← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 19

Chapter 96-100 🔚

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 5 min read

Anty Maryam ta rungume ta tana rarrashin ta

Jadda yace

"Yanzu gobe insha'Allah zamu zo Maiduguri neman afuwar kaltum jikkata kiya femin dan girman Allah ƙar ki duba matsayina a yanzu ,,

Cikin kuka fanna ta ce

"Wallahi na yafe muku duniya da lahira ,,

Hajiyan daura ta dubi ta tace

Mun gode e yayi miki albarka

"Ameen tace ,,

Abbie yace

Ni zan koma Allah ya yafe mana baki ɗaya

Addu'a gabaki jadda yayi musu ta haɗin kai

Cikin kuka ruky ta shigo tace

Abbu hajja ta hauka ce

Kafin ta rufe baki sai gata nan ta shi go tana fusgar kayan jikin ta tana ihu ta ce

"Ni na hana Giwa aure hhh Ni nayi Wa Bature ƙurciya hhhhhh owoni shegiya ,,

Uncle mansur ya ta shi yace

Kije na sake ki saki ukku security ya kirawo suka fitar da ita tuni kowa ya shiga mamaki uncle mansur ya dubi ruky yace

"Ke ce mai halin mahaifiyar ki to gani da wani ya ishi me hankali ishara,,

Ƙasa tayi da kai tana kuka

Bayan taro ya tashi su fanna suka koma ɓangaran su cikin salon wasa yace

"Uhmm yarinya baza ki gida ba sai kinyi shekara biyar,,

Buga ƙafafuwan ta ta fara ta toromin dan karamin ba kin cikin shagwaɓar nan ta ta wacce take tafiya da imanin giwa tace

"Uhmm uhmm dan Allah gobe in zasu zan bisu ko kai baka je ba ni zani,,

Dugun hancin ta ya ja ya rungumo ta yace

"Ba inda zaki domin ina buƙatar ki a kusa da Ni,

Mamakin giwa take daman yana magana kamar waka

Ɗaga mata gira yayi yace

Kee haka ake wa miji kwalliya kin bi kin rufe jiki oya cire min wannan a bun yana nuna maya fin ta

Ƙasa tayi da kan ta sallamar su lailah taji da sauri ta miƙe tsaye ta gyara mayafin ta tace

Su partner sun zo bara inje gunsu

Jan yota yayi ya danne ta ya saƙar mata nauyin sa yace

"Ai bayi sallama ba zaki tafi ,,

Tuni idanunta suka kawo ruwa ta ce

Dan Allah ka ɗagani kar su shigo su gan mu a haka fa

To sai me ai mata tace

Ganin zata fara kukan nan nata yasa ya sake ta ya miƙo mata barimar ta

Yace

"Sauran ki ƙara sawa a makaranta ko lokacin ma kishin kine yasa na ƙwace miki ita domin tayi miki kyau sosai kowa ya kalle min adon mata ta,,

Zuba mai ido tayi tace

"Na gode sosai Allah ya kare min kai ,,

Amin my lovely wife

Fita tayi lailah tace da husna da basma sai muhibbat da isham zama tayi suka fara hira

Yayin da lailah ke tsokanar ta su basma na tare mata anty sama anty ƙasa haka su isham ke ce mata yayin da ta ɗauki miemie ta rungume a jikin ta domin kamar su ta ɓaci da yarinyar kamar ita ta haife ta bayan sallar magarib suka tafi shi kuma Giwa sai da yayi Isha ya dawo ta ci ado da wani leshi baƙi da adon flower golding sosai ya haska fatar ta sallamar sa taji tuni shawarar ya gana ta waɗo mata a zuciyar ta tace

Anya kuwa zan iya sai de tayi ƙundun bala ta tafi ta rungume shi

Sosai yaji dadin sake War da tayi da shi kiss yayi mata a kumatu yace

Good girl

Dining room ta nufa da shi tace tun ɗazu ka hana ni yin girki sai da ga shashin hajiya ta aka kawo min tana faɗar haka tana ja mai kujera ya zauna

Cikin jin dadi yace

Hajiyan mu dai ai ba taki bace ke ka ɗe

Hmm tawa ce domin kai yanzu ka girma

Saƙwara ya gutsura ya ɗoni miyar agushi taji kifi da naman kaza sosai girkin yayi dadi cikin santi yace

Ai kece kika sa na girma

Bayan sun gama ci ta wanke ba kinta ta canza kaya ta kwanta tana kokarin kashe fitila ya shigo cikin kayan bacci

Saurin tashi tayi ganin yana ƙoƙarin kwanciya har ya jawo ta jikin sa a haka na tattara yan matayan ƙafafuwana na fita ina jiyo ihun fanna

Assuba ta gari


Wannan kenan

Washe gari da safe jadda ya haɗa motoci domin su kai su airport ban da fanna domin bata da lafiya haka ma Giwa be jema yana tattalin matar sa

Sun isa Maiduguri da huri kai tsaye gidan Dr buƙar suka nufa da yake yayi musu ƙwatan ce saka sunyi sauri ganewa zuwa yayi ya shiga da su daman tun jiya ya faɗawa mami za suyi baki to ta tashi tayi musu girki sallama sukai.ba kowa a floor ce musu yayi su zauna yana zuwa

Jadda yace

"Bakomai sai ya dawo ,,


Be daɗe ba ya dawo ammy na bayan sa hannunsa ruƙe da Nana Asma'u mamy kuwa tana bayan su kan su a ƙasa suka gaishe da su da sauri Mami ta ɗago kan ta jin Muryar da bata taɓa mantawa ba ja daba ta ɗinga yi tana girgiza kai

Dan girman Allah ka fitar min da su a gidana

Abbie yace

"Ki tuna Allah muna mai laifi yana yafe mana ke me isa baza yafe musu ba ,,

Shiru tayi ta sami gu ta zauna tace

Naya Fe musu


Cikin jin dadi jadda yace

Mun gode Allah yayi albarka

Wanna kenan

Iya so da ƙauna Giwa ya nuna mata tare suke zuwa makaranta su dawo ga wani irin tattali da yake nuna mata fanna ta zama yar gata duk abin da uncle Bature ya samo nata ne ga yanxu Mami tana nuna mata so da kulawa ganin su ruky basu da guri yasa suka haƙura akai bikin su suda lailah da birnin kudu

Bayan shekara hudu

"Tuni fanna ta gama karatun ta ta zama likita a asibitin Giwa yayi da ya'yan ta ukku ,,

Da me sunan Abbie ana ce mai junior sai tayi yan biyu aka sa musu sunan mami da ammy ana ce musu afreen da afifa sai mai sunan jadda ana ce mai jadda

Wata iriyar soyayyar ake nunawa yaran duk gidan yayi da musu'af ya aure ihsan yar lukuta tuni zainab ta fara son fanna ta haɗa kan ya'yan ta haka su isham da muhibbat da miemie suna kaunar ta

Alhmdllh alhmdllh alhmdllh

Anan nakawo ƙarshan littafin nan

Abin da na rubuta dai dai Allah ka bani lada abin da nayi kus kure Allah ka yafe min
Chapter 19 · 0% Book details