← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 19

Chapter 72-77

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sosai lailah take bin kowa da kallo domin lamarin na su mufeeda Niger ya fara mata tsoro tace

"Sumy lafiya ke kuma keke dariya ?"

Lallai ba dole inyi dariya ba ganin akan namiji jiyar da mufeeda take tada jijiyoyin huya kuma fa be ma san suna yi ba

Lallai ta ce

Hmmmm hakane Allah ya kyauta

Ameen

Nuratu tace jibi ba karatu saboda ɗaya da December

Lailah tace ni kuma ranar muna da biki su mai sunan uncle mansur (ya imam)

Wannan kenan

Ɗur ƙushe take gaban wani boka dan ba ace malami ba ta share gumin da ya wanke mata fuska tace

"Boka ba yarda za ayi ya aure ƴa'ta ruky domin ni yanxu bana son ya aure amal saboda ba zata bani haɗin kai ba aikin mu ya tafi daidai ,,

Wata iriyar dariya yayi yace

Ai kaf cikin ƴa'yan ki ba wanda zai aura sannan kuma asirin da mukai mai na hana shi aure ya kusan rushewa domin yanzu ya tsaya da ibada sannan mahaifiyar sa a tsaye take akan sa in kika matsa auran kine zai mutu sannan kowa zai san ke wace ce batt ya ɓace

Da sauri ta ta shi lalle kumai yana shirin tonuwa da baya da baya ta fito har ta fito daga dajin ta wahau mota gumi na wanke mata fuska wayar ta ce tayi ƙara ganin sunan ruky yasa ta ɗaga

"Hello hajja we kinji ɗazu naje gidan su Rumaisa ƙawata we ita Giwa zai aura?"

Ruky ina zan sani kin san ba komai Alhaji ke faɗamin ba sai ya gadama yawa nima ba a zuri'ar Giwa nake ba

''okay Kitt ta kashe wayar zuciyar ta na ta fasa ,,

Wannan kenan

Alhaji Dawud wata alfarma nake nema agun ka in zan samu


Da sauri ya dubi abokin kasuwanci nasa yace ina jinka Allah yasa zan iya

Ina so ɗanka ya aure ƴa'ta saboda mahaifiyar ta hankalin ta be kwanta ba karatun nan da take a wani gari sannan wannan yarinyar amana ce aguna tana tare da wasu sirri wanda sai lokaci yayi zaku sani kasan bani na haife ta ba to nida mahaifiyar ta muna tsoran dangin mahaifin ta su ƙwace ta bayan tun tana zanin goyo suka guje ta su kayi wa mahaifiyar ta sakin hulakan ci

Zuba mai ido yayi ya ce


"Zan yi shawara da jadda duk abin da ya ce zai faɗa maka ,,

Sosai ya ji dadin abin da ya ce mai haka taron ya tashi ya kuma hotal ya zauna da yake ya kusan ritaya shiya yanzu ya kama kasuwanci

Wannan kenan

*Giwa mansion House*

Cikin gaggawa aka kira meeting tuni ɗakin taron nasu ya cika barrister sulaiman honourable mansur alhaji Dawud Dr yasir shi kuma Abdullahi pilot ne suna zaune jadda na kan kujera cikin farin ganin ƴa'ƴan nasa yace

Alhmdllh ko yanzu na mutu Wallahi Ubangiji ya game min kumai ba komai ne yasa na tara ku ba anan sai bikin da ya taso mana sanin kanku ne tun shekarun baya na ruguje wannan al'ada na dole ahalin Giwa ba zai auri bare ma to alhmdllh duk da na ruguje ta ta cigaba da tafiya saboda su kansu jikokin nawa suna dai dai ta ƙan su sai dai yanzu wata dama ce ta zo mana tuni ya ƙwashe komai ya faɗa musu sannan yace ya kuke gani ya ɗace mu amshi auran nan ko Aa ni anawa tunanin zamu jefi tsintsu biyu da dutsai ɗaya domin nasa anyi binki can Dr buƙar bulama gana sannan tun danaga fusƙarsa nake tunanin ina na san shi ina ji ajikina jika tace zata dawo cikin ahalinta duba ga labarin da ya bamu inma ba ita bace za muyi kokari muga mun nemota

Tuni kowa ya Amin ce domin maganar mahaifinsu ita ce gaba da komai barin uba kamar jadda da hajiyan daura addu'a sukai na Allah ya ƙara haɗa kansu ya basu zaman lafiya tuni aka tsaida rana jibi za a ɗaura aure kamar ƴarda za ai na su Imam taro ya watsai bayan anci ansha

Wannan kenan

Fanna hutun nan da za ai zamu tafi gida da ke

Duban abie tayi tace

"Abbie da kamar ni za ai biki a gidan su lailai in banje ba bazata ji dadi ba,,

Daughter kiyi haƙuri zan bawa lailah haƙuri ni'matullah zata koma jibi kinga tana so ta ganki haɗo kayan ki

Shiru tayi ta fara haɗa kayan ta da yake lailai ɗazu ta koma gida saboda shagalin bikin da za ai

Ta fito suka ɗauki hanyar Maiduguri kai tsaye ɓangaran ammy ta nufa dan tana tsoran zuwa gun oum nana tana shiga ta rumgume tace

Oyoyo ƴata sannu da dawowa

Farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta tace

Ammy na same ku lafiya

Lafiya qalau tawo mushi ga zama be sameni ba tunda lokaci ya ƙure min

Cikin rashin fahimta ta dubi ammy tace

"Lokaci ya ƙure fa kika ce ,,

Cikin ƙauda zan can tace

Ehmn ba ranar Monday zaki koma ba dudu kwana nawa zaki yi mana

Ni'matullah da Nana ne suka shigo

hira suka zauna sunayi tuni ammy ta kira mai gyara jiki zata fara gyara ta yau

Ita dai fanna ganin komai take ba dai dai ba wanne irin gyaran jiki ita daba amarya ba da kƴar ta yarda duk da tasan ammy ba zata cutar da ita ba

Da dare yayi bayan sun gama dinner gabaki ɗayan su har da mami abie ya dubi fanna yace

Daughter kin yarda da ƙaddara kinsan komai nufi ne na Allah yar da ya tsara haka zai kasan ce

Gyeɗa mai kai tayi yawa ƙadangaruwa domin tun safe da taga me gyara jiki gaban ta yake waɗuwa

cikin tausawa yace

Fanna buƙar bulama gana ni mahaifin ki na zaɓa miki miji kuma gobe za 'a ɗaura aure zaki ci gaba da karatun ki a karkashin kulawar mijin ki

Tuni hawaye suka ƙafe mata sai bin kowa take da kallo ganin shiru yayi yawa yasa ammy ta taɓa ta ashe ta suma tuni ta waɗo daga kan kujerar dining ɗin

A ruɗe sukai kan ta

Abbie ne ya ɗauke ta ya nufi ɗakin ta da ita ya dubi su ammy yace

"Kar ku damu ta shiga yar ɗimuwa ne shi yasa ta suma zuwa anjima zata ta shi,,

Allah ya sa ƙar ta ɗaga hankalin ta har wani abu ya same ta

Amee abie yace

allura yayi mata tuni ta ɗinga sakin a jiyar zuciya

Dukan su suka baro ɗakin ban da mami da ita tana gama cin abinci ta koma sha shin ta dayake yau kwanan ammy ne

Wannan kenan

Ranar bata ƙarya tuni abokanan arziƙi da kusoshin gwamnatin da manyan yan siyasa suka cika masallacin da ke cikin Giwa estate ɗaurin aura aka fara inda aka ɗaura na mansur Abdullahi Giwa da amal Yasir Giwa akan sadaki dubu dari da hamsin sai na abdulhamid Abdullahi Giwa da naseerin ☯️ yunus Giwa tuni gu ya ɗauki kabbara sai a ka ɗau shiru sannan anɗaura auran sa'eed Dawud sa'eed Giwa da Fatima bukar bulama gana akan sadaki dubu dari biyu tuni wata juyawa take neman kada shi duk da azaune yake ga shi kuma a sahun gaba ba damar guduwa dan gashi ga jadda duban tsohon yayi

Wani murmushi jadda ya saki yace .........


RASHIN SANI


Oum yasmeen
Chapter 14 · 0% Book details