← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 19

Chapter 6-10

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 6 min read

Na shiga ukku fannah shikkenan baƙin ki yau ya jamana kin san waye acikin motar nan kuwa ?"

cikin tsiwa ta murguda baki tace

ko ma waye ba ya ganin gaban sa ya baɗa mini kura jibi fa kayana yarda sukayi nasan wannan alhuda hudar ne mai baƙar zuciya

Dafe girji lailah tayi domin ta rasa wacce irin tsana fanna buƙar gana tayiwa dr giwa ko ba komai ai dr giwa yayanta ne domin da baban shi da baban ta uwa daya uba daya fannan tana girmama kowa na dangin giwa ban da dr giwa


abu ɗaya tasani fanna bata son makarantar kwana sai gashi an kawota in tayi mata fada sai tace da be buɗe makarantar shi ba da ba a kawo ta da ƙyar ta i ya buɗe baki tace

"dan girman Allah fanna kiyi shiru kinga fa yana ƙoƙarin fitowa ai kuwa bata rufe baki ba sai gashi ya fito kallo daya nayi mai ban so in dauke ido akansa ba chocolate color ne irin black american ko kuma ka ce ethopian color shi ba fari ba ba koma ka kirashi bakiba wane irin farine da shi idanuwanshi suna sanye da baƙin glass ga wata iriyar ƙasumba ta sha gyarah sai sheƙitake yana sanye da suit baƙa inda ya samata fa'ar shirt yana sanye da wando baki yayi kyau yawa ƙar kadena kallosa a kuma tunsa na dama yana da wata tawadar allah wacce ta ƙarawa fusƙarsa kyau hannunsa ruƙe da lab coat da wasu files ahannusa yayi da sir yusif birnin kudu ya roƙemai jaka da alama magana suke mai mahimmanci jan


Laila tace

"Fanna zu mubar gunnnan ,

naƙi wallahi ko ba yau ba sai na rahama dan rainin hankali mai ido yawa na mujiya

hmmm fanna ai kida shi baku da maraba yana da ido kina dashi wallahi wani zubin ganin ki nake kina kama da family ɗin giwa

Allah ya kiyaye inyi kama da shi jibe shifa tsoho dashi yo ba dole yayi baƙar zuciya ba antsufa ba aure dole abubuwa su dame shi

rufe mata baki tayi karaf a idon sir birnin kudu yace lailah giwa ku zo lafiya kike janta yawa wasu yara

wata uwar harara fanna ta yiwa lailah kamar idonta zai waɗo ƙasa sum sum sum ta tafi duk da ji take ka mar ta koma hostel ta canzo kaya gawata yunwa da take ji daman bata karyaba suka fito sai anjima sai sudawo suyi girki su koma makaranta haka lailah ta take mata baya tsugunawa sukai da ƙƴar suka haɗa baki wajan cewa

Good morning sir daga haka su kai shiru sukayi yayin da dr giwa ko arzukin kallo basu samu ba yan mata da yawa na makarantar sun mutu akan son sa

sir birnin kudune ya amsa yace

"lailah lafiya kuke faɗa kida aminiyar ki ?"

Cikin tashin hankali har tana rarrabe magana alamun ba gaskiya tace

Sir ba-komai ke fannan tashi mutane fi aji

aa ai ban sallame kuba in ke yar barno ya akai ake janki kike turjewa da alama de jinin secondry yana jikin ku ya kafe ta da idanuwa

Wani baƙin cikine ya tokare zuciyar fanna ga wani rainin hankali shiru tayi tana wasa da yan yatsunta zara zara

cikin deep husky voice ɗinsa ako yaushe yace

"ke ciro abin da ke hancin ki ,

Da sauri ta dago ta kalleshi wato shide wannan tsohon duk inda aka haɗa hanya da shi matsalane yanzu duk irin dukiyar da yake da ita sai ya karɓi gold ɗin da befi na dubu dari biyar ba yanzu inta koma gida ta cewa ammi me inta tambaye ta yana ina domin da za atawo da ita sai da ta ƙarba ta ajiye a gunta saboda sun karanta roles ɗin makarantar sunga ba ado ba sa abin hannu balle sarka ba yin kunshi to sai tayi da bara ta je ta dauko abarta cikin sassanyar muryar ta kamar sarewa cikin shagwaɓa tace

"sorry dr ,

Tsawa ya daga kamata aikuwa tuni hawaye ya fara zarya afusƙarta da sauri ta tashi ta rumgumai lailah ta fara kuka

Lailah ciro min abin da ke fusƙarta

"TO, to yaya giwa da sauri ta dago fusƙar ta ta fara cirewa kash barimar irin me ƙawanyar nan ce kunsan da huya sata da cire ta abin ka da farar fata tuni hancinta yayi ja ana cirewa ta ja da baya ta kifa ƙanta amotar sa ta saki kuka mai cin rai

ungo

okay ya sa hannu ya amsa motar sa ya shiga ya ajiye ta sannan ya dubi sir birnin kudu yace

ni zan shiga office nan da anjima zani giwa hospital dayake bani sa da makarantar taci kima ana iya shiga

"okay afito lafiya,

tafiya ya fara tamƙar mai tasauyayin ƙasa da nutsuwa tambas kamiline kuma muskili mai kafiyar zuciya ba macan da zata same shi amatsayin miji ta kusheshi

yanzu yar barno kihi haƙuri zan yimai magana insha Allah zai baki kinji

cikin kuka tace

ɗazu ya baɗamin kura yanzu kuma ya kwacemin abuna

dokar makaranta ce haka yar barno ba mukula ba muna saurine kihi haƙuri

tashi tayi daga kifa kan datayi idanunta sunyi ja saboda kuka tace laila zo mutafi

cikin tsokana yace lailah kama hannun babyn ki naga alama yar rigima ce daga magana sai kuka

dan Allah fanna kihi haƙuri insha Allah dr giwa zai baki

kinga lailah bara in je hostel inshirya kinga naɓaci da gudu ta bar gun tanufi hostel yayin da laila tabita

wannan kenan

yana shiga office ɗinsa ya tararda aiki da yawa zama yayi ya fara duba abin da ke gaban sa cikin rashin sani ya kai hannusa dede hanci sa wani dogun tsaki ya ja we wannan rigimammiyar yarinyar tun ɗazu yake zuwa toilet yana wanke hannunsa amma oud ɗin datayi amfani dashi yaƙi barin hannun sa shifa yanzu yafara tunanin anya kuwa mutumce wannan wanne irin turarene yayi tsaki yafi cikin kwando

lafiya dr naga kana tunanin ?"

Firgigit ya dawo hayyacin sa ya maze dayake yana da zurfin ciki da huya kagano meke damunsa yace

lafiya qalau yanzu so nake inji giwa inga ya aikin nasu yake tafiya tashi yayi yafara neman mukullinsa da wayar sa

hmmm dr giwa dan Allah ina nemarwa fanna afuwa kaga sabowace bata san yarda

da katar dashi yayi yace

pls birnin kudu bana son jin maganar nan ai duk wata doka ta makarantar nan sai da na faɗa

me isa baka daukan abu da zafi amma ayannzu ka zafafa dan wannan kuskuran da fanna tayi

ban za yayi mai ya fita ya bugumai kofa mota ya shiga zuciyarsa na ɗaci yarasa dalili shima besan da lilin dayasa yayi haka ba tunda yana yiwa sababbi afuwa
……………✍🏼


RASHIN SANI

Story and writing

Oum yasmeen
Chapter 2 · 0% Book details