← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 31

Sashe 31

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wata bakwai ciff_ciff mama tafara nakuda aikuwa adaren ranan jakadiya ce ta karbi haihuwar ganin fuskan sarauniyarsu dakuma bayanta nadauke da zanen tambarin masarautar su (tattoo dake bayan fanan) yasata shiga cikin farin ciki mara misaltuwa daduk masarautar nasminaya, duk data kasance bakwai ni amma tafi wani dan wata taranma girma dakuma kuzari jakadiya ce tabukaci da abawa sarauniya nata dakin daban saboda suji dadin kula da ita dukda basaso haka suka ware mata dakinta daban ranan suna yarinya taci suna Fatima suka mata lakabi da fanan, ahaka tadinga girma dawasu abubuwan mamaki atare da ita Kuma koda wasa basa yarda tayi nisa da gida dazesa takai mangrib kansu daya da suhaima yar gidan kabiru.
___ tunda takai shekara 10 kuma wayan nan abubuwan al'ajabin suka dena bibiyarta kawarta daya dal itace amira, fanan nada shekara she uku aduniya mama tasake haihuwar ya mace suka samata ilham (auta) time din kuma su usman suka gama makaranta , haka fanan da Amira suka girma harsuka gama secondary school dinsu tare akasamo musu addimission a garkuwa school of health lokacin suna aji hudu a islamiyya, dake 2yrs program ne suka gama dawuri sukayi graduate batare da bata lokaci ba baban Amira yasamo musu aiki a asibitin specialist suka fara aiki, akaxo akayi auren anty firdausi, babban abinda su baba suka fara lura dangane da fanan shine babu wani namijin dayataba tunkararta da sunan yana sonta abun yadaure musu kai Sosai amma haka sukayi shuru.

Wannan shine takaitaccen tarihinmu cewar baba ba karamin girgiza sukayi ba dajin haka abin yabasu mamaki fiyeda yanda baa tunani gyaran murya me martaba yayi yace " tabbas fanan baiwar Allah ce wacce batasan komai ba ta cancanci girmamawa da farantawa kafin tabar duniyarmu domin ni inada labarin nan domin kafin sarki abdud daar yabar duniya Abdud Shakur yasameni yafadamin abinda yafaru dukda bansan waye sarkin nasu ba amma na tausaya musu matuka gashi bamuda hanyar taimaka musu sede nasa akata musu adduo'i! Nasan abdud Shakur ne alokacin da natafi aikin hajji nida iyalaina muka hadu dashi muka fara abokantaka be boyemin komai ba yafadamin shi jinni ne hakan bedameni ba mukaci gaba da zumunci duk sanda yasamu lokaci yakan kawomin ziyara ,ranar wata jummaa ne cikin tsohon dare yazomin amafarki naganshi acikin mawuyacin hali nan ne yake sanar dani abinda suke fuskanta yakuma bayyanamin kancewa sunyi sabuwar sarauniya ashe fatima ce Allahu akhabar " azaad de jinsu kawai yakeyi shidama tunda yaga fanan yagane bawai wani abu bane ajikinta itadince dakanta duk da bawai yayi believing da wayan nan abubuwan bane adduah yadingayi Allah yasa su shashantar da maganar auren. Haka suka cigaba da tattaunawarsu, Abba yace " ai dah nakowane Allah Ubangiji yakareta dakuma al'umman musulman duniya daga sharrinsu" amsawa sukayi da Ameen fara raba goro akayi ganin da gaske sukene yasa azaad cewa " Abba amma kasan dacewa akwai alkawarin aure tsakanina da aneesa " Abba zeyi magana me martaba yarigashi da fadin" karka damu aikana da daman dazakayi hudu" dariyar shakiyanci yaseer yasa. Shuru yamusu yana sake_saken aranshi, haka aka daura auren azaad muhammad mainasara da Fatima muhammad Umar akan naira dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba nan take suka fara gaggaisawa da juna suna taya juna murna bakin ciki kamar zekashe azaad afusace yamike yafita a falon bin bayanshi doctor ammar da yaseer sukayi. Su ya Usman kuwa tunda sukaji wacece kanwarsu din gaba daya walwalarsu taragu barinma insuka tuna zata tafi tabarsu wata rana.

Bada umarni me martaba yayi akira mishi matan gidan kiransu ya al ameen yaje yayi suka fito danduk wainar da ake soyawa basu saniba zama sukayi suna gaida me martaba kallon fanan da har time din take kwance akan kafadar ummi yayi gyaran murya yayi yabude taro da sallama " Fatima naji duk wani abinda yafaru daku iname baki hakuri da lefin danmu yashafeki amma kisani kaddara bata canzawa sede tadau lokaci " haka de yamata nasiha me ratsa jiki ita da gaba daya jamaar dake falon daga karshe yace " se abu nagaba yau aka daura miki aure keda azaad domin kutsira daga kazafin da akamuku " dagowa fanan tayi dasauri tana kallon me martaba dan san gasgata maganar daya fada wani azaad din yake nufi ................

Alhamdulillah nan nakawo karshen book 1 da izinin Allah .
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
Chapter 31 · 0% Book details