← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 31

Sashe 10

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Washe gari karfe 5:00am suka tashi nafila sukayi kafin aka shiga masallaci bayan sun idarne FANAN tace "bari inje in fara aiki" okay sena fito kitchen tawuce tahada kayan wanke_ wanke tayi tazo tayi shara da mopping sannan tadaura abin karyawa karfe 7:30 tagama komai tashiryasu afalo sannan Takoma tashiga wanka fitowa tayi tasamu suhaima nata sharara baccinta hankali kwance "ke mayyar bacci dallah tashi kije kiyi wanka kizo muyi breakfast" mikewa suhaima tayi tana salati da Mika kafin ta harareta "nifa bansan irin haka dole SE tare zamu karya Ina bacci na me dadi kin wani tasheni" Koh kulata FANAN batayi ba kayanta tadauko a wardrobe Riga da skirt ne na atamfa orange da touch din Baki sakawa tayi skirt din yadan kamata fakin din gashinta tayi tasa ribom Baki harta dauko dankwali zata daura seta fasa, shafa powder tayi tasa kwalli a idonta sannan tafesa turare hijab dinta Baki tasaka dogo harkasa me hannu daukan handbag dinta tayi da plate shoe
Hartazo fita tajuyo takalli suhaima data koma bacci dudduba dakin tayi can taga guntun pure water taje setin fuskanta tadaga ledan tafara sheka mata ruwan afuska azabure ta mike tafara banbami aikuwa dasauri FANAN tabar mata dakin tana dariyan mugunta falo tashiga taje dakin mama haduwa sukayi da mama tana kokarin fitowa gaisheta tayi "nagama abun karyawan" to muje falon suka dawo Basu fi mintuna dashigowa ba su ya Usman suka shigo suna musu "Kai wlh zanbaka shawara ka koma man city kawai" inji ya Usman "allah yakyauta mu ai Madrid bagudu baja da baya karka ga Dan abdulkareem benzema yabar Madrid kuyi tunanin yawargaje zamu dawo" dariya sosai ya al Ameen yayi kude kawai yanzu kunzama losers oho koma de Meye munji gaida mama sukayi kafin fanan ta gaishe dasu amsawa sukayi Al Ameen yace "Ina suhaima bangantaba kode haryanzu tana baccin asara" ya al Ameen natasheta tana zuwa okay zuba musu abincin tayi alele ne da Miya SE farfesu da kunun gyada Basu faracin abincin ba seda baba yashigo duka gaishesa sukayi zama yayi Yana amsawa gaisuwan nasu kallon su yayi duka kafin yace Ina suhaima , suhaima Dake bakin kofan shigowa tace baba gani nan karasowa falon tayi tana gallawa FANAN harara dariya kasa _kasa fanan takeyi Dan tasan abinda ta aikata gaida mutanen falon tayi kafin tazauna suka fara karyawa abinci sukeci Amma daga zaran suhaima da fanan sun hada ido hararanta suhaima takeyi itakuwa FANAN abin dariya yake bata harara suhaima tawatsa mata wani irin dariya ta fashe dashi Wanda seda falon yadauka kowa yatsaya yazuba mata ido takai kusan 3mint tana dariyar kafin ta tsaqaita ganin datayi kowa yazuba mata ido suna kallonta da mamaki ne yasa tashiga nutsuwarta gaba Dayansu sunkasa dauke idonsu akanta mama kam ta gumi tayi tana kallon iKon god baba ne yace "FANAN fatan de lafiyanki kalau" eh baba tana sunkuyar dakai to Allah yasa ya Usman ne cikin zolaya yace " majinyatan mu na gida Dana asibiti Allah yabasu lfy dariya sukayi duka suna Ameen bayan sungama ne FANAN tace zan tafi as usual kudin transport baba yabata Yana mata adduah dawowa lafiya kallon suhaima tayi tace "yar uwa yau ba rakiyane " eh din bazaa rakaba fita tayi tana yar dariya.

Baba ne yace "ohhh FANAN Allah yashiryeki" mama ce ta amsa da Ameen kome yasata dariya haka se Allah ya al Ameen Dake Shan kunu ne yafara fadin "aiduk abinda sukeyi ita da suhaima Ina kallonsu suhaima ce ke hararanta itakuwa hararan ne yabata dariya shine take dariya" hhhhhhh Abin dariya yabasu baba yace "alamu sun nuna yau fa sun kwabe anyi fada kenan ".
Chapter 10 · 0% Book details