana sona "

Laila da ta zuba mata ido tace

Uhmm gaskiya kam wallahi kinyi dace we fanna yawa a India na ganki a jikin giwa wow hadin zaiyi kyau kinga ke kina da haske sosai shi kuma Ethiopian color ya'yan da zaku haifa sai an kallesu an kara wallahi

tuni wani bakin cikin ya tokare mata zuciya tace........✍🏼


🚴‍♀️🚴‍♀️ Topa me ke shirin faruwa ne


RASHIN SANI


By

Oum yasmeen
Chapter 7 · 0% Book details