← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 19

Chapter 16-20

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 9 min read

"A'a hajja agaskiya nide nagaji kawe ki nemo hanyar da zai kalleni kullum ai ta abu ɗaya ,

hanka ɗeta tayi ta tashi domin abun na amal ya huce hankali anya ba wani asiri akaiwa yar tata ba anya zata bata haɗin kai su gudanar da aikin su lalle akwai aiki agaba ta faɗi aranta

Kuka Amal ta saki domin wallahi in tarasa yaya sa'eed ba zata iya rayuwa ba wayar tace tayi ring har sau bakwai ana takwas ta dauka ganin mai kiran yasa da sauri ta dauki wayar tace

Hello uncle sulaiman ina huni

lafiya lau dukkan ku kozo giwa hospital jadda ba lafiya jikin sa ya rikice na bugawa yaya be dauka ba ina ga baya kusa

"Innalillahi bara in faɗawa hajja gamu nan zuwa ,

"To, ya kashe wayar a guje ta hau sama domin sanar wa da hajja saƙon uncle sulaiman a hankali ta tora hannun kofa samon ta tayi tana kwance tana danna waya tace

"hajja ki dauko key ɗin mota mu tafi asibiti jadda ba lafiya ,

mmsswww ta ja dogon tsaki tace

We yaushe zaki yi hankali to bani da lokaci in mahaifin naki ya dawo kwaje ai ubansa ne ba nawa ba yau ƙawata da muka haɗu a charting zata zo dan haka bani da lokacin zuwa dobo tsoho ayi mutum da shegen taurin rai ya mutu kawe muci gado ina son a sa company giwa rice a cikin gaɗon mahaifin ku

Hajjjjah dan Allah ki dena son duniya duk wata hanya bata gari ba nan kike biyewa hajja kinsan ranar da yaya giwa yayi birth day ya bashi company amatsayin gift nashi dan Allah ƙarki ɓallo mana ruwa

Zanci uban ki Amal huce kiban huri shi yasa nake son ruky tana son duk wani farin ciki na huce kiban huri wallahi da ace a asibiti na haifeki Amal da sai ince canza ki akai ba jini na bace kee to ruky zan sa ta duk ga nunawa shegen yaron nan tana son shi ko za adace ke kuwa bara mahaifin ki ya dawo sai nasa ya haɗaki da wani acikin family kije can ki ƙarata

A guje ta fita domin wallahi ta fara gajiya da halin hajja

Wannan kenan

a gajiye suka dawo hostal bakin gado fanna ta zauna tana sauke numfashi tace

Dan Allah sister lailah giwa temaka ki dafa mana ko da taliya ce ai muna da miya ko ?"

"To, bara in cere kayana ,

"okay bara in watsa ruwa shiga ban ɗaki tayi tayi wanka ta ɗauro towel ta fito inya halitta ubangiji yayiwa fanna yawa ita tayi kanta bata da ƙiba amma bazaka kirata siririya ba shap ɗinta kamar na coca cola tana da diri dressing table ta nufa ta ja stool ta zauna shafe shafe ta fara har laila ta fito daga kitchen daya ke banne a dakin su ta tsaya ta kurawa fanna ido domin ta rasa dawa fanna take kama a cikin uncle ɗinta da ƙarfe tace

"yesss wallahi na gano ,

Cikin fir gici fanna ta jefar da turaran da ke hannun ta aikuwa ya fashe bakin ta na rawa tace

"Lafiya laila mai yasa me ki wani abun kika gani ?"

ke matsoraciya yau na gano dawa kike kama cikin uncle ɗina wallahi

Hmmm laila amma kin dauki hakkina kinga fa na fasa turarena

Mmssww aikin kenan daman tun ɗazu baki gama shiryawa ba gashi ni har nagama mana girki inkina wani abun wallahi halinku ɗaya da yaya inyana shiri kamar mace

Dan girman Allah ina cikin nisha ɗina kina sako min giwa aciki

da sauri laila ta zare wayarta daga chaji tace bara in nuna miki uncle Mamud kamar ku daya wallahi har da su yisham kina kama barin miemie auta wajan pic ɗinta ta nufa tafara dubawa cikin sa'a ta gano pic ɗin su uncle Mamud tace kinga

amsa tayi tini ta waro ido domin abin ya fara bata tsoro musamman babban mutumin da alama shine uncle Mamud gawata mace zata girmi amminta sun rumgumai juna cikin farinciki kallo daya zakaiwa family ɗin kasan hutu da jindaɗi sun zauna musu tuni suka bata sha'awa inama family ɗinta ne a haka suke farinciki ajiyar zuciya ta sauke ta miƙawa laila wayar ta tace

muna kama dasu daman haka ubangiji yake ikon sa

Hakane wannan uncle Mamud ba'a ƙasar nan yake da zama ba saboda tunda wani abu ya faru a cikin giwa family ya dena zama saide ya zo ziyara yana da kirki sosai yau shekara goma sha tara kenan da dena zama akano yana Turkiya tare da matarsa da ya'yan sa guda ukku yisham shine banban ɗansa sai muhibba sai auta miemie sunan hajiyar giwa ne da ita wato maryam shine ake cemata miemie a hannun maman su dr giwa ya tashi saboda haka sun saƙu da dr giwa uncle Mamud dan bokone mai haƙida kinsan da dr giwa zaiyi degreen ɗinsa na hudu agunsa yaje yazauna yayi duk wani harkar kasuwancin uncle Mamud to ahannun dr giwa suke wasu acikin familyɗin mu cemai suke uncle baturai saboda tun da dr giwa ya fara magana sai yace uncle baturai

In akace mai yace

Uncle mamud sai yaƙi tanan sunan baturai ya fara binsa iya so da kauna dr giwa yana yiwa uncle shi

fanna tace

Allah sarki wallahi har ya shiga raina zanso ingan shi a zahiri

Dariya lailah tayi tace

Infaɗa mai ga mai ciwa ɗansa kuma mai sunan jadda tsoho

dukan wasa fanna ta kaiwa laila aikuwa ta guce cikin so da kauna suka fara cin abinci tashi fanna tayi

badai har kin ƙoshi ba nifa tsiyata dake kenan zaki ta ihu yunwa yunwa ana zubuwa ki ci kaɗan ki tashi

hmm sister so kike cikina ya fashe iya abincin da zan iya ci kenan fridge ta buɗe ta dauko lemo da ruwa ta ajiye musu kadan ta tsiyaya a kofe ta sha sanna ta ɗaga jakar ruwan ta shanye ajiyar zuciya sauke tace

"kinga yau abbiena bekirani ba bara in kira shi saboda basan aikine ya tsare shi ,

aikuwa gwara ki kirashi tunda kinci kin ƙoshi ai dole ki tuna da abie

pillow fanna ta jefa mata tace

Wallahi laila kiki yayeni bara insa kaya sai in kirashi mu gaisa yau nasan aikin kwana yake ba zan sami gaisawa da nana ba

"To, ki kira mama sai ku gaysa da ita,

tuni farin cikin fanna ya gushe cikin ƙarfin hali tace

"yanzu Mama ina kirata balalle ta ɗaga ba saboda nasan tana aiki daman ace da rana ne zan iya cewa ammi ta kai mata wayar sai mu gaisa ,

"okay ni wallahi ina mamaki we kice ammi kishiyar maman kuce amma suna da haɗin kai wallahi ba kamar irin banzan kishin da yanzu da akeyi ba

" murmushi fanna ta saki tace,

Ai ita ammi ba ruwan ta ta riƙeni tamƙar yar ta Allah be bata haihuwa ba tana son yara sosai

wayar lailah ce tayi ringing da sauri ta daga tace

hello sister basma yakike ya su mamy

"Wallahi lafiya kinsan jikin jadda ya tashi ?"

innalillahi wallahi bansani ba

aikuwa an faɗa a cikin group

"tun da safe ban hau online ba a ina aka kwantar da shi ?"

giwa hospital aikuwa gobe zan zaje in duba shi koma kafin arufe hostal bara fanna ta rakani

"to shima fa anty Aisha dazu ta bugowa mamy waya tana kuka we uncle baturai ba balafiya wallahi na sara wanne sirri suke ɓoyewa suda big brother inaga damuwar sa ce fa tasa jadda rashin lafiya inna tambaye mamy sai tace a kwai lokacin da kowa zai sani innace ta faɗamin sai tayimin shuru

Wallahi nima nasha tambayar abba mai yasa uncle Mamud baya zama saidai in anyi mutuwa yazo ko biki to mai suke ɓoyewa haka

Allah masani mu cigaba da yimusu addu'a koma mene yazo da sauki

"To insha Allah

"saida safe ki gaishe min da fanna ,

Allah ya kai mu insha Allah zata ji

fanna shirya ki rakani dubiya

"Wane bashi da lafiya ?"

jadda ne

Allah ya bashi lafiya

"Ameen"
cikin nutsuwa ta tashi ta nufi wardrobe ta nufa inda ta dauko wata hadaddiyar lufaya pink color da adon flower blue da milk color tayi kyau iya kyau kana nan kaya tasa aciki sanan ta naɗa lufayar ta

masha Allah fanna komai kika sa kyau yake miki wallahi

"murmushi tayi tace

"kema abayar da kika sa tayi miki kyau sosai,

barimar azurfa ta dauko ta sa aɓolal hancin ta satin da ya huce suka fita shopping suka siyo lips gloss tasa a labbanta sai sheƙisuke sun ƙara pink color agogo tasa da ƴar ƙamar sarƙar huya tasa glass ɗinta sai zuba sassanyan kamshi yata ke humra ta ƙara daukowa ta shafa ajikinta nan turaran kabbasa da ta turara kayanta dashi suka haɗu suke bada wani irin kamshi mai daɗi jakarta ta janyo tasa ta sa plat shoe milk color cikin siririyar muryar ta kamar sarewa tace

Lailah ki sauri ki fito mu tafi

Iyee dan yau kin rigani shiryawa ko to veil zan ɗauko saboda yaya baya son shigar banza wata ƙila mu haɗu dashi

Insha Allah baza mu haɗu dashi ni wallahi sai in fasa zuwa ai rasa wana je dubawa zanyi jadda tsoho shi tsoho

dariya laila tayi harda ruƙe ciki tace

wallahi fanna ki guje ranar da dr zai san abin da kike mai hmm haduwar ku bazatai daɗi ba fito mutafi fitowa sukai

aa fanna lailah unguwa za aje

juyowa sukai laila tace

Ehwallahi xubaida

adawo lafiya fanna kinyi kyau

nagode zubaida ina taƙwara ta

Fatima tana ɗaki wallahi

okay to mu muntafi

Kudawo lafiya

Tafiya suke suna yira domin da nisa daga school izuwa giwa duk da darene wajan tamƙar rana agaskiya S.D giwa iya tsaruwa makarantar ta tsaru ban gane dare muke ko rana ba har suka iso giwa hospital kallo daya zakai wa asibitin kasan ankashe dukiya yawa kana america saboda tsaruwar asibiti ga fararan fata sai shige da fice suke domin ma aikatan giwa ba iya baƙar fata bane har da farare suma kansu jar fatar zuwa suke zuwa aduba su kai tsaye suka nufa areception wayyo fanna ban tambayi basma wanne ɗaki yake ba bara in kirata ringing take yi ba'a daga ba waiting chairs da aka tana dar domin zama fanna ta zauna ta dauko wayar ta tana dad dan nawa kamar daga sama taji ance

yar barno da sauri ta ɗago tuni sukai ido hudu da dr giwa da sir birnin kudu aibata san lokacin da ta rasa nutsuwar taba sabo kallo ɗaya dr giwa yayi mata hanjin cikin ta ya kaɗa tashi tayi cikin rawar murya tace laila juyawa tayi bata ga lailah ba alamarta ta tafi tambayar ina aka kwantar da jadda

"yar barno dubiya kikazo ?"

kai ta ɗaga mai yawa ƙadangaruwa yayin da dr giwa ya kafeta da macizan idon sa masu kama dana macizi domin besa glass ba…………✍🏼


RASHIN SANI


B̑̈y̑̈

O̥ͦu̥ͦm̥ͦ y̥ͦḁͦs̥ͦm̥ͦe̥ͦe̥ͦn̥ͦ


*KING AND QUEEN WRITING CHAMMBER*
✬✬✬✬✬✬✬✬✬✬❃✬✬✬✬✬✬✬✬✬✬✬★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★✬✬✬✬✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰
Chapter 4 · 0% Book details