← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 31

Sashe 3

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin karfe 12:00 nadare wata farar motace ke sharara uban gudu akan hanya kamar bazata tsaya ba domin kuwa me motar kansa ba lalle in Yana hayyacinsa ba duk iya kokarinsa na ganin yataka birki motar ya tsaya Amma ina abin yacitura , ganin dayayi saura kadan yafada wata katuwar Rami ne yasa yafara Kalmar shahada cikin kankanin lokaci mota ya wantsila cikin ramin bayan 5mint motar ta kama da wuta🔥 nafitan hankali.

Karfe 5:00am wani Dan saurayine yafito zeyi bayan gari acikin dajin kawai yaga motor nadanci da wuta kadan kadan karasawa yayi Yana me adduah allah yasa ba mutum aciki domin inde akwai zeyi wahala yarayu gama duba wajan yayi kaff bega kowa ba harya fara tafiya yadanyi nisa kadan cikin ciyawa yaga hannun mutum cike da fargaba azuciyarsa yakarasa wajan aikuwa kwance yaga bawan Allah kwance kamar gawa babu alamun daze nuna maka Yana Raye domin kuwa jini yama jikinshi wanka, salati yasa gashi ba cikin gari bane balle yanemi taimako haka yasabashi akafada yafara tafiya Yana Nishi dakyar harya samu yafito titi duk motocin Daya tsayar basa tsayawa, dakyar wata mota tatsaya bayani yayi WA mutumin cikin jinjina lamarin me motar yafito yataimaka mashi suka kamashi suka kwantar dashi abaya tada motor yayi direct asibitin gombe SPECIALIST suka wuce suna shiga nurses sukayo kansu aka shigar dashi emergency room akashiga dashi tsabar yanda sukaga yayi mumunar raunata dakuma jigata doctor's din ko takan police Basu biba, rufuwa sukayi akanshi suna bashi taimakon gaggawa awajan ward kuwa wannan saurayin ne da mutumin suke zaune sunyi jugum dukda Basu sanshiba Amma sunyi matukar tausaya mishi bayan kamar 1hour doctor yafito ya rubuta magani yabasu yace agaggauta siyowa yanzu nan karban takardan mutumin yayi cikin sauri yaje yasiyo yakawo musu Karba sukayi suka koma 2hours later doctors din suka fito Suna goge gumi karasowa kusa da doctor din sukayi fuska asake doctor din yace musu alhamdulillah munsamu numfashinsa yadawo Dede, alhamdulillah suka fada atare suna musabaha, sannan doctor yace sede wani hanzari ba gudu ba yashiga coma inba iKon allah ba ze Kai wata Daya ko fiye da hakan kafin ya farfado. Kallon juna sukayi yanzu yazaayi gashi yanzu niba mazaunin gombe bane a Yola nake dama inakan hanyane nahadu da wanann bawan Allah yace intaimaka musu ah ah bakomai karku damu inde bazakuna samun daman zuwa akai akai ba Munada nurses kwararru wayanda zasu bashi kulawa yanda yakamata kafin yadawo hayyacinsa. Masha Allah shikenan yanzu doctor kamin lissafin duk wani charges din abinda akamishi dakuma Wanda zaa mishi nan gaba har izuwa time din daze samu lfy sannan kaban phone number ka sbd indingajin lfyr sa . Kallonsa doctor yayi yace Gsky alhaji kanada kyakyawar zuciya duk da bakasanshi ba gashi kataimakeshi inba damuwa zan iya sanin sunanka, sunana alhaji badamasi me ruwa Kara kallon sa dakyau doctor yayi yace dama kaine alhaji badamasi me ruwa iKon Allah yau de naganka dariya sukayi kafin yayi WA doctor transfer 2million domin yanasan abawa wanann bawan Allah de besan awata duniya yake ba kulawa na musamman. Sallama sukayi wa doctor tare da alkawarin zasuna zuwa dubashi akai akai.

Bayan tafiyansu time din har 9:00am yayi akafito dashi aka kaishi private ward inda SE Wanda ya Isa zeyi jinya aciki. Komai na more rayuwa akwai sa aciki ansa duk wani abinda zaawa coma patient amfani dashi akwai. bayan sungama seta mishi su oxygen da pulse oximeter, ventilator machine etc. Fitowa sukayi suka shiga office din doctor ammar suna tattaunawa akan waya kamata su tsayar akanshi wanda zedinga bashi kyakyawar kulawa Daya daga cikinsu yace ni aganina abawa nurse mufida koya kuka gani girgiza Kai doctor Ammar yayi yace noooo tanada rawan Kai Gsky bari zuwa karfe 12 narana zanbi list din nurses din dabasu fi 1yrs dafara aikiba acikinsu semu tantance waye ya kware dabawa patient kulawa yanda yadace dakuma sakin fuska da nutsuwa duk kansu sun yarda da shawaran Daya kawo.

FANAN tagama duk wani aikin data sabayi kullum tayi wankanta tashirya tafito falo tayi breakfast 🥞 sannan tayi musu sallama ya Usman ya ajiyeta Yana zolayanta yau naga kamar yar kanwar tawa da farin ciki ta tashi dariya tayi wlh kuwa ya Usman kome yasani haka oho dariya yayi yace tom Masha Allah ai haka akeso tafiya yayi tana mishi bye bye tashiga asibitin.
Bayan tashiga tafara duba patient's duddubawa tayi bataga bestie ta Amira ba alamun bata karasoba tukun.

Amira batashigo ba SE 11:30 tana shigowa kuwa wajan FANAN tayi kawata yau kam kinyi latti mtsssw tsaki tadanja kede bestie bari kawai bestie bakisan meyafaru ba daddy ne yasamomin addimission a pen resources wai zanyi degree Dina acan rungumeta fanan tayi cikin farin ciki tace wlh bestie natayaki murna sosai. Zuba mata ido kawai Amira tayi kafin tace nikuma wlh banaso nafijin dadin haka na wani degree ne zedameni wlh kwata kwata banasonyin nisa Dake duka FANAN takai mata kekam wlh se adduah sannan kuma ai ba rabuwa zamuyiba nasan inkin dawo school zakizo asibiti ko eh in sha Allah haka nakeso suna tsakiyar magana wani security yashigo yasamesu yace Dan Allah, Tambaya nake sukace allah yasa munsani dorawa yayi dacewa doctor ammar ne yake neman Fatima M Umar dakuma Aysha abubakar wada kallon juna FANAN da Amira sukayi kafin sukace mune allah yasa balefi mukayi ba ah ah bansaniba Gsky cewa yayi de inkiraku okay tom Bismillah muje, tafiya sukeyi Yana gaba suna binshi abaya harsuka Isa office din doctor ammar sallama sukayi suka shiga gaishesa sukayi Amsawa yayi yana tsokanansu Anya ku ba Yan biyu bane kuwa kullum Kuna tare dariya kawai sukayi. Tom yanzu de kuzauna zama sukayi kafin yace Meye sunanku fada mishi sukayi......

To masu sauraro koya zata kasance kubiyoni kuji.😜😜😜😜
🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story Written by ( MRS 🌹 ISHAM 🌹)
Da sunan allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen 🙏🙏

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci 🥰🥰🥰

___________________________________________

Page5️⃣

Fada masa sunansu sukayi, doctor ammar gyara glass din idonshi yayi yace Muna dawani patient ne Wanda muke bukatar abashi special care Wanda yake cikin coma yanzu haka, so nayi bincike akan Wanda yakamata yakula dashi se bincike na yafado takanku yanzu dole ne mutum Daya nake bukata wacce zata dinga bashi kulawa dakuma attending nashi da wuri Banda letting, yanzu yakuka gani fanan nakokarin magana Amira tayi sauri tace am doctor Gsky sede abawa FANAN kura mata ido sukayi sunason Jin dalilin dayasa tafadi haka,kafin tadaura dacewa nide yanzu Gsky koda ace nice zanna kula dashi tofa Gsky bazanna zuwa da wuri ba saboda nasamu addimission a pen resources zanyi degree anan shisa nace abawa FANAN gyada Kai doctor Ammar yayi cikin gamsuwa da bayananta yace to FANAN yanzu gareki daga yanzu aikinki yafara saboda inada yakinin Zaki bawa patient dinki kulawa yanda yakamata.
Harga Allah fanan bataso haka ba har zuciyarta taji badadi domin tasan dole yanzu zatana takura fiyeda dah Amma haka ta kaqulo murmushi dole tayi tace to shikenan doctor allah yabani iKon kula dashi shikuma allah yabashi lfy amsawa sukayi doctor ammar nakara yaba hankalinta da nutsuwarta, kafin yace ke Amira Zaki iya tafiya sallama tamusu tafita juyowa yayi yakalli FANAN yace muje dakin nashi tafiya sukeyi Yana gaba tana binshi abaya harsuka Isa shiga ciki sukayi har gaban gadon nashi Yana kwance besan inda yakeba. kura masa ido doctor ammar yayi tabbas yasan wannan fuskan Amma yamanta, daure masa Kai abin yayi domin kuwa ba shakka yasanshi Kuma sani bana wasa ba sannan baya tunanin a Nigeria suka hadu. Ganin tunanin baze kaishi ba yajuyo Yanawa FANAN Dake bakin kofa magana karaso mana kintsaya awaje. Shigowa ciki tayi tana karewa dakin kallo, sauka idonta yayi akan wani kyakyawan balarabe idan kuwa ba Arab guy bane to tabbas half_cast ne domin kuwa kyaunshi yawuce misali, karasowa tayi tana kallonshi domin kuwa kyaunshi yatafi da ita, duk da akwai oxygen afuskanshi hakan behana kyaunsa bayyana ba, tubarkallah Masha Allah tafada azuciyarta.ashe doctor ammar nata mata magana ita batajishiba tana ta santin kyau din patient dinta, sunanta yakira da Dan karfi FANAN firgit tadawo hankalinta Naam murmushi kawai yayi domin yasan abinda yasa tashiga tunani yace your time Start from now on tace okay doctor. Fada mata Abubuwa masu amfani dazata dingayi yayi kafin yafita yabarta. Warm water tahada a bowl tasa karamin towel tajika tafara goge mishi jikinshi sannan tayi feeding nashi through vein Yi mishi abinda yakamata tayi har zuwa karfe 8:00 nadare kafin tagama komai fitowa tayi tawuce gida.

Tana shiga gida tasamu mama da baba awaje tambayarta suka shigayi meyasa tayi dare, bayanin duk abinda yake faruwa tamusu to shikenan allah yabashi lfy sannan kuma duk sanda zakiyi dare ki kirani awaya ko yayanki azo adauke ki karki Kara dawowa dakanki kinjini ko baba yagama magana Yana kallonta amsawa tayi da in sha Allah baba shiga cikin falo sukayi duk kansu anan tasamu taci abinci. Sannan tawuce dakinta tayi wanka tafito tasa kayan bacci ta kwanta tana tunanin wannan bawan Allah daga gani yayi matukar Jin jiki kudurtawa tayi aranta in sha Allah zatasashi a adduahrta . Ahaka har bacci yadauketa bata sani ba, karfe biyu nadare ta farka taga ashema bacci tayi lalle yau takwaso gajiya mikewa tayi tashiga toilet tayi alwala kasancewar tafara sallah shinfida sallaya ta tada sallah adduah tadinga Mishi nasamun sauki ta idar ta koma tayi adduah bacci ta kwanta.

Washe gari 5:40am ta tashi tayi sallah bayan tagama azkar ta mike taje ta gaishe dasu baba sannan tafara aikinta nayau da kullum tahada breakfast 🥞 sannan Takoma taje tayi wanka tashirya fitowa tayi ta karya baba yabata kudin transport sannan Ya usman yakaita direct addimission ward tayi taje taduba patient's dinta bayan ta sallamesu tawuce private ward kamar yanda tabarshi jiya haka tasameshi bayida maraba da gawa karasawa tayi inda yake tamishi duk wasu abinda yakamata.

Sannan tasamu waje tazauna tana hutawa.
Chapter 3 · 0% Book details