← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 19

Chapter 91-95

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 6 min read

Basma tace

"Daman kun san juna ne ?"

Cikin farin ciki lailah tace

"Eh ita ce fanna fa ,,

Zaro ido basma tayi tace

Dan Allah ina yi miki murnar shigowar a halin mu

Murmushin ƙarfin hali fanna tayi ta zauna a baƙin luxury bed ɗin ta

Lailah kuwa mamaki take tuni ta tuno da zantukan fanna kwanciya tayi ta ɗinga dariya yawa wata zarar riya cikin dariya tace

"Besty wannan shi ake kira da kamun Ubangiji we yau gaki a gidan tsoho Giwa hhhhhhhhhhh,,

Shiru fanna tayi kwalla ta taro a idanunta

Lailai tace

"Yau ba bakin magana ne Mrs Giwa ?"

Banza tayi mata ta tashi ta shiga toilet sai da tayi kuka me isar ta tuƙunna ta canza kaya zuwa sleeping dress ta sa hibaji ta fito

Yauwa basma dare yayi ya zo mu tafi

Dan girman Allah ƙar ku tafi mu ƙwana tare

Zaro ido lailai tayi tace

"Ki rufa mana asiri gobe dai zamu dawo ko basma,

Ehmn wazai ƙwana shashin ya Giwa gobe da safe a kai mu asibiti a yi mana ɗaurin ƙaraya tab

Jin abin da ƙanwar shi tace yasa cikin fanna ƙara kaɗawa tace

"Dan Allah ku tausayamin mu ƙwana tare da ku,,

Kin ga lailah ni na tafi dan Wallahi ina son jiki na

Wani hawaye ne ya zobo a idanun ta domin ganin su lailai sun tafi

A bangaran Giwa kuwa

Shirin kwanci bacci yayi bayan ya sha coffee addu'a yayi ni kuwa na ce asuba ta gari


Turkiyya Istanbul


Uncle Bature zaune yake yana shirya kayan sa domin gobe zai je Kano hankalin sa yayi gida

Tun safe zainab take cika tana batsai wa sosai yaran suke murna zasu Kano

Gama haɗa komai yayi ya ƙwanta ƙarfe bakwai suka gama shirin su suka fito driver sa ya ɗauke sa ya nufi airport da su sauke su sukai suka nufi Kano

"Cikin farin ciki sojojin da suke tsaron gidan suka buɗe musu domin sun gane wane tuni labari ta ishi ƙunnan hajiyan daura da jadda kowa na gidan fitowa tayi tarar sa shashin jadda suka nufa duk kan su har ƙasa su zainab suka gaida su

Uncle Bature yace

"Ina my son yake ?"

Cikin ɗauki uncle sulaiman ya bashi labari

Sosai yayi farin ciki inda ya ɗauko waya

Zai kira shi

Jadda ya daka tar da shi yace

"Bara ai mai baza ta in Kira Shi da waya ta,,

To yace

Bugu ɗaya biyu ya ɗaga

Yace

"Tsoho lafiya da farar safiyar nan ka kirani ?"

Uban kane tsoho domin har yau jina nake a matashi na ku zo kai da matar ka Kitt ya Ka she wayar

Daman tun a suba yayi wanka jallabiya yasa ya xora slippers ya fito ganin an share komai sai ƙamshi ko ina yake zubawa jin alamun motsin mutum yayi a kitchen nufar kitchen yayi sosai tayi mai kyau cikin duguwar riga ta atamfa ta sa babban mayafi ta rufe cikin sa tamar wani maganaɗisu su ya ji ya jata gun ta yayi mata kyakkyawar runguma

A firgi ce ta juyo har yana iya jin ɗimin numfashin ta lallausan hannu sa yasa a bakin ta yace

"Shiiiii ƙarki min kuka domin nasan ke baki da wata sana'a sai ta kuka ,,

Mamakin Giwa kusan sumar da ita yayi bata tsinke da lamarin sa ba jin yayi mata wani kiss a kumatun ta yace

I love You my lovely wife

ƙasa tayi da idon ta bakin ta na rawa tace

"Aiki nake ka sake ni inci gaba da aiki na ,,

Naƙi zo muje shashin jadda mu dawo in taya ki

Dan murmushi tayi tace

"Ka iya girki ne ?"

Cikin jan ta a jiki yace

Muje mu dawo kiga irin abincin da zan girka miki

Hannu ya ruƙe mata suka nufi shashin jadda ganin sun zo yaƙi saƙin ta yasa ta fusge hannunta

Dan murmushi yayi yace

Yarinya zan kama ki

Sallama sukai

Tuni idon kuwa ya dawo kansu da sauri uncle Bature ya tashi yace

"My son kai ne ina yar tawa ?"

Har ƙasa fanna ta ɗurƙusa ta gaishe da su

Cikin farin ciki Giwa ya ɗauki miemie yana yi mata wasa

Uncle Bature yace

Kunu namin pictures ɗin biki in gani

Jadda yace

Husna saka flash a TV ya gani

"To jadda tace ta tashi ta saka ta

Gun pic ɗin abba da jadda da Dr buƙar

Tuni uncle Bature ya tashi yace

"Wallahi jadda shine Wallahi shine,,

Cikin rashin fahimta jadda yace

"Shiwa ?"

Wallahi shi ya ɗauki ta ita da abin da ta haifa shi malamin mu da ya ɗauke mu zuwa project a Turkiyya dan girman Allah ku nemo min shi ya faɗamin ida take

jadda yace

"Alhmdllh shine mahaifin matar Giwa,,

Cikin sauri ya juyo ya ƙurawa fanna ido tambas wannan yarinyar kamar su ɗaya da miemie da isham zamin gu yayi ya zauna domin yana ji a jikin sa wannan ita ce ƴar sa

Waya Alhaji Dawud ya ɗago ya fara kiran Dr buƙar

Cikin mutun tuwa ya ɗauka gaisawa sukai Abba yace

Yau zan tawo Maiduguri

"Allah isa lafiya domin yau Ni ina kamo a sharaɗa kasan na siyi fili ana gina min masana antar shin kafa ,,

"Yauwa faɗuwa ta zo dai dai da zama ko zaka zo nan gidan namu ?,,

Gani nan zuwa Allah isa lafiya ko wani abun dannaw tayi

Wallahi ba abin da tayi sai alkhairi

To gani nan

Sosai fanna ta shiga damuwa ganin har Abbie Ankira to wa abbien ta ya ɗauka Allah isa bashi da laifi

Sallamar shi taji da sauri ta ɗago

Cikin sauri uncle Bature yace

Sir buƙar

Cikin mamaki yace

"Mahmud sa'eed dikko Giwa kaine ?"

Alhmdllh ka gane Ni ga gu ka zauna

Zama yayi kowa na ɗakin ya gaishe da shi

Sir buƙar ina kaltum take da abin da ta haifa ?"


Shiru Dr buƙar yayi yace

Ga fanna ita ce ƴar da ka tafi kabari tambas akwai abin da Allah ya tsara shi yasa ya nufa fanna zata dawo ahalin ta bayan tafiyar ku na tarar jini ya ɓalle wa kaltum ni na kula da ita da baby da ta haifa bayan wata ukku mukai aure daman ni mata ta bata haihuwa to alhmdllh zuwan kaltum ta haifa min yara biyu ni'matullah da Nana Asma'u mai sunan mahaifiya ta

Tissue jadda ya ɗauka ya goge idanun sa ya mai da glass ɗin sa yace

Alhmdllh bayan dana sani da nayi Allah ya nufa da raina zan roƙi su afuwa

Tuni fanna ta kasa gane komai kenan

Abbie ba mahaifin ta bane kenan Giwa ɗan uwan ta ne hawaye ne ya ɗinga zubowa a idanun ta tambas wannan shi ake kira da rashin sani.....✍🏼


RASHIN SANI


By

Oum yasmeen
Chapter 18 · 0% Book details