← Book details Rashin Sani Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 19

Chapter 26-30

Rashin Sani Complete Hausa Novel · about 5 min read

Duk abin da zai sa su haɗa hanya da yaya giwa basa so domin in yaro yayi laifi to baya yi mai ta daɗi saboda irin tarbiyar da yake musu ganin sa suke mugu shine jikan farko a gidan dan haka baya shi a gidan

"a gajiye ya tora wata haɗadɗiyar stunning iron gate kallo daya zakai mata kasan mai tsada ce ga tsaruwa datayi da alama shashin sane wajan bawani babba bane amma iya tsaruwa ya tsaru ga wasu shuke shuke ga ɗawesu biyu sai yawo suke ga filin ball daya ƙawata shi tamƙar kana stadium hannun dama kuwa wani haɗadɗan gun motsa jiki yayi wajan glass ne na ciki yana iya ganin na waje amma na waje ba abinda yake gani amma na waje baya ganin komai nima leƙawa nayi na gano muku ga wasu park bench guda biyu da table mai kyau stunning door ya sa hannun sa a wani gu da farko ta kawo ja sai da ta gama tantan ce hannusa tasa blue tace your well come sai ta buɗe switch ya kunna tuni haske ya gauraye daɗin wow wasu irin luxury sofa ne up white color da adon golding iya kyau sunyi brief case ɗin sa ya ajjiye a kan wata cuddle chair itama up white fridge ya nufa ya buɗe wayayi shaƙe yake da kayan alatu gora ya dauka ya buɗe ya kafa abaki be cire ba sai da yaga ba koami a cikin ta ya saki wata ajiyar zuciya benan da yake manne da floor sa ya nufa cikin nutsuwa yake taka stairs case ɗin ga baki daya balcony ɗin na glass ne amme ado silver gaban wani ɗaki ya nufa shi kadene a benan da alama bedroom ne tora kofar yayi ya shiga tuni wani kamshi ya bigi hancina dum light ne a ɗakin tuni ya dannan switch tuni farin haske ya gauraye ɗakin ba tar kace komai yana cikin tsari

"gawasu irin labulaye farari tas wata irinyar tagace ƙatuwa hasken waje yana shigo wa ga wani lilo ajikin ta da table da alama gun anyi shi dan hutu ne kayan sa ya cire ya shiga toilet komai nashi cikin tsari yake wani gune babba ansa glass towels ne farare tas ajere na goge kai daban haka na goge ciki dana daurawa daban ko wanne a jikin sa ansa s.d.g da alama na musamman akai mai su bathtub ya shiga yayi wanka sosai yake zabga kamshi saboda irin sabulan da yayi amfani da su towel ya daura ya fito T-shirt yasa yar gidan puma blue black inda ya sanya wando equarter turaran al rayyan yasa sai ya haɗu da turaran wankan sa yake bada wani kamshi agogo rolex ya daura ya dauki wayoyin sa slippers yasa dayake ƙafar shi ya sa safa saboda sanyin da ake ya fito ko briefcase ɗin sa be biya ta kai ba ya nufi wata siririyar ƙofa da alama wani gun zashi abin mamaki wani tamƙameman floor ya shiga sallama yayi ciki ciki da sauri yan matan biyu da na miji daya suka ɗago cikin farin cikin dawowar yayan nasu suka amsa da sannu da zuwa yaya

"amsa musu yayi cikin deep voice ɗinsa yace

'Ina hajiyar mu take ?"

Basma ce tace

tana bed room ɗinta

"Okay kai musu'af baka koma makaranta ba zaman me kake ?"

Cikin rashin gaskiya da kame kame yace

Big brother yau mun dan sami hutu ne sai wani satin zan koma

"okay a kula kuma bana son inji wata magana ta biyo baya ,

Insha Allah yaya ba abin da zaka ji

"huce wa yayi wani ɗaki wata mata ce ta juya baya tana karatun qur'ani wasu haɗadɗun luxury funiture masu kyau da tsaruwa kallo daya zakai wa ɗakin kasan an kashe dukiya sallama yayi ga nin tana karatu yasa ya sami arm chair ɗin dake bedroom ɗin ta ya zauna ganin ta kusan idar da karatun ya sauko ƙasa wani haɗadɗan carpect ne mai taushi ash color da ratsin black color anyi flower da silver color ya tanƙwashe ƙafar shi tamƙar malami da ɗalibin shi ganin zata shafa yasa shima ya ɗaga hannu sa sukai addu'ar tare juyowa tayi farace tas kallo ɗaya zakai mata kasan buxuwa ce hutu da jin daɗi ya zauna mata

"hajiyar mu barka da dare da fatan na same ko lafiya ,

cikin kulawa da soyayyar ɗan nata tace

Lafiya qalau giwa ya aiki

"Alhmdllh hajiyar mu ,

Masha Allah giwa a yanzu bani da buri da ya huce in ganka kayi aure ka duba fa ka gani December ɗin nan da zamu shiga watan farko za akai kayan su mansur duk ƙannan ka sunyi aure dan Allah giwa ka nutsu ina so inga ƴa ƴan ka

"sosa kai ya shi ga yi cikin burin kunya yace ,

Insha Allah na kusan kawo miki budurwata kar ki damu

Buɗa baki tayi zayi magana yayi sauri yace

"addu'a kawe zaki ciga ba dayi ,

dungure mai kai tayi tace

Wallahi duk uncle bature ne yake daure maka in akai magana yace aure lokacine giwa ko dan lalurar ka kai aure

"dariya yayi in yana gaban daddy da hajiyar mu ji yake ba shi da wata damuwa ya koma kamar yaro yace,


"To, zanyi first love,

jin muryar husna ta ce

Hajiyar mu mun kammala abincin


"To, husna gamu nan zuwa ,

Kai ya lamgwaɓa yace

Hajiyar mu yau ta fitinan niyar yarinya na haɗu da ta duk ta gajiyar da ni

Juyo watayi ta fasa cire hijabin ta wannan shine karon farko da taji yayi mata zancan mace a rayuwar sa cikin salon jan yaro a jiki ta ce

"me ya haɗa ku my son ?"

hmm first love Allah shagwaɓabɓiya ce da ga nayi mata magana sai ta fara kuka

topa ita da haka za ai auran

Zaro ido yayi yace

Hajiyar mu bafa budurwata ba ce ɗaliibaaata ce ……………✍🏼

*RASHIN SANI*

By

Oum Yasmeen
Chapter 6 · 0% Book details